Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

tsayi nan nan nake ɗaukarka kana yaro har goya ka nake yi," duk Omar na jinsu yana murmushi kawai saboda atare suka jera suka nufi cikin gidan, ɗan gyaran murya yayi tare da cewa "Abba yanzu ae sai dai ka goya grandchild dinka masu zuwa," Omar ya faɗi, Abban su yace "hmmmm taya hakan zata faru bayan ƴan bukulu sun hana ruwa gudu, burina kenan kullum kamar yadda na haifa nima nawa su haifa amma abun takaici duka ya'yan nawa babu wanda ya ajiye ko budurwa bayan ni tun ina 20 years aka sanƙamamun aure muka sha soyayya gaba ɗaya,' Omar yace "Kada ka damu Abba, Insha Allah burin ka zai cika, in har hakan zaisa ka farin ciki, kawai acigaba da yi mana addu'a,' Jinjina kai abbansu yayi yana ɗan kallon SGR dake gefensa shiru tamkar baya jin me suke cewa, Ruko hannunsa yayi cikin nasa sannan yace "kai fa Son, Naji baka ce komai ba ? Ko baka son farin ciki na ne? yatsina fuska yayi tare da cewa "In dai yaron da zaka goya ne zan kawo maka shi,' "Uwar fa"? Abban ya tambaya adai dai lokacin da suke shiga babban falon SGR yace "Babu," dariya omar kawai yake yi.abbansu kuwa baki sake yace "Shege zaka kawo min,'? "Ko baka so ne"? Sgr ya tambaya shima da zolaya, Abbansu yace "Ae da babu gwara ba daɗi, akawomin inaso," Omar yace "So funny wlh, abba son jikokin harya kai haka, to. Insha Allah ba shege acikinsu, Original zaka samu daga gurin kowan nan mun, ' cike da nishaɗi suke fira kamar bazasu iya rabu ba, wuce wa Abbansu yayi part dinsa, shima SGR tare da OMAR suka wuce Uptairs nasu parts din, 💪 Tun da Omar ya shiga bedroom dinsa ya rage kayan jikinsa toilet yashiga ya yi wanka, yafito ya zura kayan baccinsa, har cikin ransa yaso ya kira Aunty babba don abasu Hosana yaji Muryarsu amma ransa yana bashi cewa yanzu sun isa suyi bacci, wannan dalilin ya hana shi calling ɗinsu, Fitowa parlor dinsa yayi yasamu wuri saman sofa yazauna hannunsa ruƙe da wayarsa, sai lokacin yake dana sanin rashin daukar su hosana da jahad hoto ya ajiye acikin wayar shi koya samu na rage kewarsu, yana cikin wannan tunanin wayarsa ta soma ruri karatun kur'ani Ne ringin tone dinsa duba sunan daya bayyana a screen dinsa yayi nan take sunan*ABUSUFYAN*ya bayyana muraran, Cikin hanzari ya ɗaga ya kara a kunnansa "Assalamu Alaikum Uncle Sufyan yau an tuna dani ne"? On ther other hand ABUSUFYAN yace "Ko da yaushe cikin tunawa nake yi dakai Omar, nayi trying number dinka dazu baya shiga, kuma na jaraba ta RAFAYET tana ringing amma bai ɗaga ba,' Omar yace " Kash ! rashin sani ɗazu ne na kashe wayar muna aiki ne shiyasa," Abusufyan yace "Dama inaso na maka magana ne About wannan yaran da goggon katsina ta ƙaƙabamun a matsayin ya'ya na"? Murmushi Omar yasaki kamar yana agabansa yace "Ae ko ɗazu da safe ta kira ni awaya, kusan kullum ne sai ta mun Complain akan ƴa'ƴan abusufyan ɗinta,' Abusufyan yace"Allah sarki, Nima tana kira na tana mun complain akan nasa ka mayar mata da ya'yana wuri ta, ynx ina yaran suke ne? Ya tambaya yana jiran amsa Omar yace "A gidan general ishaq suke da zama, can na kaisu," "Ina iyayen su suke ne"? Ko yan uwan matar ishaq din ne? Ya tambaya Omar yace "A'a Uncle yaran fa basu da kowa kamar yadda suka sanar mun, na haɗu dasu ne a asibiti cikin mawuyacin hali tagwaye ne baza su wuce 17years ba Suna buƙatar taimako, Ajiyar zuciya abusufyan yasaki kafin yace "Meyasa ba zaka dawo dasu nan ba cikin abuja kusa da kai ba"? "Uncle kaima ka sani, zaman su anan bazaiyi yu ba, maza ne mu duka duk ba wannan ba AMMI bazata ta6a lamuntar wani bare ya zauna acikin jinin ta ba,especially su da suka kasance basu da asali,' bayani yake masa tamkar yana agabansa ɗan gyaran murya abusufyan yayi kafin yace "Listenin to me OMAR! kana da kyakkyawar niyya akansu, inaso ka kaddara aranka cewa waɗannan yaran jinin ka ne, kasanya wa ranka cewa Ƴa'Ƴa na ne, ya'yan ƙanin mahaifin kane *ABUSUFYAN* ina so ka basu kulawa Omar ! Dan Allah kada ka bari su wulaƙanta kayi mun wannan alƙawarin....... Jikin Omar ne yayi mugun sanyi jin abun da Uncle Abusufyan ke faɗamasa, yanayin sautinsa da yadda yake yin kalamansa haƙiƙa ya ta6a Zuciyar Omar sosai, tunani omar yashiga yi aransa har sai da Abusufyan yace"Naji kayi shiru OMAR," Cikin sauri yace "Insha Allah Uncle i wll take care of them more than u think, nima inajin su araina sosai Uncle, ina ƙaunar yaran har cikin raina, yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar Abusufyan alamar hankalinsa ya kwanta kuma yasamu natsuwa da bayanin Omar, ABUSUFYAN yaci gaba da cewa "OMAR! INA SO KA DAWO DA YARAN NAN GIDA NA DAKE ANAN SU CI GABA DA RAYUWA, KA SANYA MUSU SECURITY TARE DA MAI AIKIN DA ZATA KULA DASU, INA SO SU RAYU ACIKIN GIDA NA, KAYI MUN WANNAN ALƘAWARIN!!!" runtse ido Omar ya ɗanyi yana jinjina kalaman Uncle din nasa daga bisa ni yace "Insha Allah Uncle zanyi komai kake so, zan dawo dasu nan acikin gidan ka kamar yarda kake so," Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama, ya ajiye wayar yana mai tunani iri-iri aransa, yana ji aransa in ya ɗauke su hosana daga gidan aunty babba tamkar baiyi mata adalci ba don ya Lura tana son yaran kuma sun saba dasu anya kuwa zai iya cika alƙawarin Uncle Abusufyan Na dawo dasu hosana cikin Abuja da zama!!? 😟 Yana cikin wannan tunanin Sehrish ta shigo da sallama, batare da ya ɗago ya kalle ta ba ya amsa mata sallamar, sam ransa ajagule yake uncle dinsa ya ɗan ruɗa masa brain ɗinsa Tray na a hannunta ƙarasawa tayi tare da gaishe shi "ina yini ya Omar," ƙiris ya rage omar ya ɗago ya kalle ta saboda Voice dinta tayi mashi kama da ta JAHAD, amma yabar Abun a matsayin muryar mai aikinsu ne ya koma masa ta Jahad Saboda kewarsu da yayi sosai Amsa mata yayi da cewa "Lafiya lou" Ajiye masa tray din tayi mai dauke da food stuffs dinsa asaman table Din dake a front dinsa sannan ta juya takama hanyar fita tana jiyo shi yana furta "ngde," Sauƙin kan MARSHAL OMAR yana matuƙar burgeta, babu ruwan shi ba kamar SGR ba, yana da IZZA ta wani bangaren kamar abinci muddin takai masa sai tayi saving ɗinshi, amma Omar sam baya buƙatar wannan kawai daga an kaimasa shi yake zuba abunshi yaci, Saukowa tayi down a lokacin har su Twins da kanal yusuf Sun hallara suna cin dinner dinsu, tayi mamakin ganin babu Abbansu da junaid may be yana a part dinsa azmee takai masu acan Gaishe su tayi gaba ɗaya suka ɗan dago suna kallonta, Kanal yusif ya amsa mata da sakin fuska amma Ayaan da jahan kuwa sai dai suka bita da ido,😡 Har bugun zuciya take ji in ta gansu cikin hanzari ta shige kitchen ta shirya ma SGR dinner ɗinsa ta fito ɗauke da tray ahannu ta nufi hanyar upstairs dinsa,

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47