Chapter 36
Chapter 36
abunda junaid yace yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa zaune daga saman gadon tana cewa "ngde da jin hakan junaid, naji ma anata kiran sallar magrib bari naje nayi alwala," junaid yace "to shikenan nima bari naje nayi salla,pls reesh karki ƙara sa damuwa irin haka, kuma in kin kammala sallar, ki fito muyi dinner atare," Murmushi ta sakar masa tare da cewa "Ok my lovely bro, da zarar nayi sallah zan fito nima," lumshe ido junaid yayi tare da buɗe su akanta fuskar nan ɗauke da Murmushi, sai da yaga sehrish tashiga toilet sannan yafuce hankalinsa a kwance..........................❤ remain 2 pages free su ƙare, wanda baiyi payment ba ya hanxarta Yi, Abban Sojoji 300 ne, discount da nayi na Abbban sojoji fans group ne kawai 200, Vip kuma 700, bank details ɗin da za'a tura,3196407426 First bank, Bature Hafsat Muhammd Evidence of payment 08103884440 [9/13, 11:08 AM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────EPISODE 23-24 ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️ *Mallakin Hafsat Bature Moh'd* ~BossBature~ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• Fitowa tayi tana faman yarfar da ruwan alwalar dake hannunta,hijab da sallaya ta ɗauka a wardrobe, ta shimfiɗasu tare da kabbara sallah,bayan ta kammala tabar darduman anan saboda in an kira isha'e, hijab ɗin ta cire tare da ajiye shi saman gadon sai ta ɗauki Mayafinta, ta yafa shi akanta, Fitowa tayi kai tsaye ta wuce dining, a lokacin junaid ma yana a wurin tare da Haroon sai kanal Yusif duk suna zaune, yayin da Azmee ke faman ɗawainiyar Zuba masu abinci, Ƙarasawa tayi tare da cewa "Sannu da aiki Aunty Azmee," Juyowa azmee tayi tare da kallonta tace"Yawwa mutuniyar sarkin kuka, Lamarinki naban mamaki kamar me iska," Sunnar da kai Sehrish tayi tana ɗan Murmushi kafin daga bisani ta gaishe da Kanal yusif da fara'arsa yace "Our Princess,duk yau ban saki a idona ba, Yakamata ace kina sakewa da ƴan uwanki sosai," Murmushi kawai Sehrish tayi tare da zama kusa da junaid suna facing ɗin kanal yusif da haroon ta hannun dama, Zuba mata abinci azmee ta soma yi a plate, junaid dake a gefenta yace"Da ace baki fito ba ko, da bazanci komai ba Allah," Kafin sehrish tace wani abu haroon yayi saurin cewa "Saboda ciki ɗaya kuka fito ko? murmushi junaid yayi tare da cewa "Yaya Haroon yadda na ɗauƙi Sehrish ta wuce haka a wurina," ta6e baki Haroon yayi yana kallonta, Harara Sehrish taɗan wurga masa tare da murguɗa masa baki, jinjina kansa yayi tare da cewa "An fa samu freedom of sitting the same table da Ƴa'ƴan masu gida dole ayi iya shege, Jin wannan maganar ta Haroon ta sanya junaid ɗaure fuska lokaci guda yace "Yaya haroon me kake nufi da hakan? Haroon yace "Abunda ranka yabaka" Dakatawa kanal yusif yayi daga cin abincin da yakeyi ya ɗan bubbuga plate ɗin dake gabansa da cokalin hannunsa ya bada sauti sannan ya aza idonsa akan na Haroon, Ganin irin kallon da kanal yusif ya jefa masa ne yasa shi, yin tsit ya shiga taitayinsa, Mayar da idonsa yayi kan Sehrish yace"Sister Yaushe ne zaki fara zuwa school ɗin? yayi hakan ne donya mantar da ita maganar haroon, ganin yarda tayi sanyi lokaci guda, daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa "Gobe ne insha Allah," Kanal yusif yace "Masha Allah,A matsayina na yayan ki, akwai wani jan hankali da nakeso nayi maki, kin ga gobe zaki fara zuwa, kuma zaki fara haɗuwa da sababbin ƙawaye iri-iri,akwai good friends waɗanda zasu dunga ƙarfafa maki guiwa akan karatu ta hanyar baki shawarwari masu kyau,bayan su kuma akwai bad friends gur6atattu waɗanda majority ɗinsu ba karatu ya kaisu ba,Asarar kuɗin iyayensu kawai suke yi, basa karatu ƴan abi yarima asha kiɗane,babban ma tashin hankalin yanzu majority na irin waɗannan ƙawayen ƴan Lesbian ne,fitsararru marasa kunya waɗanda suka gagari iyayensu da malamansu, burinsu kawai su 6ata tarbiyyar wasu, bana so ki kasance ɗaya daga cikin irin waɗannan ko kusa, dayawa wasu suna kuskuren yin abota da irin waɗannan bad friends ɗin, sai suce ae basu suke aikatawa ba,sun manta cewa zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai,to koda gigin wasa bana so ko fira ta haɗaki da irin waɗan gur6atattun balle harku ƙulla Abota, Ina gargaɗin ki akan hakan ! And i want u to know that Ke yanzu kina ɗaya daga cikin Mutuncin gidan nan!! Kuma kinsan yarda sunan family ɗinmu ya karaɗe ko'ina, ba inda ba'asan Jinin SALAHUDDEEN HUSSEIN ba, don haka yazama dole ki kiyaye mutuncin family ɗinmu da kuma ƙimarsa, ina fata kina fahimtar abunda nake cewa"? Ya tambaya yana kallon sehrish wadda ta natsu tana sauraronsa cikin sauri tace "Ina fahimtar duk wani abu da kace yaya yusif, kuma insha Allah zan kiyaye faruwar hakan,kuma naji daɗi sosai harma baxan iya misaltawa ba,saboda na samu ɗan uwa nagari wanda yake mun nasiha akan na tsira da mutunci,babu wanda ya tunasar dani akan hakan sai kai, kuma insha Allah bazan ta6a baku kunya ba, zan kasance ɗaya daga cikin abun Alfaharin gidan nan," taƙarasa maganar yayin da idonta suka ciko da kwalla, gaba ɗaya Azmee da Junaid sun kasa kunne suna sauraron maganar tasu, dukansu babu wanda baiji daɗin maganar Kanal yusif ba, Illa mutun ɗaya Wato Haroon wanda ke ta faman tur6une fuska yana faman hura hanci aransa yana cewa "Insha Allah ni kuma bazan taba barin ki ki xama abun alfaharin gidan nan ba, balle har ki samu matsayi acikinsa, saina san yarda zanyi in tarwatsa komai har inyi sanadiyar korarki acikin gidan nan," ya faɗi yana kallon sehrish rai a6ace yana faman tura dambun nama abakinsa har yana shaƙewa, Kanal yusif kuwa murmushi ya saki sannan yaci gaba da cewa "Allah ya yarda Sehrish,Nima inason ki zama Abun alfaharin mu gaba ɗaya," ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu ya ɗauki glass cup dake ɗauke da Lemu mai sanyi yakai bakinsa yana kur6a, ƙasa-ƙasa da murya junaid yayi tare da cewa "sehrish nima fa naso nayi maki nasiha akan zuwanki makaranta, amma kash sai gashi Yaya yousouf ya riga ni, amma duk da haka ban makara ba, don Allah sehrish karki canzamun koda kin fara zuwa school don nasan zaki ƙara wayewa sosai..........' Murmushi sehrish ta saki jin abunda junaid yace, kafin tace "Insha Allah junaid hakan baxata ta6a faruwa ba,mu aminnan juna ne zamu kasance atare ako wane hali na rayuwa, kaine abokin shawara na," ajiyar zuciya junaid ya saki aransa yana ƙara samun kwanciyar hankali jin bayanan da sehrish tayi masa, wayar haroon ce dake acikin aljihunsa ta soma ringing taken waƙar nan da ake cewa "ɗan duniya hayaƙin taba," jin ringing ɗin wayar yasa kanal yusif girgiza kai tare da cewa "Allah ya shirya ka," Haroon yace "Ameen don son Annabi," sannan yayi saurin tashi daga dining ɗin yakama hanyar fita daga falon yana zaro wayar daga aljihun wandonsa, ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnansa yana cewa "Shegen bisa ashe har ka isa hotel ɗin, ae ko gani nan zuwa Yanzun nan Allah yasa ka taho mana da harkar nan..........' ya yi maganar da dariya a fuskarsa kafin yasa kai ya fuce, Bayan sun kammala dinner ɗin junaid suka wuce masallaci tare da kanal yousouf jin ana kiran isha'e,. Itama
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47