Chapter 15
Chapter 15
ma kin sani Allah,saki ukun nan sun Wajaba Akan ki muddin Abba yaji abunda kika aikata, saboda wancan karan Ladi mai aikin mu da kika ma bugun mutuwa sai da ya aika ki maiduguri bayan marukan da kika sha awurinsa ina ga waɗan nan bayin Allahn da kika naƙasa har Su biyu, gasky mommy kin shiga Uku, ga kuma ƴa Omar zaizo ni addu'ata Allah yasa Abba kada ya sake ki yabarki kawai da hukuncin Omar na zuwa prison kowa ma ya huta..... Hankali tashe aunty babba tace"Hafsat prison fa kika ce? So kike akaini can kin gaji dani kenan"? Rai a6ace hafsat tace "dole nagaji dake mommy, duk ke kika ja mana wannan masifar da muke ciki muna zaman lafiyar mu,' ta faɗi a ƙuke hada buga tsoki kamar bada uwarta take magana ba, Jinjina kai aunty babba tayi batare da tace komai ba, adai dai time ɗin dr ya fito daga ɗakin da aka kwantar dasu hosana, jiki na rawa tabishi tana faɗin "dr ya jikin nata ta farfaɗo,"? dr yace "Alhamdulillah tafarka yanzu haka bacci take yi itama saboda allurar da nayi mata," ɗaga hannu tayi tana cewa "Alhamdulillah har naji ɗan sauki, amma dr babu yarda za'ae ciwon fuskarsu ya warke nan take? kumburin ya sa6e, ni dr kodai surgery za'ae musu ne acanza fuskar,' tayi maganar in serious matter tana kallon shi, Wani irin kallo dr ɗin ke yi mata yama rasa amsar da zai bata, wuce wa gaba yayi ya tunkari Office ɗinsa yana cewa "sam Bazaiyiyu ba gsky,ba muyin irin wannan aikin anan, kuma fuskarsu batayi komai ba da za'a canza musu Ba,da alama madam kema kina buƙatar Aduba ki,' sarai taji abunda dr ɗin yace amma bata ji zafin maganarsa ba, saboda bata cikin natsuwarta a yanzu, Yini su kayi cikin fargaba ba salla ba salati dama ba ita bace agabansu ba, an saba haɗa salloli ayisu a lokaci guda,Saboda duniya aka sa agaba Ba lahira ba, gajiya su kayi gaba ɗayansu da zaman asibitin ga uwar yunwa kamar suyi hauka, ga zullimi da fargabar zuwan Omar, ganin har Magrib tayi babu kiran Omar yasa suka fidda tsammani da zuwan shi, Ƙarshe basu jira dr yayi discharge ɗinsu ba, aunty babba ta ɗauko hosana dake kwance saman gado agalabaice ta sa6o ta a kafaɗarta ta fito da ita, sai cikin mota ta kwantar da ita, Jahad ma tashiga motar baiwar Allah ga zazza6i tana ji, gashi dr yace suna buƙatar jini su duka biyun amma babu yarda zasu yi, rayuwarsu a tagayyare sai yarda akayi dasu, Shiga motar hafsat tayi mazaunin driver aunty babba na gefenta suka ja motar suka bar asibitin, a time ɗin har dr ya biyo su da sauri sauri don ya dakatar dasu amma ina tuni har sun bar arean asibitin............. A tsiyace ta shiga da motar cikin gidan tayi parking ɗinta, tana fito wa ta wuce ciki saboda jirin da take ji na yunwa, fitowa itama aunty babba tayi sam bata tsaya taɗauki hosana ba ta shige ciki itama, Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba ganin sun tafi sunbar hosana kwance sai faman nishi take saki numfashinta na fita daker-daker, bata son yaya zatayi ba ta ɗauke ta saboda itama babu sauran ƙarfi ajikinta, fitowa tayi daga cikin motar tana faman zubda hawaye, Iya cuta dae an cuci rayuwarsu, Ganin yarinya tsaye abakin mota yasa wani soja ƙaraso wa yana faɗin "Lafiya dai ƴan mata meke faruwa ne," Cikin shessheƙar kuka jahad tace "ƴar uwata ce ciki kwance bata lafiya bansan yarda zan shiga da ita ciki ba," Sojan yace "Can I help"? Jahad tace masa "eh" saboda bata da wata mafita da ta wuce hakan, Buɗe motar yayi ya zura hannunsa ya sungumo hosana dake kwance magashiyyan ya ɗaurata a kafaɗarta ya shige da ita ciki jahad ta bi bayansa, A saman 3 seater ya kwantar da hosana, jahad tayi masa godiya sannan tasamu wuri daga ƙasa ta zuƙunna fuskarta na dai-dai saitin ta hosana, Hawayen fuskarta har ɗiɗɗiga suke yi a fuskar hosana, addu'o'i tashiga karantowa tana tofa mata,. Duk hosana na jinta tana so ta buɗe idonta amma ta kasa saboda kumburar da su kayi, tana so ta buɗe bakinta tayi ma Jahad magana amma tagaza saboda haƙoranta kansu sun raunata sosai don ba'a rasa mai girgiɗi acikinsu, ga la66anta da sukayi suntum sam bata iya motsa su, Cikin kuka jahad tace"Hosana na sani nasan akwai abunda kike son faɗa mun amma kin kasa, kada ki damu ina jin duk wani raɗaɗi da kike ji azuciyarki, inaji inama ace zan iya ɗauke maki zafin ciwon da kike ji da tuni nayi wlh.......taƙarasa mgnr tare da kifa kanta ajikin hosanna,sun jima a haka wulaƙance babu wanda ya leƙo su, sai daga bisa ni hafsat tafito har tayi wanka da alama ta canza kayan jikinta, doguwar riga ce tasanya har ƙasa, ta ɗaure gashin kanta, Binsu da kallo tayi gwanin ban tausayi ita kanta duk rashin imaninta yau ta tausaya ma twins ɗin,girgiza kai tayi tare da wuce wa ta nufi kitchen, Jim kaɗan sai gata ta fito hannunta ɗauke da tray mai girma, Tea set ne ɗauke asaman shi, sai French toast ɗin da ta hado masu dashi da sauran snacks, duk da tasan ma daker zasu iya ci Bedroom ɗinta ta shigar masu da shi ta ajiye Tray ɗin asaman table ɗin dake a dab da gadonta, Sannan ta fito ta nufe su jin takun tafiyar hafsat yasa jahad ɗagowa daga kwancen da take tana kallonta da rinannun idanuwanta da suka jigata, Hafsat batayi mata magana ba hannu kawai tasanya ta cicci6i hosana ta ɗaura a kafaɗarta sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinta tana cewa jahad "Ki biyo ni," Cikin sauri jahad ta tashi tabi su cikin ɗakin, kwantar da hosana tayi asaman shimfiɗeɗen gadonta, sannan ta juyo ta kalli jahad tace "Ga tea nan da snacks nasan kina jin yunwa ki ɗaure ki sha,' Girgiza kai jahad tayi tana cewa "Bazan iya cin komai ba, "Soboda me"? Hafsat ta tambaya tana kallonta, Jahad tace "Sabodo ƴar uwata, bata ci komai ba,idan naci ita kuma fa"? Shiru hafsat tayi jikinta yaɗanyi sanyi aranta har tana mamakin dama har yanzu akwai ƴan uwa masu ƙaunar junansu haka aduniya? Jinjina kai tayi kafin tace " kada ki damu, zan ƙara dubata yanzu insha Allah,zata ji sauƙi," Shiru kawai jahad tayi,amma fa ba zancen Cin abinci agare ta muddin hosana bata ji sauƙi taci ba itama, sai dae yunwa takashe ta, "Ave a seat," hafsat ta faɗi tana nuna mata saman gadonta, Jahad tace "Ina so nayi sallah tukunna," ta6e baki hafsat tayi tana cewa "okey ga toilet nan ki shiga," wuce wa Jahad tayi ta shige toilet ɗin tana rufe ƙopa tafashe da kuka mai cin rai tunaninta yanzu shine yarda zasu gudu daga gidan gaba ɗaya, don yanzu ta kwammace Su ƙare rayuwarsu a titi akan su faɗa hannun wani, tunda abun nasu ba sa'a kowa baisan taimakonsu don Allah batare daya cutar dasu ba,mutun huɗu kawai tasan suna da kyakkyawan niyya akansu, tsohuwa wadda Allah yayiwa rasu sai Goggon katsina da aunty saude da Yaya Omar ɗinsu..... hafsat na jiyo kukan jahad dake acikin toilet, jikinta duk ya ƙara mace wa, karo na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47