Chapter 2
Chapter 2
yau sun ƙyale mu basuyi mana komai ba, Jahad ce ke wannan maganar wadda ke atsaye tana kallon hosana, Murya na rawa hosana tace "Jahad naji abunda su Hafsat ke cewa ita da Momynta," "Me suke cewa ne"? Ta tambaya tare da matsawa kusa da Hosanar don taji dakyau, Hosana ta kora mata bayani tun daga farko har ƙarshe, Jahad ta jinjina kai tare da cewa "Ashe buri yayi kama da mutun, shiyasa ta tsane mu kenan saboda tana tunanin cewa Omar zai iya son ɗaya daga cikinmu, ran nan tace mun batason mune saboda mun shiga tsakaninta da abun harin ta, Yanzu nagane inda ta dosa, To amma wacece matar da hafsat ta haɗu da ita yau? Wadda ke son A zubar mata damu!? "Ni inaji araina jahad so suke su rabamu da ƴa'ƴa Omar kawai," hosana ce tayi maganar ido cike tab da kwalla don bata son duk wani abu yanzu dazai rabasu da Omar, "Insha Allah burinsu bazai ta6a cika ba Hosana, baza su iya raba mu ba da yaya omar ɗinmu," tayi maganar tare da janyo hosana suka rungume junan su __________________________________________ Tuni sun kammala aikin su na dinner, har sun kammala jerawa a dining Kowa ya bama cikinsa an ware, yanzu gidan ya ragu ba laifi kasancewar tun week ɗin daya wuce aka tura mutun Huɗu Aiki, Irfan jabeer, khaleed da Fawan duk basa nan, yanzu wanda suka ragu Acikin gidan Haroon, twins, junaid, Sai Marshal Omar da Sgr duk da basu cika zama cikin gidan ba suma, always working saboda suna bada gudummuwa sosai shiyasa koda yaushe suna headquater ɗinsu don ana buƙatarsu sosai game da insecurity ɗin qasar tamu, kasancewarsu kwararrune a6angaren aikin soja dama sun kasance international Armies, kowace ƙasa aduniya suna bada gudummuwarsu wurin kame tantirai sune maganin ƴan Iska, shiyasa sunansu ya shahara a faɗin duniya duk inda suka je, ansansu girmamasu ake gani kamar kamar me (Tiger da Lion) Kenan ba wasa 😇😇😇 SEHRISH Shiga bedroom ɗinta tayi Wurin isha prayer, duk ta rame kamar ba Reeshi ba, alwala ta ɗaure a toilet, ta shimfiɗa sallaya, ta gabatar da salla, bayan ta kammala ta naɗe hijab da sallayar ta tura a wardrobe ɗinta, komai nata a slow take yinshi saboda rashin kwarin jikinta da fargabar da take fama dashi na Haroon, Haye wa tayi saman gadonta tare da janyo pillow ta rungume tunani kala kala a ranta, hawaye ne suka soma gangarowa daga idonta sbd tuna yadda haroon ke ta6a jikinta, hannu tasa tana share su, daga bisa ni tayi lamo tana tunanin duniya, Tana cikin wannan halin taji an kwankwasa ƙofa, shiru tayi bata Yi magana ba cike da tsoron waye ke mata knocking, ji tayi an sake buga ƙopar muryar na rawa tace "wanene"? Muryar junaid taji yana cewa "Sehrish ni ne," Ajiyar zuciya tasaki jiki na rawa ta sauko tare da karasawa wurin kopar ta buɗe, Gabanta ne yayi mugun faɗuwa ganin haroon hankali tashe tace "Kaineeee !!!!" a tsorace tayi maganar jikinta na rawa,. Fashewe da dariya haroon yayi tare da wuce ta yashi ga ciki yana cewa "ƴar shila ni ne, ae nasan bazaki buɗe ba shiyasa nayi maki muryar junaid don na lura kuna good time dashi,' juyowa tayi tana bin shi da kallo a razane,. "Me ya kawo ka"!? "Abunda yasa ba kawo ni, Yau nazo ne ayi ta taƙare, Haƙƙina nake son ki bani," Cikin shessheƙar kuka sehrish tace "Me kake nufi wai !!! Wani haƙƙi ka ke dashi akaina? Dan Allah kabarni nayi rayuwata cikin salama !! Ka rabu dani mana !! ta6e baki haroon yayi tare da cewa "Na amince zan rabu dake, amma bisa sharaɗi ɗaya"? Ya faɗi yana kallonta fuska a ɗaure, a lokacin tadawo tsaye front of side drawer ɗinta tana facing ɗinshi, Gabanta na faɗuwa tace "Menene shi"? Cikin sanyin murya tayi maganar Haroon yace "Your Virgin!! shine abunda nake so,and if u do so i wll be out of ur life" Fashewa da kuka sehrish tayi cikin tsananin jin ƙunci da raɗaɗi aranta, tuni zufa tagama wanko mata kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwa, tsanar haroon take ji kamar kamar me, tarasa amsar da zata bashi sai faman kerma take, A tsawace haroon yace "Ke !!! Ki amsa mun kin amince ko baki amince ba"!? A Firgice tace "Na'amince" ita kanta batasan ta bashi amsar ba saboda tsoratar da tayi da tsawarsa, Wani irin shu'umin murmushi haroon yasaki, bin shi da kallo tayi ganin yasa hannu yana zare belt ɗin wandonsa, tuni ta runtse ido ganin gashin jikin shi, bakomai ya faɗo mata arai ba fa ce Sgr shine namijin da take so tafara kasancewa dashi arayuwarta bata buƙatar wani namiji in ba shi ba, shi take so ta mallakawa komai nata muddin ta mallake sa, Jiki na rawa ta zura hannunta ta baya, taci sa'ar damƙar fititalar Kwan dake gefen gadonta, kafin haroon ya ɗago ta daddage da iya ƙarfin ta na ƙarshe ta ɗago da fitilar dake hannunta ta kwaɗa masa a tsakiyar kai !!!!! Ji kake KWASSS !!! A razane haroon ya ɗago jin saukar fitilar kafin yayi wani yunƙuri tuni Sehrish tabi ta gefensa ta watsa da gudu sai cikin toilet ta datse ƙopa sosai, ta sulale daga jikin ƙopan zuƙunne tana kuka don tasan dole haroon ya ɗauki matakin abunda tayi masa, Ba ƙaramin buguwa haroon yayi ba, don wurin harya fashe Ae kuwa rai a tsananin 6ace yace "Ke don ubanki ni kika fasa ma kai"? Sehrish dake acikin toilet murya cike da kuka tace "Ba dai ubana ba sai don Uban Mai zagi !! Fasiƙi ɗan iska insha Allah bazaka ta6a cin nasara akaina ba, sai Allah ya nuna maka iyakarka, wulaƙantacce kawai ƙazami mai warin baki," Tuni idon haroon sunyi jawur kamar garwashin wuta, ransa yayi mugun 6aci bai ta6a tunanin yarinyar zata iya mayar masa da martani ba, amma sai gashi yau ta zage shi tass, "Bazan ƙyaleki ba, sai na wulaƙanta rayuwarki ba dai kina acikin gidan nan ba kuma zaki fito ba, zamu haɗu ne wlh," Ya faɗi tare da tunkarar hanyar fita yana mayar da belt ɗin wandonsa daya fara cirewa,.(ba'aci nasara😂) Sehrish batayi shiru da bakin ta ba taci gaba da cewa " Ta Allah bata ka ba wlh !! Mugu azzalumi mummuna kawai, da wasu idanuwan ka kamar na Mujiya ni ina kokwanton Cewa anya kai Jinin Abban sojoji ne !! Sbd duk ƴa'ƴansa ba Fasiƙi irinka," Jinjina kai haroon yayi kawai yana huci, ya tura ƙopar ɗakin ya fuce, Wani sabon kukan ta sake fashewa dashi, tana faɗin "wayyo Allah na nasan haroon baxai ƙyale ni ba, nashiga uku........' Jiki na rawa ta miƙe ta nufi wurin bathroom cabinet ɗinta, akwai wasu Chemicals dake ajiye cikin toilet ɗin masu illah ga jikin mutun tamkar poison suke, ta riga ta yankewa kanta shawarar kwara ta kashe kanta ta huta da fitinar haroon, Hannunta har kerma yake yi, wata ƙaramar roba ta ɗauko mai ɗauke da chemical ɗin, buɗe murfin tayi yayin da idonta ke zubar da hayawe, bakowa ya faɗo mata arai ba face Hosana Jahad, junaid, Aunty azmee uwa uba Burin ranta, yanzu shikenan duk zata rasa su? Zata mutu tabarsu? Runtse idonta tayi aranta tana faɗin "bani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47