Chapter 11
Chapter 11
bedroom ɗinsa ya wuce don ya kimtsa yau zasu yi fita ta musamman da sehrish don ya tsara har ice cream sai sunje sha, haka itama azmee kimtsawar take yi don su fice, Haroon sam yagaza fitowa saboda kunyar haɗuwarsa da sehrish baisan martanin da zata yi mashi ba, dama jiya ta yarda masa magana a cikin toilet ina ga yau da tasamu ƴanci Allah kaɗai yasan Zagin da zaisha, ga yunwa yana ji amma sai faman zarya yake aransa yana faɗin "Ke ma bazan ƙyale ki ba Yarinya saina ƙasƙantar dake kuma bazan fasa abunda nayi niyya ba akan Ki,*YANZU WASAN YA FARA* 🙆 Fitowa azmee tayi jikinta na sanye da doguwar riga ta atampha ta kashe ɗaurin kallabi, sai ƙamshi take cikin hanzari ta wuce kitchen saboda tunawa da Marshal Omar wanda bai fito yin breakfast ba kuma ba'a kai masa ba, shaf shaf ta shirya masa a tray ta wuce part ɗinsa ta shiga da Sallama babu kowa a falonsa hakan na nufin koma bacci bai tashi ba, ajiye masa tayi asaman ƙayataccen table ɗinsa sannan ta fuce, Tana saukowa down stairs taci karo da haroon wanda ke tafiya cikin sanɗa zai shige kitchen wai don karya ci karo da Sehrish girgiza kai azmee tayi aranta tace "Shi ko haroon ko lafiya yake faman tafiya cikin sanɗa haka kamar mara gaskiya, Ni wlh nama manta dashi ashe yana nan,' Gyaran murya tayi tare da cewa "barka da fitowa mlm haroon," firgit yayi tare da juyowa ya kalle ta, ajiyar zuciya yasaki ganin azmee ce "Aunty azmee barka dae fatan an tashi lafiya, shine aka manta dani ina ta fama da yunwa yanzu da ban fito ba da shikenan sai dae yunwa ta kashe ni ko? Ya tambaya hada ruƙe qugu dama ransa a 6ace yake......... Azmee tace "Kayi haƙuri wlh ni sam na manta ban lura da baka fito ba ba," ta6e baki yayi tare da cewa "koda yake dama ae ni ba'a sona na lura, bama kallon mutun ake mun ba acikin gidan nan kowa ya raina ni," Murmushi azmee tasaki tana kallonsa tace "kadaina cewa haka bana jin daɗi, koda kowa zai guje ka amma kasan ina tare da kai ko? Ka ta6a ganin inda UWA ta Guji ƊANTA?" tayi maganar ne don ta kwantar masa da hankali ganin ya ɗan fusata, Sakin fuska haroon yayi sannan yace "Shikenan nadaina aunty azmee tunda baki so, yanzu dai a haɗa mun breakfast ɗina wlh yunwa nake ji har wani jiri nake gani, Wuce sa azmee tayi tana cewa "a ina za'a kaima abincin anan ko a ɗakin ka," cikin sauri yace "Ki haɗamun kawai natafi da abuna ɗakina naci,Zai fiye mun kwanciyar hankali na" Kitchen ɗin tashiga ta haɗa masa a tray sannan ta miƙa masa jikinsa na rawa ya kar6a ya wuce ɗakinsa, Gefen gadonsa ya zuna hannunsa har kerma yake yi yana cusa abincin abakinsa, kamar daga sama yaga sehrish ta bayyana agabansa jikinta sanye da Kayan Sadaukai na Yaƙi, hannunta ruƙe da Zungureriyar wuƙa kanta na ɗauke da Kambun Sarauta, hankali atashe haroon ya fesar da donuts ɗin daya cunkusa abakinsa yana kallonta cike da tashin hankali, fashewa da dariya sehrish tayi tare da cewa "Kai Haroon! Ƙaryarka taƙare ! ka jima kana ƙuntatamun gashi yanzu Allah ya ɗaukakani, babu wata sauran barazana daga gare ka ta ƙare, nazo ne don na ɗauki fansa akan ka, yanzun nan zan fille kanka da wannan wuƙar ta hannu na, Da ƙarfi sehrish ta ɗaga wuƙar zata fille ma haroon kai, aikuwa a firgice ya miƙe tsaye yana dafe saitin zuciyarshi a tsorace Lokaci guda Sehrish ta 6ace masa 6aaat hakan na nufin ba ita bace idonsa ne ke masa gizau,amma shi tabbas ita yagani kodai yarinyar Aljana ce ? Ya tambayi kansa,.wannan ba kowa bace face Hafsat Bature Aljanar sehrish 👿 Koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da cin breakfast ɗinsa anatse, yayin da ransa ke saƙa mashi abubuwa da dama game da mummunan ƙudirinsa __________ 💪 ______________ OMAR a hankali ya soma buɗe idanunsa bakinsa na ambaton addu'ar tashi daga bacci, yayin da zuciyarsa ke cike fal da son ganin Tagwayensa, tun da asuba daya sha maganin mura bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi sai yanzu Allah yayi mashi ikon Farkawa daga bacci, a hankali yasa hannun sa ya janye blanket ɗin daya lullu6a dashi jikinsa na sanye da Night dress riga ce dai dai guiwa mara nauyi, fararen idanuwansa yafara kaiwa ya kalli agogon dake manne jikin bango ƙarfe 12 na safe yayi mamakin yadda lokaci ke gudu har haka, ko don yayi overdose na maganin muran daya sha ne yasa shi yin dogon bacci har haka, Cikin sauri ya yunƙura ya miƙe direct toilet ya wuce , brush yafara yi yana tsaye agaban wash basin amma idonsa Fuskar Jahad da Hosana take hasko masa ta cikin mirro ɗin gabansa, shaf shaf yayo wanka ya fito jikinsa sanye da Bathrobe(rigar wanka) fara, wadda ta tsaya masa adai-dai guiwarsa, Marshal Omar kenan Son kowa ƙin wadda tarasa 😉 kai tsaye wuce wa yayi ya ɗauki wayarsa dake a saman gadonsa, sak irin ta sgr ce, Company ɗaya ce waya ce ta musamman domin Manyan jami'an sojoji irinsu kirar Companyn Iphone Ce, hamshaƙiyar waya haɗaɗɗiyar gaske wadda kuɗinta sun haura 30millions, ba kuɗinta bane abun mamaki ba a'a amfaninta shine abun dubawa, ƴar bala'en wayace bakowa ma zai iya Controlling ɗinta ba sai mamallakinta. dannata ya soma yi Contact ɗinsa ya shiga kai tsaye numbar aunty BABBA ya laluba, ya buga mata Calling ta shiga ringing, burinsa tayi picking yasanar da ita cewa Zai shigo kaduna don ya duba su Hosana da Jahad, almost 3 times ba'a ɗaga kiran ba, domin kuwa wayar tabar ta agida, canza ra'ayi yayi ya dannawa Wayar Hafsat kira, Suna a asibitin nan zaune saman waiting seats, bacci duk ya kwashe su daga zaune don daren jiya ba wanda ya runtsa sai da sassafe wurin ƙarfe 10 suka samu baccin wahala shima saboda likita yasanar dasu cewa Yarinyar da ranta bata mutu ba, farkawa ne kawai batayi ba doguwar suma tayi, shine suka ɗan samu natsuwa suka baje suna bacci kamar wasu shanaye ga uwar yunwa na cinsu, kiran Omar ne yashigo da ƙarfin gaske a wayr hafsat dake acikin purse ɗinta data aza saman cinyarta, a firgice suka farka su duka wuri wuri da ido, cikin hanzari hafsat ta zura hannunta cikin purse ɗinta ta duba me kira sunan MARSHAL OMAR ne ya bayyana, dafe ƙirjin tayi hankali atashe tace "MUNSHI GA UKU ! MOMMY YA OMAR NE KE KIRA"😳 Mu haɗu ranar monday Insha Allah🙏 Kar amanta da paymemt wanda suka shirya sumin magana 08103884440, 300 ne VIP kuma 700 ga wanda basa ra'ayi a grp*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* *🔥The Father Of Soldiers🔥* ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖 *Story & Written by* *Hafsat Bature Muhammad* ~💋BOSSLADY💋~ *Abban Sojoji part 2* *EPISODE 7-8* *AYAAN* arab name ne for boys means God's Gift (kyautar Allah) ❤️ Waro ido waje aunty babba tayi tana faɗin "Shikenan komai ya ƙare, Hafsat kada ki ɗaga kiran nan, katse shi kwai , a rude take magana, Hafsat tace "Mommy how can i reject his calls ! Idan zuwa zai fa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47