Chapter 3
Chapter 3
da wata manufa face wannan, kuyi haƙuri ku yafe mun bazan Iya cigaba da rayuwa a wannan duniyar ba mai cike da tashin hankali, ban ta6a cutar da kowa ba, amma gashi wani nason cutar da rayuwata ....................." Cikin sauri ta shiga zazzaga hodar abakinta A dai dai lokacin Motocin Sgr da marshal Omar suka shigo cikin gidan atare jiniyarsu ta karaɗe ko'ina har cikin kunnan Sehrish Zuciyarta ce taji tayi wani irin bugu, nan take kuma zuciyarta tace "Yanzu kin amince ki mutu baki cika burinki ba!? ke fa musulma ce ! Kin kuma son hukuncin wanda ya kashe kansa da gangan!! Runtse idonta tayi hawaye na zuba, fuskar sgr kawai take tunawa da fuskar su hosana da jahad, "Ina son sake sashi a idona," ta furta da wani irin sound, nan take tayi wurgi da robar chemical ɗin dake hannunta, cikin hanzari ta shiga amayar da wanda ke bakinta agaban basin, fanfo ta kunna tashiga kuskure bakinta da hanzari ta kora aman, sannan ta wanke face ɗinta ta fito, tana tafiya zuciyarta na ƙara bata ƙwarin guiwa da cewa "Saboda wani shashasha zaki halaka kan ki, share hawayenki sehrish kina da damar rayuwa, wani banza bai isa ya tarwatsa miki burinki ba," Gyara jikinta ta shiga yi saboda tana son zuwa kai mishi dinner ɗinshi shi da Omar don ta son da yunwa suka dawo, duk da tana tsoran kada suci karo da haroon a fitarta, dama riga da wando ne ajikinta, gashin bakinta kawai ta manna, ta gyara hular kanta da mayafin da take naɗe hular dashi, bayan ta kammala ta buɗe kopan cikin fargabar ta fuce,. Ko'ina haske fauuu gidan cikin sanɗa ta wuce kitchen taji sanyi aranta ganin babu kowa, Cikin hanzari ta shirya ma Omar nasa a tray, a palor ɗinsa takai masa babu kowa aciki alamar yana cikin bedroom ɗinsa, ajiye masa kawai tayi ta fuce, izuwa kitchen ta sake shirya wani a tray sannan ta wuce upstairs part ɗin BABBAN YAYA Haryanzu jikinta kerma yake, kuma bata fasa maganar shan poison ɗin nan ba, burinta ta sanya Sgr a idonta 4 the last time before tabar duniyar, Baiwar Allah Babu kowa a palor ɗinsa tsit kake ji sai ƙamshin dake tashi, shiga ciki tayi ta ajiye masa a saman table ɗinsa, Tsayawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya yayin da idonta ke cike taf da hawaye, kamar daga sama taji muryarsa ta cikin bedroom ɗinsa yana faɗin "who's There"? Runtse idonta tayi saboda jin sanyayyiyar muryarsa, daker ta dai daita natsuwarta tace "Tukur ne mai aiki," Voice ɗinsa tasake ji yace "Come In! i wanna see YOU Right now," zaro ido sehrish tayi jin abunda yace wato ta shigo ciki yana som ganinta 😳😳😳😳😳 Dake ta dai dai ta natsuwarta, ta tafi izuwa cikin bedroom ɗinsa kamar yarda ya umarta ta shiga da sallama"Assalamu alaikum" "Wa'alaikum salam" ya amsa mata, tsaye yake agaban mirror jikinsa sanye da sleeping dress riga da wando Milk colour masu ɗigon² baƙi ajikinsu ba ƙaramin kyau su kayi mishi ba, turarurruka yake ta fesa ma jikinsa, Sam tagaza janye idonta akan shi daker ta iya cewa "barka da dare" ya amsa mata da "Yawwa" sannan ta ƙara da cewa "Gani" Hannu yakai ya ɗauki kalbar turaren SHUMUKH ya feshe shi sannan ya mayar ya ɗauki wani turaren na Jar yana fesawa, mutun ne mai tsananin son ƙamshi shiyasa baya gajiya da bin jikinsa da turare, Shiru sehrish tayi zuciyarta na ɗar ɗar, kusan 15 minsa sannan Boss Man ɗin yace "Ni zan zo ne"? Ya tambaya yana jiran amsa, Cikin sauri sehrish ta ƙarasa hankali atashe ta tsaya daga bayansa jikinta na rawa, Cikin natsuwa yaso ma magana" Wacece ke"? Waro ido waje sehrish tayi jin abunda yace murya na rawa tace "Ni.....mai.....aiki...ne ...." a wani irin slow sgr ya juyo kai tsaye ya tunkare ta gadan gadan, a tsorace sehrish ke ja da baya tana kallonsa tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf a jikinta, Sam idonsa basa a kanta ƙasa suke, har sai da suka ƙurewa bangon gaba ɗaya, yarfa hannu sehrish ta shiga yi a tsananin tsorace take karanto addu'o'in da duk suka zo mata abakinta, kuma abayyane take yi saboda tsaban ruɗi tuni ƴan hanjin cikinta sun motsa, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar wadda sanyi yakama, Hannunsa yasa ya daki wall ɗin data ke manne ajikinsa ya aza hannun anan jikin bangon ya dafe sannan yace "ƙarya ke bana so arayuwata, am gonna ask u some questions idan aka min ƙarya za'a fuskanci matsala," Ya faɗi yayin da idonsa ke a lumshe tamkar a datse suke ba don komai ba sai don gudun kada mai aikin ya Sume a ƙaro na biyu saboda launin ƙwayar idonsa dake razanar da shi, . Kallon shi kawai take yi zuciyarta na bugawa da ƙarfi, daker take haɗiye yawu ga wani fitsari daya matse ta tunda taji ya ambace ta da mace tasan cewa ya gano ta kenan, "maca ce ko Namiji"? ya tambaya yana jiran amsa, Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi, muddin tamasa ƙarya wannan ba ƙaramin shaqa zata sha ba, Wannan shirun da tayi masa shiya fusata shi, buɗe Blue eyes ɗinsa yayi duka akanta , ta firgita sosai amma sam ta sanƙare ta gaza motsi da alama suman tsaye tayi Hannunsa yasa ya damƙi hular kan sehrish yayi wurgi da ita tare da mayafin duka, nan take sumar kanta tasoma warwarowa tana saukowa saman kafaɗarta, kyakkyawan sumar kanta mai matuƙan kyan gaske ga laushi, mayar da hannunsa yayi saman gashin bakin da take sawa ya cire shi shima, nan take ainihin kyakkwar fuskar reesh ta bayyana a matsayim mace 😊😉 sam fa bata motsi idonta sun kakkafe sun ƙame, kamar wata saƙago haka tayi, jinjina kai sgr yayi maganar Adams ta tabbata, yayi mamakin ganin yarinya ƙarama kamar wannan da ƙarfin halin Yin shigar Maza tazo gidan sojoji aiki, ko nawa aka biyata don tayi hakan? Ya tambaya aransa, sam shi baya tunanin ta haura 12years saboda ƙarantarta dayake gani agabansa Ko shouder ɗinsa tsayin sehrish bai kai ba, daga tsaye inda yake yana kallon tsakiyar kanta saboda ba ƙaramin tsayine dashi ba, kowa yazo gabansa kallon ƙarami yake masa, Janye hannunsa yayi daga jikin wall ɗin da sehrish take sannan yayi tattaki izuwa inda fridge ɗinsa yake, buɗewa yayi ya ɗauko bottle water mai sanyi sannan ya dawo inda take tsaye, ya buɗe murfin ya yayyafa mata, a wani irin firgice sehrish ta girgiza ta dawo in sense ɗinsa, sai faman zazzare kyawawan idanunta take, bin chest ɗinsa tayi da kallo izuwa face ɗinsa cikin tsoro, hannu tasa ta shafa sumar kanta gabanta ne ya faɗi jin wayam babu yar hularta, hankali tashe ta wurga idonta inda sgr yayi watsi dasu.........nan fa tashiga faɗin "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un dan Allah kayi haƙuri.....nashiga ukuna........' tana kuka tana magana , gaba ɗaya yayi mata rumfa tamkar Zaki haka take ganin sa agabanta 😳😳😳 Idonsa na kumshe yana sauraronta left hands ɗinsa na riƙe da bottle water ɗin, yayin da ɗayan hannun kuma ya mayar dashi jikin bangon ya dafa, sehrish kuma na agabansa suna fuskantar juna, "haɗiye wannan kukan bana so" cikin hanzari sehrish ta dakatar da kukan tashiga taitayinta, bakomai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47