Chapter 10
Chapter 10
halayanka Abba ba abunda zamu ce sai dai Allah yaci gaba da tsare mana kai, ya tsare zuri'arka, Ya kare ka daga sharrin mahassada da maƙiyan ka, Allah yaci gaba da ɗaukaka darajarka da ta ƴa'ƴanka a faɗin duniya, kamar yadda kake faranta ma wasu Kaima Allah ya faranta maka aranar gobe ƙiyama yasa Aljanna tazama makomarka................azmee bata tsaya ba haka taci gaba da yiwa Abbansu addu'oi' dasu kansu , gaba ɗaya sunji daɗin addu'o'inta kuma dukkansu suke amsa mata da Ameen ameen, daga bisa ni kowa ya mayar da hankalinsa ga abincin dake agabansa zanso kuka sehrish duk ta gaza samun natsuwa ba wai don bata jin daɗin kasancewarta atare dasu ba, sai don tsoran su ayaan da jahan da take yi, saboda wani irin kallo da suke mata Sam tagaza gane kallon menene wannan, dama fa su ƴa'ƴan Alexandra wuyar sha'ani ke gare su kamar uwarsu haka suke basu cika yarda da mutane ba ko kuma sake musu, junaid ne kawai mai sauƙin kai saboda kaf halayansa shigen na Abbansu ne, shin wai ina haroon ? Ae tuni ya koma cikin bedroom ɗinsa cikin tsananin ƙunci ransa yayi mugun 6aci sai faman yawo yake a ɗakinsa cike da jin baƙin ciki aransa sai faman huci yake bakowa yafi bashi haushi ba face Abbansu da Babban yayansu saboda sune suka nuna Amincewarsu da ita, a can ƙasan zuciyarshi kuma bakowa yafi ƙuntata masa ba fa ce*JUNAID* Saboda shine silar komai daya fara sanar da Abbansu akan maganar yarinyar, dama junaid ya jima yana ci masa tuwo a ƙwarya don ya lura Yaron Abbansu yafi Son shi fiye da kowa tunda har bai iya 6oye son da yake mashi agaban kowa, Kuma ya Lura cewa Babban yayansu ya mutu akansa hakan na nufin shima Yafi Son*JUNAID* bama su kaɗai ba kowa na gidan in kana so kaga fusatar shi to ka ta6a junaid nan xaka ga tashin hankali, shiru yayi a lokacin ya koma gaban mirror ɗinsa yana kallon fuskar shi ta cikin madubi, a fili yace "saboda*Junaid* Abba da Babban yaya suka mare Ni, a gaban ƙanne na, mutun Uku da suka kasance maƙiya na acikin gidan nan muddin inaso In ƙuntata musu dole saina Cutar da *JUNAID* 😳 ya faɗi tare da sakin wani irin shu'umin murmushi yace "Haroon kenan Mai Fuska biyu ! Wasu suna mun kallon shashasha ɗan giya yayin da ni kuma nake masu kallon garori wannan Alwashi ne na ɗaukarwa kaina saina Tarwatsa farin cikin gidan nan kuma ba da kowa zanyi amfani ba fa ce *JUNAID* 👌💔 "na'am " ya amsa yana Satar kallom sehrish da ta kira sunan shi ta wutsiyar idon shi, "nifa tsoro nake ji junaid nagaza cin abincin dake gaba ba," murmushi junaid yasa ki tare da cewa "CALM DOWN your mind reesh, ke fa ynx ƴar gida ce, ki saki jikinki ki ci Abincin ki a natse," murmushi tasaki yayin da ta sa hannu cikin plate ɗin dake gabanta mai ɗauke da fried chicken taci gaba da ci, ta6e baki Jahaan yayi yana kallonta aransa yace " ƴar shisshigi da kutsu bansan daga ina aka samo wannan yarinyar ba yanzu haka bata Wuce Zariyya dama gata nan kamar Zararrriya sai faman zare ido take,' ya yi maganar yana Hura hanci kamar wanda akayiwa dole yana Cusa bugger abakinsa, Ayaan kuwa cewa yake yi aransa "ƙarfin hali irin na Ifritanyar nan kalli yadda ta wani shige tsakanin Abban mu da junaid tana cin abinci ita ga isasshiya mai walkin sa, ala dole ga ƙanwar Sojoji zaki gane kurenki ! Jibi kunnuwanta don Allah kamar na Zomo falo falo sai faman ƴan ƙefce ƙefcen ido take kamar wadda aka aza A saman kujerar lantarki......,😂 Har cikim ranta sehrish duk ta tsargu da su Twins kamar tasan abunda suke cewa aransu, Azmee ce keyi mata alamar ta kwantar da hankalinta don itama ta lura da abunda su twins ke mata, wani irin Kallon hadarin Kaji 😾😼 Tuni sgr ya bar dining ɗin dama breakfast ɗinsa shaf shaf yake yinsa gyaran murya Abbansu yayi ya kalli azmee yana cewa "idan mun kammala ku shirya ke da sehrish da Junaid saboda yi wa daughter siyayyar kayan sawa da abubuwan amfani na mata, hada ma Saloon da gyaran jiki duka komai nake so ayi mata,' Atare Jahan da Ayaan suka ɗago suna kallon Abban nasu, shima kanal yusif abun ya basa mamaki, Sehrish kuwa murmushi kawai take saki haka Junaid daɗi kamar ya rufe sa, Azmeee tace "To Abba Insha Allah komai za'ayi mata," "Ke ma hada ke, azmee siyayyar duk zakuyi," cike da farin ciki azmee tace "Mun gode sosai Abba Allah yasa ka da alkairi," mayar da idonsa Abban nasu yayi kansu Ayaan da jahan da kanal yusif yace "Bafa ni zan biya kuɗin siyayyar ƙanwarta ku ba, wannan nauyin ku ne, don haka kowa ya tattaro ya bada gudummuwa, babu wasa a fuskar shi yayi maganar, shiru su kayi don baza suyi mashi musu ba, Abban nasu yaci gaba da cewa "Yusuf kai zaka biya kuɗin siyayyar kayan sawanta, Jahan kuma shi zai ɗauki nauyin kayan ado na mata da za'a siya mata, sannan Ayaan shi kuma zai ɗauki nauyin na gyaran jiki hada takalma da bags ɗin da za'a siya mata ina fata duk kunji," sam takaici ya hana twins yin magana bawai kuɗin bane damuwarsu ba sam basu da matsalar kuɗi saboda bada albashinsu suka dogara ba, Mahaifiyarsu duk ƙarshen wata tana tura masu makudan kuɗi dollars wannan ba tare da sanin Abbansu ba ko Babban yayansu ba, haushin su yarinyar da aka ƙaƙaba musu wadda basu san daga ina aka tsinto ta ba, gashi kuma har ana ɗaura musu responsibilities ɗinta, "Naji kunyi shiru"? Abbansu ya tambaya yana kallo su, Kanal yusif yace "Atm ɗin yana a cikin side drawer ɗina, junaid yaje ya ɗauko in zasu tafi," Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa "Haka nake son ji ku fa"? har suna haɗa baki wurin cewa "akwai kuɗi cash a ɗakin mu junaid yaje ya ɗibi yarda zai ishe su,in kuma Atm suke so shima yana anan saman mirror muka barshi...." suna magana suna yatsina fuska irin an musu dolen nan, Kanal yusif yace "A'a Abba ba sai sun bada nasu ba, kawai suyi using da Atm ɗina zasu ishe su har ma su rage," acewar kanal yusif, Abban su yace "a'a ni nafison su sauke nauyin dake akansu na ƙanwarsu yakamata tun yanzu su son yadda zasu ɗauki ɗawainiyar mace kafin Allah yasa lokacin auransu yazo," . atare suka haɗa baki wurin cewa"Aure kuma Abba," "Eh mana" ya amsa musu, Kallon Ayaan jahan yayi tare da cewa "tashi mu tafi lokacin aiki yayi " miƙewa Ayaan yayi yana cirar tissue yace "Abba mu mun wuce," Murmushi Abbansu ya saki tare da cewa "adawo lafiya, aure dae ba fashi in lokacinsa yayi mutun ko bai so saina ɗaura masa in yaso ya haɗiyi zuciya ya mutu, zan zauna in ta zuba muku ido ne," fashewa da dariya junaid yayi bashi kadae bama hada su azmee da sehrish, kanal yusif dae murmushi kawai yayi, Na wani lokaci kowa yabar dining ɗin cikin zumuɗi sehrish ta wuce don ta shirya zasu tafi Shopping mall ɗoki har ba'ayi, shima junaid
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47