Chapter 33
Chapter 33
Daddy zai dawo in yaji wannan abun tabbas Nashiga Ukuna! Yunƙurawa tayi cikin sauri daga saman gadon jikinta na sanye da dogon wando baƙi sai ƴar Riga fara mai dogon hannu ajikin rigar an rubuta *I Love Paris* Hannu tasa ta ɗauki ribbom ɗinta da ke ajiye saman mirror, ta ɗaure sumar kanta dashi sannan ta fito cikin hanzari, a babban falon tasamu Jahad da hussana zaune saman 3 seater suna kallo a plasman dake facing ɗinsu, jin alamar tafiyar hafsat yasa su ɗagowa tare da haɗa baki wurin cewa "Barka da fitowa Aunty hafsat," daker ta iya yi masu murmushin yaƙe tace "Yawwa My Twins," sannan cikin sauri ta wuce upstairs direct izuwa bedroom ɗin aunty babba, tun kafin ta shiga ɗakin nata take faman kwala mata kira Mommy!mommy!!Mom!!" Aunty babba da fitowarta kenan daga bathroom waist dinta daure da farin towel tana faman tsane gashin kanta da karamin towel tace"daughter lafiya kike mun irin wannan kiran na tashin hankali !!!," Shiga ciki hafsat tayi tana cewa "Mommy akwai matsala wlh! Dakatawa da tsane gashin kanta tayi sannan ta juyo ta kalli hafsat tare da cewa "Matsala kuma ta me kenan"?Cikin tashin hankali hafsat tace "Mommy wannan matar data ban kuɗi don na zubar mata dasu hussana da jahad, wlh itace ta kira ni yanzu, ban ɗaga kiran ba shine ta turo mun saƙon cewa na biya ta kuɗinta ko kuma ta haɗa ni da hukuma!!Ta ƙarasa maganar tana jira taji mai Aunty babba zata ce, abun mamaki sai taga ta fashe da dariya mai sautin gaske....... Cikin ruɗu hafsat tace "Mommy na faɗa maki tashin hankalin da nake ciki maimakon ki tayani jimami amma sai naga kina dariya saboda me!? tsagaitawa da dariyar Aunty babba tayi sannan tace"Hafsat kenan to ni menene ruwa na aciki? Ki mayar mata da kuɗinta mana shine kwanciyar hankalin ki," Muryarta tamkar xatayi kuka tace "Amma mommy sarai kinsan cewa nariga da na ta6a kuɗin nan kusan dubu ɗari takwas nayi amfani dasu aciki, Bani da kuma hanyar da zan biya su shiyasa nazo wurin ki saboda nasan akwai kuɗinsu Jahad wanda yaya Omar ya bayar ayi masu hidima, Inaso ki bani su don na biyata kuɗinta," Turusss ! aunty babba tayi kafin tayi Uwar shewa tace "Ahayyeeeee ! Anzo wurin dana fi so !! tabbas don kuɗi akwaisu kuwa suna kwance cikin bank account ɗina suna bacci, Ko sisi wlh baxan baki ba !! Har ni zaki watsa ma ƙasa a ido saboda waɗancan tsintattun yaran da ke da kan ki kika ce zasu iya zama nakiyar da zata tarwatsa mun plan ɗina, amma sai gashi akan idona kike nuna masu soyayya don ki 6atamun rai Ko?, don haka kije kiji da matsalar ki ! Ni babu ruwana acikin lamarin ki!!! Ido cike taf da kwalla hafsat ke kallonta cikin tsananin 6acin rai da ƙuna har ta nufi hanyar fita daga ɗakin ta tsaya tare da juyowa ta kalle ta tace "Mommy naji duk abunda kika ce ! Nayi mamakin yarda kike tada jijiyoyin wuya akan kuɗin da bada gumin ki kika same su ba! Kuɗin nan Mallakin Su hussana ne! saboda su Omar yabada ayi masu hidima, ke kuma kika kwamashe su Saboda son zuciyarki, don haka muddin kika ce zaki hanani kuɗin nan, zan kira yaya Omar ne na tona maki asiri game da duk irin cin Zalin da kika yima Twins ɗinsa.............' dakatawa tayi da maganar tana faman haƙi, Aunty babba kuwa wani irin shu'umin murmushi tasaki kafin tace "and then So What Hafsat! Go ahead ki faɗa masa wlh ko ajiki na! Ni nasan yarda zan fidda kaina wlh, kece a ruwa bani ba, Ni dan Allah fuce mun daga ɗaki............ tayi maganar tare da nuna ma hafsat hanya alamar ta fuce mata daga ɗakinta, murmushin takaici kawai hafsat tasaki kafin tasa kai ta fuce daga ɗakin, cikin tsananin jin 6acin rai Fuuuuu ta wuce izuwa downstairs ta wuce bedroom ɗinta, wuri ta samu gefen gadonta ta zauna cikin tashin hankali tana cikin wannan tunanin message ya sake shigowa cikin wayarta data bari saman gadon,Hannu tasa ta ɗauki wayar tare da buɗe saƙon ta karanta kamar haka "ina tsammanin jin alert ɗin kuɗina, a yau ɗin nan in ba haka ba, nasamu labarin cewa yau general ishaq zai dawo wato Abbanki, kai tsaye zanzo har gidan ku, adai-adai lokacin dana tabbatar cewa ya iso gari zan shigo na tada maki 6alli" Shiru hafsat tayi gabanta na wani irin faɗuwa tuni idonta sun canza launi, bata da wata mafita daya wuce ta koma ma mommyn nata, ta lalla6a ta tasamu tabata kuɗin ta mayar ma jarababbiyar matar nan, ko sun rabu lafiya, Zumbur ta miƙe tashi ga yin sintiri acikin ɗakin nata cikin tsananin damuwa, Sallamar Jahad ce ta katse mata dogon tunanin da ta shiga, "Jahad har kun gama kallon"? ta tambaya yayin da take ƙaƙaro murmushi a fuskarta, Jahad tace "A'a aunty an fara kiran sallar la'asar ne shine nashigo nayi sallah," Hafsat tace"Allah sarki, na lura bakya wasa da sallah Jahad, da zarar lokacinta yayi komai kike saina ga kin dakatar dashi don yin ibadah,"Murmushi jahad tasaki tare da shige wa ciki tana cewa "aunty babu abunda yakai sallah muhimmanci acikin dukkan aiyuka, babu wani jin daɗi na duniya da zai sanya na manta da yin ibadata abisa lokacinta..........' Wayar Hafsat da tayi ringing ya hana jahad ƙarasa jawabin nata, cikin sauri hafsat taƙarasa ta ɗauki wayar tare da dubawa, ganin numbar matarnan ce tsanya ta, yin wurgi da wayar, hankali tashe ta fuce daga ɗakin......... Shiru jahad tayi cikin mamamki ganin yarda hafsat tayi wurgi da wayarta ga fuskarta da alamun damuwa hakan na nufin wani abu na damunta, "Ya Allah ka yaye ma aunty hafsat damuwar dake damunta, ka kawo mata mafita Alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W)," ta faɗi acikin ranta sannan tashige cikin toilet donyin alwala,kai tsaye Hafsat ta koma ɗakin Aunty babba, lokacin da ta shiga har ta kammala shirya kanta cikin atampha Embellished mai tsadar gaske da kyau, tana zaune saman stool agaban mirror tana shafa jan baki abakin ta, Hafsat ta shigo, wuri tasamu gefen gadonta tazauna tana kallonta,Juyowa Aunty babba tayi ta kallota tare da sakin Murmushi tace "My daughter, Look at my face how do i look? Kinsan yau Abban ki zai dawo, Shiyasa na taƙarƙare ina masa kwalliya, yau inajin kaina tamkar sabuwar amarya," Fuska a ɗaure hafsat tace"Kinyi kyau,"Aunty babba tace "Ae ko baki faɗa ba, nasan cewa ni kyakkyawa ce, tun da gashi nan ke ma albarkacin kyau na kin samu har kinyi ɗan haske da dogon hanci ga gashi har kina taƙama," Hafsat tace "hmmm mommy kenan, amma dai kinsan cewa Hanci na ba irin naki bane ko? kuma da kike maganar kyau kar ki manta Abbana fa kyakkyawa ne hausa fulani," Tsoki aunty babba tasa ki tana cewa "Menene wani hausa fulani, Jinin Larabawa ake magana, kowa yasan mu da kyau babu jinsin da suka kai mu kyau aduniya kaf," ɗan guntun murmushi hafsat tasaki kafin tace"Ae shi kyau mommy ba'a fuska yake ba, ko a Surar jiki, a zuciya yake!! Duk kyan mutun muddin zuciyarsa baƙa ce, to ya tashi abanza mummuna ne shi,'Jin abunda hafsat tace ne yasa ta ajiye jan bakin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47