Chapter 44
Chapter 44
inaso zan fita daku," Jiki a mace jahad tace "Toh," cikin sauri hafsat ta fuce daga ɗakin, Jahad kuwa jikinta har kerma yakeyi saboda tsoran inda hafsat zata kaisu, daker tasamu hussana ta farka daga bacci sannan ta sanar da ita cewa ta tashi su shirya Sister hafsat zata fita dasu, Batare da sunyi wanka ba, tsaka tsami kawai su kayi acikin toilet sannan suka fito suka shirya, jahad ta zumbula doguwar riga Orange colour ta yafa mayafi launin fari akanta, ita kuma Hussana riga ce Square neck green colour, sai Skirt Ethnic maxi ta sanya ajikinta yana da dan faɗi ya bude da ƴar bazarsa, ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, Mayafi tasamu launin skirt ɗin black colour mai ɗigon fari² ajikinsa, tayi rolling ɗinsa tamkar yadda Jahad tayi, Kallon hussana kawai jahad keyi kallon tausayi don ita ranta yana bata cewa lokacin barinsu gidan ne yayi, yanzu kuma zasu fuskanci wata ƙaddarar !!! lokacin da suka fito daga ɗakin hannunsu ruƙe dana juna, Aunty babba na'a falon sai faman zagaye zagaye take yi, tana ganinsu ta nufo su cikin sauri gudun kada ishaq ya farka daga bacci ya fito yagansu, Tana ƙaraso wa inda suke tace "Ku biyo ni," sannan ta juya ta miƙi hanyar fita daga falon, bin bayanta su jahad su kayi gabansu na faɗuwa, suna fitowa daga falon a harabar gidan tuni hafsat ta fito da motarta, buɗe musu motar aunty babba tayi tana cewa "Maza ku shiga ciki, ku jira hafsat yanzu zata zo, Allah ya kiyaye hanya," ta faɗi tana faman tiƙar dariya sannan ta rufe musu motar, Kusan minti goma sha biyar suna zaune jigum cikin motar gaba ɗayansu babu mai magana duk jikinsu yayi mugun sanyi ganin yarda Aunty babba ke faman yi musu dariya, tun daga haka suka gane cewa ba lafiya," 😳😳😳 _wannan na jiya ne da banyi ba, da Anjima zan saki next page insha Allah kuma shine, Ga masu son cigaba da karanta Littafin Abban Sojoji su tuntu6e ni ta wannan numbar (08103884440) [9/16, 2:19 PM] 💋BOSS LADY💋: 💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋 The father Of Soldiers Story & Written by_*Boss Bature* page 27 Fitowa hafsat tayi hannunta janye da trolley ba komai bane aciki ba fa ce kayansu jahad, ɗayan hannun nata kuma na ruƙe da basket na breakfast dinsu data haɗo masu, 😥😥😥 Tana isowa ta buɗe boot ɗin motar ta saka trolley ɗin sannan ta rufe, duk aunty babba na tsaye ruƙe da qugu tana sakin murmushi, Bude back seat ɗin hafsat tayi inda su jahad ke zaune ta miƙa musu basket ɗin, hannu na kerma jahad ta kar6a, Sannan ta rufe musu murfin motar, har tasa hannu zata buɗe gaban motar ta shiga ta juyo ta kalli aunty babba idonta jawur tace "Baki bani numbar mutumin ba, wanda kika ce zai kaisu Orphanage home ɗin," cikin sauri aunty babba ta ɗago wayarta dake hannunta, tashiga contact numbar baba alamu ta lalubo, sannan ta shiga karanto ma hafsat ita kuma tana rubutawa a wayarta, bayan ta kammala sa numbar tashige cikin motar kafin ta rufo ƙopar ta aza idonta akan aunty babba tace "Ina fata kin ji daɗi mommy, yau hussana da jahad zasu bar miki gidanki, sai ki zuba ruwa a ƙasa kisha don murna," tana faɗin hakan ta datse motar tare dayi mata key, ta juya sitiyarin motar tayi baya² da ita sannan ta karya kwana ta juyar da ita direct ta nufi gate ɗin gidan ta fuce da motar aguje, Lumshe ido Aunty babba tayi afili tace "Alhamdulillah na kawar da wannan matsalar, yanzu abunda ya rage mun shine zuwa wurin boka domin gudanar da target ɗina na gaba," tana faɗin hakan ta nufi cikin gidan fuskarta washe yau ta rabu da alaƙaƙai, sai da ta ɗan yi nisa da motar ta fito bakin titi sannan ta dakatar da driving ɗin, wayarta ta ɗauko dake ajiye agefe, Lambar baba alamu ta danna ma kira, bayan ya ɗaga ta sanar dashi kwatancen inda motarta take, bayan ta katse kiran ta ambaci sunan Jahad da Hussana, atare suka amsa mata da "Na'am," juyo taɗanyi ta kallesu da idanunta waɗanda suka canza launi, cikin sanyin Murya tace"kun san inda za'a kai ku"? Har suna haɗa baki wurin cewa "A'a," Shiru taɗanyi kafin taci gaba da cewa "Gidan marayu !!!!!!!' Zaro ido su kayi gaba ɗayansu hankali atashe suna kallonta, hussana da tagaza jurewa tuni ta soma kuka tana cewa "Yaya Omar fa? dan Allah kar akaimu can ku bari yaya Omar yazo ya ɗauke mu mana, ni bana son mu rabu dashi," Murmushin takaici jahad ta saki tare da cewa "Aunty hafsat ba wai gidan marayun ke bama so ba, kawai ni so nake naji da sanin yaya Omar za'a kaimu can"? girgixa kai hafsat tayi tare da cewa "Jahad bada sanin shi ba, kuma nima ba da son raina ba na amince da hakan, amma ina so ku sani can shine zaifi muku zama cikin salama, saboda shi kan shi ya Omar ya manta daku tun da gashi ko kira a waya yadaina yi, babu tabbacin cewa ma yana ƙasar tunda dama banan yake zaune ba, don haka ku Cire tsammani da shi, kawai ku rungumi ƙaddara, kuyi haƙuri³," har kusan sau uku tana maimaita masu kalmar suyi haƙuri,. Hussana dae bata dakata da kukan da takeyi ba sai ma sautin da ta ƙara, jahad ta jinjina kai idonta acikin na hafsat tace "Shikenan Aunty hafsat, kada ki sa damuwa aranki, mu kan mu bamu ta6a tunanin zamu kawo wannan lokacin araye ba, amma gashi mun kawo da ran mu da lafiyar mu, wannan alama ce dake nuni da cewa Allah yana sane damu !!! Kuma shine zai kare mu aduk inda muka kasance a faɗin duniyar nan! mun gode sosai da kulawar da kika nuna mana," daga haka jahad tayi shiru idonta na zubar da hawaye hussana kawai take kallo wadda ke ta faman shessheƙar kuka, Jikin hafsat ya gama yin sanyi sam tagaza yin kwakkwaran motsi, suna cikin wannan Yanayin Motar baba Alamu ta ƙaraso dab da tasu, wata tsohuwar jeep ce ta ragwaggwa6e ta fita hayyacinta, kai wannan motar ko kyauta aka bani ita wlh na kwammace in ƙaraci yawona da ƙafafuwana saboda muninta, gaba ɗaya fa glass ɗin motar ya faffashe kana hangen cikin motar, babban abunda zai ɗaure maka kai shine yadda yakeyi wurin tayar da motar domin kuwa babu wurin zura mukulli atada mota, sai dae wasu wayoyi gasunan birjik su yake haɗawa sannan ya tashi motar, hankaɗa murfin motar yayi sannan ya fito, wani irin Matsolan mutun ne ramamme sai uban ƙasusuwa gashi baƙi wulik kana ganinsa kaga cikakken ɗan duniya, fuskarsa yana da wasu irin tsaguna waɗanda zasu tabbatar maka da cewa Magobiri ne, yadda kasan kwarya haka tsagunan fuskarsa suke, yana da kwalakwalan idanuwa kuma jawur dasu, ga wani irin fankacecan hanci harya so yafi ƙarfin fuskarshi, haƙoran bakinsa kuwa sunyi jawur dasu saboda Cin goro, a shekaru zai iya zarce shekara hamsin, jikinsa na sanye da wani tsohon yadi wanda yausha rabon da yaji dutsen guga tun 1960 😔 fitowa hafsat tayi ita kanta da ta ga mutumin sai da gabanta ya faɗi saboda muninsa, shi kuwa washe baki ya shiga yi yana cewa "Yarinya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47