Chapter 43
Chapter 43
rashin jin magana) Hannunta na ruƙe dana Sehrish suka tunkari benen da zai sadaka da Upstairs ɗin makarantar, anan Classes ɗin suke akwai kuma na down, sehrish dae sai bin ko'ina take da kallo makarantar ta haɗu kamar ba wurin ɗaukar karatu ba saboda tsaruwarta ga wuraren shaqatawa, shiga Class ɗin sukayi mutun goma ne a cikinsa a ƙa'ida kowane class mutun 12 ne kacal acikinsa maza 6 mata 6, idan aka haɗa da Sehrish da Amrish 12 kenan student ɗin cikin sa, gaba ɗaya Ido yadawo kan Sehrish kowa da irin kallon da yake yi mata, Mazan class din kuwa tuni sun soma sakin baki suna cewa "Wow so beautiful, so hot, She looks so sexy," Gabanta ne ya faɗi kowa da irin abunda yake cewa, Matan kuwa wani irin kallo suke binta dashi irin kallon hadarin kajin nan,' ƙara ƙanƙame school bag ɗinta tayi daga tsayen da take, Amrish ce ta soma magana" Hello Class we ave a new comer today, She's from awesome family, i hope zaku bata hankalin ku domin tayi mana Introducing kanta," ta ƙarasa maganar tare da kallon Sehrish tace "Pls introduce ur self," ɗan gyaran murya Sehrish tayi sannan ta soma cewa "am....Sehrish Salahuddeen Hussein by name, 17years old.... Alhamdulillah I love the Way i am," Wannan bayanin na sehrish yasa su gaba ɗayansu Clapping hands ɗinsu suna tafa mata, musamman ƙarshen maganarta ta ƙayatar dasu, Sun mata kyakkyawar tarba duk da akwai waɗanda tunda ta shigo ma basu ɗago da kansu ba daga saman desk sun kife shi kamar masu bacci, Kowane seat mutun ɗaya ne, Amrish ta sama ma Sehrish gurbi a Middle Roll na Class ɗin 0a Second seat Amrish kuma na'a First seat, sai da tafara neman alfarma wurin asalin mai seat ɗin na sehrish akan tabar mata, kuma cikin sa'a ta amince shine har tasamu gurbi abayanta, komai yazo mata cikin sauƙi kuma ba ƙaramin daɗi taji ba na haɗuwarta da AMRISH 💃 ******************AUNTY BABBA*********************** tun da sassafe suna kwance wayarta ta soma ringing a firgice ta farka jikinta na sanye da kayan bacci brown colour, leƙa fuskar Ishaq tayi taga koya buɗe ido samun shi tayi sai faman Sharar baccin sa yake, don haka a hankali ta lalla6a ta sauko daga saman gadon cikin sanɗa, Bayan ta sauko ta ɗauki wayarta data ajiye saman side drawer ɗin shi, sannan ta lalla6a ta shige cikin toilet ta duba mai kiran nata mutumin da tayi tsammani shi ta gani wato*BABA ALAMU* murmushi ta saki cikin sauri ta ɗaga kiran ta kara a kunnanta tun kafin tayi magana baba alamu yace "Na faso gari fa, tun jiya da daddare inata kiran layin ki baya shiga," Aunty babba tace "wlh bansan ka kira ba, dayake nabar wayar acikin ɗakina sai da asuba na ɗauko ta, tun jiya nima nake jiran kiran naka mutumina," Dariya baba Alamu yayi sannan yace "Ae ke baki sani ba, jiya muna dira gari na kwaso rugwagwar motata na shigo unguwarku don in sanar maki kawai sai naga waɗannan Masu fuskar shanayen tsaitsaye ruƙe da bindiga ae ba arziƙi naja motata na koma," Fashewa da dariya aunty babba tayi tace"Ae mijina ne yadawo jiya shiyasa kaga sojoji nan," Baba Alamu yace "Oh to ashe angon ne yadawo, yanzu dae ya za'ayi wurin fitar da yaran kinsan fa wlh shegen tsoran Soja nake, don kwanaki sun ta6a tarar mu a hanya suka sanya mu tsallen kwaɗi a tsakiyar titi da rana tsaka," Aunty babba tace "Ae basu da Imani, musamman in suka ji su acikin kakin nan sai su dunga ɗaukar kansu tamkar wasu dodonni, yanzu abunda za'ayi kana ina ne? Baba alamu yace "yanzu haka na fito da mota ta ina kan hanyar zuwa unguwarku amma fa bazan shigo ciki ba sai dai ki san yarda zakiyi a fito da yaran, Aunty babba tace "Shikenan ka jira ni, zaka ga kirana yanzun nan bada jimawa ba,". bayan ta kammala maganar ta kashe wayar sannan ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sanɗa ta lalla6a ta fuce daga ɗakin, Kai tsaye ta nufi ɗakin hafsat ta shiga, tsayawa tayi tana kallonsu hussana da jahad dake ta faman sharar bacci baje saman gadon hafsat, yayin da ita kuma hafsat ɗin ke kwance saman doguwar kujerar ɗakin tana bacci, da alama dukansu daga tashin asuba suka koma bacci, jinjina kanta tayi sannan ta ƙarasa dab da hafsat ta ɗansa hannu ta bubbuga ƙafarta, a dan firgice hafsat tafarka tana cewa "wanene," Murya ƙasa ƙasa aunty babba tace "ke ki taso inason magana dake," Bin ta da kallo hafsat tayi tana yamutsa fuska Alamar bacci bai ishe ta ba, daker tasa hannunta ta janye bargon data lullu6e rabin jikinta da tashi sannan ta miƙe tsaye tabi bayan aunty babba, suka fito daga ƙopar ɗakin suna fuskarta junansu hafsat tace "Meya faru mommy naga kin tashe ni ina tsaka da bacci na? Aunty babba tace "Mutumin fa wanda zai kai su hussana da jahad gidan marayu ya ƙaraso....," jin hakan yasa hafsat canza fuska tuni tace "Mommy yanzu dole sai kin raba ni da yaran nan? Wai me suka tsare maki ne? Dan Allah mommy kibarsu suyi rayuwarsu cikin salama, sun sha wahala fa baki tausayin su? tsoki Aunty babba ta buga tuni ta tamke fuska tace "Tausayin Uban me? menene alaƙata dasu? ke bana son zancen banza mun riga da mun gama magana dake don haka ! Ke nake so ki fidda yaran nan daga cikin gidan nan!! In yaso zan baki numbarsa in kin fitar dasu acikin motarki sai ki kira shi ki bashi su ya tafi dasu can Orphanage home ɗin," Murya asanyaye hafsat tace"shikenan mommy amma ina so ki sani haƙƙinsu ba zai ta6a barin mu ba! Sai Allah ya saka musu duk wani cin zalinsu da mu kayi,!!!!!!!!!!!!!!!! tana faɗin hakan ta juya tare da shigewa cikin ɗakin, wani irin matashin murmushi aunty babba tasa ki tare da cewa "Komai zaki ce ki ce, nidae in dae burina zai cika ba abunda bazan iya aikatawa ba ehen," acan ciki kuwa bayan hafsat ta shiga wuri tasamu gefen gadon ta zauna maimakon ta tashe su sai kawai tafashe da kuka mai cin rai Sautin kukanta ne ya farkar da jahad a firgice ta tashi zaune hankali atashe take cewa "Subhanallahi Aunty hafsat meya faru naga kina kuka? Meya same ki? jahad ta tambaya fuskarta cike da nuna alamun damuwa, Ci gaba da kukan hafsat tayi sam ta gaza cewa komai jikinta har wani jijjiga yake yi, jahad ta kuma cewa "dan Allah sister hafsat ki daina kuka, ban ta6a tunanin zanga wannan ranar ba, idan wani abu ke damunki, zan taya ki addu'a Allah ya yaye maki jin wannan maganar ta jahad yasa hafsat ƙara sautin kukan nata, ɗagowa tayi ta kalli jahad idanunta jawur suna fitar da zafafan hawaye tace"Jahad ba saboda kaina nake wannan kukan ba, face saboda ku ! Ina tausayinku, Nasaba daku zan iya cewa akanku nafara jin tausayin wani ɗan adam aduniyar nan !! tun da jahad taji hakan gabanta ya faɗi Rasssss !! Duk da hafsat bata fito fili ta faɗa mata kai tsaye abunda yasa ta kuka ba, miƙewa hafsat tayi tana faman sharar hawaye tace "Ki tashi hussana ku shirya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47