Chapter 4
Chapter 4
take kallo ba fa ce damtsen hannunsa, tunani kawai take yarda zai kai mata naushi tabbas tasan sai dai Uwarta ta haifi wata (Hafsat bature ana magana) 😂 Cikin natsuwa yasoma magana__________________________________ Abt payment 300 ne, still muna free pages ne wanda suka shirya 08103884440 sumin magana 👍 *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* *🔥The Father Of Soldiers🔥* ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖 *Story & Written by* *Hafsat Bature Muhammad* ~💋BOSSLADY💋~ _Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo💫_ *Abban Sojoji part 2* *EPISODE 2* *💞LAFAZI WRITTERS ASSOCIATION*💞 Cikin natsuwa ya soma magana "tambaya biyu kawai Wacece ke? Kuma waya turo ki"? Cikin rawar murya sehrish tace "Ni ba kowa bace ba, kuma babu wanda ya turon.......'. Interrupting ɗinta yayi da cewa "ki mun magana a hankali don bana fahimta sosai," Gyara muryarta tayi sannan taci gaba da cewa "Sunana Sehrish, kuma ni babu wanda ya turo ni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, aiki kawai nake don nasamu kuɗi........' buga wall ɗin da yayi yasata dakatawa a tsorace "Nace wa ya turo ki!!? Hankali atashe tace "Allah shine shaidata, wlh ni babu wanda ya turoni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, ƴan uwana ne Basu lafiya an kwantar dasu asibiti ana buƙatar kuɗin aiki shine na nemi aiki gidan wata hajiya...............sehrish bata 6oye masa komai ba ta faɗa masa tass dalilin zuwanta da dalilin yin shigarta na maza batayi masa ƙarya ba ko kaɗan, ta ƙarasa masa labarin tana faman zubda hawaye tsoranta wane hukunci zaiyi mata don tasan watan Cin Ubanta ya tsaya, shiru su kayi na wani lokaci, kafin daga bisa ni Babban yayan yaja da baya ya juya bedroom ɗinsa ya shige kafin daga bisa ni, ya fito hannunsa ɗauke da wayarsa wuri yasamu ya zauna saman sofa ɗin sannan yaba sehrish damar ta matso kusa, sai da tafara tattara hularta da mayafin da yayi watsi dasu, ta ruƙesu a hannunta sannan jiki asanyaye ta matsa inda yake kamar wadda tayiwa sarki ƙarya, jikinta sai faman kerma yake, yace "su nan su? da sunan state da sunan hospital da aka kwantar dasu? and the date!? Murya na rawa tace "Hosana Sayyad, da jahad sayyad an kwantar dasu a Fmc katsina........" duka ta faɗa masa hada date ɗin da aka kwantar dasu duka don bata manta ba, danna wayar yashiga yi kafin daga bisani ya danna calling, ta soma ringing, nan take aka ɗaga wayar suka soma magana, Duk sehrish na tsaye tana kallonsa yadda yake speaking anatse, Bakowa ya kira ba face Babban Likita, dama already sai da yafara tura masa message na sunan yaran da bayanan dayake son sani sannan yakira, kuma anci sa'a On duty yake,' Tabbas yayi mamakin ganin kiran Surgeon general rafayet, kuma yayi mamakin jin sunan yaran da yakeson aduba mishi files ɗinsu, tabbas yasan yaran, waɗanda Omar ya taimaka daga wurin Police, ranshi ne ya bashi cewa may be Omar yasanar mishi game dasu ne that's why yake neman Information akansu , without wasting time Babban likita ya binciko masa files ɗinsu Hosana Da jahad na rashin lafiyarsu duka bayanan ya masa snaping dinsa ya tura masa ta whatsapp ɗinsa, bayan sun kammala phone ɗin, Sgr ya shiga whatsapp ɗinsa ya duba, sai ga Files ɗin yaran na rashin lafiyarsu raɗau da sunansu ajiki Hosana Sayyad Da Jahad Sayyad, Ajiyar zuciya yasaki yanzu ya shaida maganar Yarinyar duba time yayi dare yayi ga wani bacci daya ke ji gashi ko dinner ɗinsa bai cin ba, Ga yarinyar nan dake tsaye duk a tsorace don yana ganin yadda yatsun ƙafarta ke kerma, gyaran murya yayi sannan yace "You're not guilty of anything, the mistake you made shine shiga na maza after knowing that it is forbidden in Islam for a girl to dress like a male,' yayi maganar yana danna wayar hannunsa... Murya na rawa Sehrish tace "bazan ƙara ba........' Jinjina kansa yayi kafin yace"As from now i don't wanna see u wearing this dress again! u can go" ya bata Umarni ta tafi Wayyo Allah sam sehrish ta gaza rufe bakin ta don mamaki, kama hanyar fita tayi tana waiwayansa da kansa ya shiga saving dinner ɗinsa yana ci, Tsantsar farin ciki ne ya cika sehrish sam ta rasa inda zata tsoma ranta, ae tana fita daga part ɗinsa ta buga Wani uban tsalle na murna fuskar nan kamar wacce akayiwa Albishir da gidan Aljanna, watsa wa tayi da gudu gudu sauri sauri tana tattaka Stairs ɗin tana saukowa down a babban falon dama ba kowa nan fa tashiga rawar murna tana zagaye sofas ɗin dake a falon kamar wata yar baby, Duk wannan abun da take yi akan idon Sgr domin kuwa ya biyo bayanta ashe yana daga can Upstairs yana kallonta, don bai cika yarda da mutane ba shiyasa yayi following back ɗinta don yaga reaction ɗin da zata yi bayan da ta fita daga part ɗinsa, abunda yayi tsammani ba shi ya gani ba, zura hannayansa yayi cikin aljhun wandon baccinsa yana kallon Ikon Allah, Sam sehrish bata son babban yaya yana kallonta ba, ita kaɗai tasan farin cikin da take ciki, ta jima tana mamakin yarda Sgr ya kasance mai matuƙar sauƙin kai har haka a tunaninta zai bata horo mai tsanani daga nan akore ta kuma daga gidan, Nace "*Sehrish ba ke kaɗai ba hatta Hafsat bature da sauran makaranta labarin rayuwarki sunyi tsammanin hakan tabbas Surgeon general Rafayet ya bamu mamaki, haƙiƙa shi ɗin na daban ne*"😍 Yanzu abunda ya rage wanda take yi ma fargaba shine sauran matasan gidan shin zasu amince a ranar da ta bayyana kanta a matsayin mace !? Uwa uba Abban su,kuma tuna wannan yasa jikinta yin sanyi, dakatawa tayi daga yin wasan da takeyi na zagaye gujerun babban falon, jiki a mace ta kama hanyar bedroom ɗinta, ranta ne ya bata cewa akwai mai kallonta, Cikin sauri ta juya ta kalli upstairs a time ɗin har sgr yabar wurin ya koma part ɗinsa Ganin wayam yasa ta sauke ajiyar zuciya,ba ɗakinta ta wuce ba ɗakin aunty azmee ta wuce don sam tagaza daina murna tafison ta sanar mata abunda yafaru yau ɗin nan da zafi zafinsa, Haryanzu hannunta na ruƙe da hularta da mayafin duka ta ƙanƙame su, tsayawa tayi a ƙopar ɗakin tana bubbugawa , Azmee dake zaune saman darduma tasha hijabi ajikinta ga qur'ani agabanta hannunta kuma na riƙe da Cazbaha sai faman gyangyaɗi take yi, jin bugun ƙopa yasata cewa "Wanene" sehrish dake tsaye a bakon ƙopan tace"Nice aunty azmee" Murmushi azmee tayi tare da cewa "Ashe bakiyi bacci ba," tayi maganar tare da tashi daga dardumar ta buɗe mata ƙopa, Shiga ciki sehrish tayi tana faman zabga murmushi, a ɗan ruɗe azmee ke kallonta bayan ta rufe ƙopan tace"Yau wata rana! Sehrish kece da Murmushi haka a fuskarki? Wane albishir ne akayi maki?Cos I forgot when last naga wannan annurin a face ɗinki" cikin mamaki azmee ke wannan maganar kafin ta mayar da idonta kan Hular sehrish dake ruƙe a hannunta ta kuma cewa "Ikon Allah yau kuma hularce da mayafin duka a hannu? Dariya kawai sehrish take yi daker ta tsagaita tace "Aunty azmeee abun mamaki! Abun farin ciki !" Cike da ɗoki azmee tace "menene shi? Nan sehrish ta shiga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47