Chapter 23
Chapter 23
ya dubo su, amma ya shirya zuwa gobe domin ya duba su, Yana gama wannan tunanin ya dawo Downstairs da sauri ya sauko a lokacin Sehrish harta gudu zuwa ɗakinta saboda ta tsorata, Abbansu na ganinsa yace "Omar wai lafiya meya faru ne? Naga duk ka rikice lokaci ɗaya ko don saboda wannan yarinyar ne da ka gani yanzu," Zama Omar yayi yana cewa "No ba haka bane Abba just there's something that confused me but am ok now," Ajiyar zuciya Azmee tasaki jin yace babu komai, ci gaba da yin breakfast ɗinsa yayi anatse but still his brain was confused, Zuwa wani lokaci kowa ya Kammala breakfast ɗinsa sai daga bisani Sehrish ta fito suka shiga gyara gidan ita da azmee, ______________________________________________Farkawa hosana tayi da wata irin matsananciyar yunwa don hada kukan ta dama ita bata da jumurin yunwa ko kaɗan, hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda hosana ke ta faman rusa kuka gashi sai faman lallashinta takeyi amma sam taƙi yin shiru sai ta runƙa cewa "baki ji yadda nake ji bane, babu komai acikina kamar zan mutu," runtse ido jahad tayi sam tarasa abunyi, yanke shawara tayi kawai tafita waje taga ko zata samo mata abinci, tun da taga akwai visitors dake zuwa wurin marasa lafiya wata'kil ko Allah ya haɗa ta dana gari su sam mata abinci taba Hosana, tashi tayi cikin sauri tana cewa "Hosana ki jira dan Allah ki daina kukan nan, yanzun nan zan dawo," shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, fita jahad tayi tana faman zarya a asibitin wurin nema musu abincin da zasu ci, taimako yayi ƙaranci a arayuwar nan domin kuwa duk wanda jahad ta tunkara da niyar ya taimaka musu sai suce suma bazai ishe su ba, ga abinci nan tana gani haje-haje agaban wasu sun baje suna ci amma tarasa wanda zai taimaka musu koda da rabin plate ɗaya ne, A ƙarshe da ta gaji da yawon neman taimakon abinci sai ta samu wuri abakin wata bishiya ta zuƙunna tare da kifa kanta tana faman shesshekar kuka, babban tashin hankalinta yarda zata tunkari hosana tace mata bata samo masu komai ba, 😥 tana cikin wannan zuƙunnan Motar hafsat tashigo asibitin da gudu tayi parking ɗinta a harabar ajiye motocinsu, fito wa tayi fess da ita tayi wanka ta canza kayan jikinta yanzu tsadaddiyar atampha ce riga da skirt ajikinta sun bi shape ɗin jikinta very tight, ta ɗaure kanta da ɗan kwalin sannan ta yafa veil a shoulder ɗinta, ƙarasawa tayi ta buɗe back seat ɗin Motar hannu takai ciki ta ɗauko kwando mai ɗauke da kayan abincin da tazo masu dashi, bayan ta rufe motar ta wuce ciki sam bata lura da Jahad ba, haka itama jahad bata ɗago ba balle taganta,. tana ƙokarin shiga cikin ɗakin da aka kwantar da hosana dr yafito suka ci karo, ganin ta yasa ya saki fara'a yana cewa" ke ce mai kula da wannan patient ɗin ko"? Hafsat tace "Yeah its me," Dr yace "yawwa tun dazu take faman kukan yunwa gashi naga ba kowa tare da ita, amma tun da kin zo yakamata ki kula da ita, sannan idan ta kammala cin abincin akwai magungunanta dana ajiye wanda za'a bata," hafsat ta amsa mashi da cewa "Shikenan dr ngde ssae," tana faɗin hakan ta wuce ciki shi kuma ya nufi cikin asibitin, Samun hosana tayi tayi kukan tayi mai isarta har ta gaji, tana zaune saman gadon ta kife kanta saman guiwowinta, jin muryar hafsat yasa ta ɗagowa cikin sauri, Ae tana ganinta ɗauke da food stuffs a basket nan take jikinta ya soma rawa kaf-kaf kamar kura taga nama, Da murmushi hafsat ta isa ta zauna gefen gadon kusa da Hosana tana cewa "Ya jikin naki"? Murya na rawa Hosana tace"da sauƙi sosai" ita burinta tafara zuba ma cikin ta abinci, Ajiye basket ɗin hafsat tayi ƙasa, sannan tasanya hannunta ta curo flask mai ɗauke da haɗaɗɗen ruwan tea ta ajiye sa, Cup ta curo guda biyu ne a haɗe, ɗaya ta ɗauka ta bude flask ɗin ta tsiyaya mata shi sannan ta zuzzuba mata madara da bornvita aciki har sai da yayi kauri, sannan ta miƙa ma hosana, kar6a tayi takai bakinta tana sha da hanzari har wani sauti maƙoshinta keyi kwat-kwat , kusan sau 3 tana shanye wa hafsat na ƙara mata, bayan ta kammala ta ciro kula mai ɗauke da Chips haɗi na musamman, ta zuba mata a plate, miƙa mata tayi tana cewa "ki ci a hankali saboda ciwon ki," hosana ta amsa da "toh" Turawa kawai take yi abaki kamar zata haɗa da plate ɗin duka, bayan tagama dashi hafsat ta zuba mata fruits a plate ta bata, shima tashiga sha kamar kamar me, "Ina Ƴar uwarki take ne ban ganta ba"? Hafsat ta tambaya yayin da take kallon hosana,. Hosana tace "tun ɗazu ta fita tace na daina kukan yunwa na jira ta, har yanzu bata dawo ba," Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Nasan bai wuci taje nema muku abunda zaku ci bane, May be tayi tunanin na tafi nabarku ne," suna cikin magana jahad ta turo ƙopar a galabaice take tafiya saboda tsabagen yunwa, ƙafafunta har harɗewa suke yi tana tafiya kamar wadda tasha Codine, shigowa tayi tana faɗin"hosana sai dai kiyi haƙuri wlh bansamu komai .........' ganin hafsat yasa ta dakatawa da maganar cikin mamaki take kallon su, hannu tasanya tana murza idonta don ta tabbatar wa kanta cewa ba mafarki take yi ba, sakin hannunta tayi tana ƙare masu kallo, Expecially hosana data gani sai faman cusa fruits takeyi abakinta wanda hafsat ta zuba mata, Wani irin farin ciki ne ya cika jahad har batasan lokacin da ta fashe da kuka ba Don tsabar murna, tashi hafsat tayi ta ruƙo hannunta tana cewa "Kukan ya isa haka, tun da gani na zo ko? Halan kinyi tunanin na gudu ne nabarku shiyasa kika fita nema muku abinci"? ta tambaya tana kallon jahad dake faman shesshekar kuka tace"Nayi tunanin kin tafi kin barmu ne shiyasa na fita, ashe zaki dawo,". ɗan murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Am so sorry nayi laifi ban sanar muku ba, da asuba na tafi gida, nayi sallah bacci ya kwashe ni without my knowing bayan na tashi ne kuma na wuce kitchen na shirya muku breakfast dana kammala shine nayi wanka na fito," bayani take yi jahad na kallonta tsananin mamaki ne yakamata ganin yadda lokaci guda Hafsat ta canza musu gaba ɗaya tamkar ba ita ba, tazama wata mutuniyar kirki lokaci guda ANYA? jan hannunta hafsat tayi ta zaunar da ita gefen hosana sannan tashiga saving ɗinta abincin tare da miƙa mata, sannan ta haɗa mata tea itama, bayan ta kammala ta samu wuri saman plastic chair ɗin dake facing gadon da suke tana kallonsu, A hankali Jahad ke kurbar tea ɗin tana ɗan kallonta, bakomai take jin tsoro ba fa ce kada ace Hafsat tasanya musu POISON acikin abincin da takawo su,tun da dama tasan sarai neman hanyar da zasu kawar dasu suke yi, kuma wannan ce hanya mafi sauƙi, yadda hafsat ɗin ke kallonta ido cikin Ido yasa Jahad ƙara jin wani irin Tsoro aranta nan take hannunta ya shiga yin kerma kaf!kaf!kaf! 😳😳😳 Wani shu'umin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47