Skip to content

Chapter 35

Chapter 35

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fito ta wuce upstair domin takai masa, tana hawa saman stairs ɗin sai ga SGR shi da Marshal Omar suna nufo stair ɗin, ganin su zo dab da benen yasa ta saukowa gaba ɗaya don tabasu wuri su wuce, dukansu suna sanye da jean da t-shirt, sai faman sauri suke alamar akwai wani Uzuri dake gare su, suna ƙarasowa inda take tsaye tayi saurin cewa "ina yinin ku," Omar ne kawai yasamu damar Amsa mata, amma shi SGR sam ko kallo ma hasalima baisan da mutun a wurin ba, gabanta ne ya faɗi don alamu sun nuna cewa ba ƙaramin abubane ganin yanayin fuskar kowannansu Especially Omar da ta sani, Kullum cikin sakar mata fuska yake duk in suka haɗu amma yau dakyar ya amsa mata gaisuwarta, Bin su tayi da kallo, yayin da suka wuce kai tsaye hanyar fita falon suka nufa, har sun kusa fita Omar ya juyo ya kalle ta, bakomai yasa Shi juyowa ba fa ce tuna Hussana da jahad yau tsawon wata kenan baije ya dubo su, saboda busy ɗin daya shiga, yana da burin zuwa ɗaukosu amma aiyuka sun hana shi, Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da kansa suka sa kai suka fuce, sam sehrish tagaza yin motsi da ƙafafunta, hakanan ta dunga jin gabanta na faɗuwa, bata kai ga hawa benen ba, taji dirar motoci cikin gidan nan take ta sake jin faɗuwar gaba, cikin sauri ta haye upstairs ɗin da hanzari ta shiga bedroom ɗin junaid a lokacin yana cikin toilet yana wanka, ajiye masa tray ɗin tayi saman table, sannan tafito da sauri-sauri ta fito daga babban falon ta tsaya abakin ƙofar shigarsa, . Kamar dai ranar da SGR da Omar suka zo Nigeria tare da uban security guards na sojoji haka yau ma, tsoro ne yakama sehrish gudun kar ace US zasu koma, Tana ganin lokacin da suka shiga cikin motocinsu kuma nan take motocin ajere suka nufi dogon titin da zai fidda ka daga cikin gidan, Komawa ciki tayi da gudun gaske ta faɗa kitchen tana faman kwalama aunty azmee kira, a ɗan razane azmee ta juyo ta kalle ta tare da cewa "Sehrish lafiya kuwa kike ta faman kwalamun kira haka!? Cikin tsananin tashin hankali tace "Aunty azmee meke faruwa ne? Yanzun nan naga Babban yaya tare da Yaya Omar, sun fito fuskokinsu ba annuri kuma ga tarin motoci can sun fita dasu," tsayawa azmee taɗan yi jimmmmmmm tana ɗan tunani kafin tace "Tabbas ina hasashen cewa Us zasu tafi Saboda ɗazu da safe naji ƙishin-ƙishin ɗin cewa Momynsu matar Uncle ɗinsu donald tana fama da blood cancer, To ina da tabbacin cewa kodae ta rasu ne...........' Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali take furta "Innalallahi wa'inna ilairaji'un Allah yasa bata mutu ba, Yanzu shikenan in suka koma ko yaushe zasu dawo.....' Murmushi Azmee tayi kafin tace "naga kin tayar da hankalin ki, nasan saboda Tafiyarsu Rafayet ne bawai don jin mutuwar ba, Hannu sehrish tasa tare da rufe fuska saboda hawaye da taji sun tafo mata, bin ta da kallo kawai azmee tayi cike da mamakin ganin tana shessheƙar kuka, Matsawa tayi kusa da ita tare da dafa ta tace"Sehrish !! Wannan kukan na menene? Ba dai don tafiyarsu bane? shiru kawai tayi batare da tace komai ba, ita kaɗai tasan me take ji aranta, gaba ɗaya fuskarta ta damuje da hawaye, Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Ki koma ɗaki ki kwanta kawai," Cikin kuka sehrish tace "a'a aunty azmee zanyi aikin," Azmee tace "a'a banaso ki tafi kawai zan ƙarasa abuna," Juyawa sehrish tayi tare da fuce wa daga kitchen ɗin ta koma bedroom ɗinta, saman gado tafaɗa tare da cigaba da kukan, To fa sehrish komai yasata yin kuka? Allah wa'alamu, Azmee kuwa ta jima tana mamakin dalilin kukan Sehrish tarasa gane mata, aranta tana cewa "Badai saboda tafiyar SGR take kuka ba? Don ta lura da yadda sehrish ke matuƙar ƙaunarsa, sam bata iya fira batare da ta, Amabaci sunan shi ba ita dae kawai tafison jin Ana maganarsa,nan zakaga sakewarta, "Lallai ne akwai Babbar Matsala, muddin abunda nake zargi ya tabbata,ya zama dole in ja ma Sehrish burki, don gujema kamuwa da CIWON ZUCIYA,"!! Azmee ta faɗi acikin ranta, _______________________ Sehrish kuwa Tuni wani Irin zazza6i taji ya rufe ta lokaci guda, jikinta har kerma yake yi wurin janyo bargonta dake asaman gadonta ta lullu6e jikinta dashi, tana faman fidda numfashi mai zafin gaske, sam tarasa ina zata tsoma ranta ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta Har wuraren Sallar Magrib sehrish bata motsa ba, tana nan yarda take ƙudundune cikin barko,tamkar mai bacci alhalin nan Idonta biyu jikinta ne kawai da bayayi mata daɗi, Acan ciki kuwa fitowa junaid yayi bayan yasha baccin sa, ya sauya kayan jikinsa izuwa riga da wando, lokacin daya sakko down yayi mamakin ganin Azmee ita kaɗai tana faman jera masu dinner a dining, ƙarasawa yayi cikin sauri yana cewa"Aunty Azmee ina sehrish ɗin ne? Ita bazata fito ta tayaki ba? Azmee ta ɗan ɗago ta kallesa tare da cewa "Junaid ni kaina bansan meke damun Sehrish ba, Lafiya lou fa muke aiki da Ita, amma tunda tazo ta tambaye ni game da babban yayanku da Omar da taga sun fito fuskarsu cikin wani irin yanayi, kuma taga Sun fita tare da motoci dayawa, shine nake ce mata may be Us zasu je, tunda ɗazu da safe naji ƙishin ƙishin ɗin cewa Matar Uncle ɗinku donald tana fama da blood cancer may be ta rasu ne.....shine fa kawai sehrish takama kuka har nace mata ta koma ɗakinta kawai ni zanyi aikin," ta ƙarasa maganar cikin damuwa, Junaid kuwa shiru yayi hankalinsa ya rabu gida biyu, sam ya rasa gane inda maganar Azmee ta dosa, cikin mamaki yace "Us kuma? Taya babban yayan mu zaibar ƙasar nan batare da sani na ba? Anya kuwa aunty Azmee am just doubting about it bana tunani Us zasu je, kuma Matar uncle donald bana tunanin ta rasu gaskiya, tunda da naji ko a wurin Abban mu ne, Ni dai Allah yasa ba wani abu bane ya faru mummuna," ya faɗi cikin tashin hankali kafin ya wuce yana cewa "Bari naje wurin Sehrish ɗin naji meke damunta," Azmee tace "to shikenan," A hankali ya tura ƙopar ɗakin yashiga da sallama, tsayawa yayi yana kallonta yarda take ƙudundune cikin bargo, A hankali ya kira sunanta "Sehrish..........' shiru bata amsa masa ba, ƙarasawa yayi izuwa gab da gadon nata yaɗan zauna gefe tare da sa hannu ya yaye mata bargon dake jikinta, dogon numfashi taja tare da cewa "Junaid ka mayar mun da bargona, Sanyi nake ji," Junaid yace "Reesh wai meke damunki ne? Aunty azmee ta faɗamun cewa kinbar kitchen kina faman kuka? Cikin kuka tace "Junaid wai dagaske ne cewa Babban yaya da Yaya Omar us zasu koma yau? Sakin baki junaid yayi yana kallonta cikin tsananin mamaki amma bai kawo ma ransa komai ba sai cewa yayi "Sehrish dama akan wannan kika shiga damuwa? to ki kwantar da hankalin ki, Yaya Omar da yaya Rafayet bana tunanin sun bar ƙasar nan ne, Aunty azmee ce kawai tace maki hakan a hasashen ta, just calm down ur mind My lovely sis... . ...........jin

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47