Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

slow saboda zuciyarta dake tariyo mata abunda yafaru yanzun nan, kusan 3 times tana knocking sai daga bisa tajiyo muryar junaid yace "Come in," Ashe door ɗin a buɗe take, tana zura ƙafarta ciki karaf taci ido dashi gaban mirror daga shi sai short towel a waist ɗinsa sam baisan cewa sehrish bace, ta cikin mirror ya hangota, aikuwa cikin sauri yace "dakata !! Kada ki shigo! Ja baya," dariya sehrish tayi sannan taja da baya ta tsaya jikin ƙopar tana cewa "Junaid yaushe ka fara jin kunyata har haka"? daga cikin ɗakin tajiyo muryarsa yana cewa "tun ranar dana gane cewa ke maca ce.....,' Murmushi ta saki tana faman sauke ajiyar zuciya har time ɗin temperature ɗin jikinta yayi mugun zafi ba don komai ba sai don abunda yafaru da ita yanzun nan, "Come in Sehrish," junaid ya faɗi, Shiga ciki tayi a lokacin harya zura jallabiya ash colour ajikinsa yana gyara hannun rigar, wuri tasamu agefen gadonsa ta zauna tana cewa "Junaid dama wannan wayr tawa nake nema narasa inda na jefar da ita, shine nazo ka taimaka ka kiramin layin dake cikinta, may be in tayi ringing in gano ta, Murmushi junaid yasaki kafin yace "shikenan zan kira maki ita, amma under one condition? Ya faɗi ayayin da ya tsaya agabanta ya ruƙe qugu, sehrish tace "Menene sharaɗin? Junaid yace "Tun ran nan nake ta fama dake ki nunamin gyaran gashin ki kin ƙiya, to yau indai kina So na kira layin wayarki sai kin cire mun nagani" ya faɗi yana murguɗa mata baki, Yamutsa fuska tayi tare da cewa "look junaid yanzu ba lokacin wannan bane, am not in mood Just ka kiramun wayar,' ta faɗi tana tsuke baki, Bin shi tayi da kallo ganin ya ɗan ɗaure fuskar shi alamar baiji daɗi ba, Cikin lallashi tace "junaid are u angry with me? Am sorry pls ni bazan so naga king of smile ya koma king of Angry ba,' tayi maganar da ɗan zolaya, Ɗan sakin fuskarshi yayi sannan yace "its ok, go back to ur bedroom i wanna call u righ now," Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "yawwa mutumi na, Allah yabar mun kai," ta faɗi tare da miƙewa ta wuce bedroom ɗinta cikin sauri, Junaid kuwa acikin ransa yace "Ameen sehrish Allah yabarmun ke till the end of my life,' sannan yasa hannu ya ɗauki wayarsa dake ajiye saman mirror, contact yashi ga tare da lalubar nombar sehrish da yayi mata Saving da*FUTURE DREAM* sa'an nan ya danna mata kira, tunkan sehrish tashiga ɗakinta ta rinƙa jin ringing ɗin wayar da ƙarfin gaske, tura ƙopar ɗakin tayi ta shiga ciki tana bin inda sautin ke fitowa, ashe tana cikin bedside drawer ɗinta, duk wannan uwar wahalar da tasha, cikin hanzari ta janyo drawer chest ɗin gida na farko, sai ga wayar ajiye sabuwarta kusan 1 month kenan tana ajiye bata mutu ba, saboda ruƙon chargyn ta, ajiyar zuciya sehrish tasaki tana shasshafa screen ɗin wayar da hannunta, . .........................tuna da azmee dake jiranta yasanya ta fice da wayar cikin sauri ta isa ƙopar ɗakin azmee knocking tayi daga ciki taji azmee tace "in kin son bada wayar kika zo ba ki koma," wato har ta gane ce sehrish ce ta kwankwasa mata, Gyaran murya sehrish tayi tare da cewa "Tare da wayar nazo aunty azmee," Azmee tace "shigo ciki," Tura kopar sehrish tayi ta shiga, samun ta tayi kishingiɗe saman gadonta, ganin sehrish yasa ta tashi zaune tana cewa "yanzu naji magana," Murmushi sehrish tasaki tare da samun wuri gefen azmeen ta zauna sannan Ta miƙa mata wayar tace "Gata," Azmee ta kalli wayar tare da cewa "dama ba wani abu zanyi da ita ba, ke nake so ki runƙa amfani da ita akai-akai takasance tare dake, saboda daga yanzu duk wani mai buƙatar wani abu ke zai kira kai tsaye a waya yasanar miki," jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa da bayaninta, Sannan azmee taci gaba da cewa "nikam inaso na tambaye ki, shin kin ta6a yin makaranta ne before? ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta a wani irin yanayi kamar wani abu yaɗan sosa mata zuciya, shiru tayi na wani lokaci kafin tace "eh nayi primary bayan nan nafara secondry karatun duk ashiriri ce ƙarshe ma muna gab da zamu shiga ss3 nadaina zuwa gaba ɗaya......' ta ƙarasa maganar asanyaye Azmee tace "yanzu kina da burin ci gaba da karatun ne ko kuwa a'a? Ta tambaya tana kallonta, Sehrish tace "ina so mana sosai, ina so nayi Ilmi saboda wata rana nima nazama abun alfahari, kuma wannan burin mahaifiyarmu ne, tun lokacin da ta haife mu takance Sehrish zata zama Achitecture, Hosana kuma Doctor, Jahad kuma Nurse haƙiƙa inaso nacika mata wannan burin nata.......................' idonta ne suka cuko tab da kwalla sunnar da kanta tayi ƙasa tana kallon wayar dake hannunta, Cikin mamaki azmee ke kallonta ita kanta sehrish batasan me take cewa ba, ci gaba da magana tayi kawai tana cewa "Allah sarki a lokacin ni nafi kwarewa wurin yin zane, hosana ce mai ƙoƙari acikin mu amma yanzu bata da cikakken hankali tun lokacin da ta duro daga saman window mai tsayin gaske ..........ban......ban....... Kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da yazo mata nan take ta fashe da matsanancin kuka, Gaba ɗaya hankalin azmee ya tashi sam tarasa gane ma sambatun da sehrish ke yi, cikin ruɗu tace "sehrish wai meke faruwa ne? Su wanene waɗannan kike magana akansu ne? ƴan uwanki ne? ɗaga mata kai tayi alamar "Eh" jinjina kai azmee tayi tare da cewa "share hawayenki daina kuka ya isa haka, duk da bansan Labarin ki ba amma ina da tabbacin cewa wani mummunan abu yafaru acikinsa wanda ke yawan saki cikin damuwa, don haka zanso naji labarinki sehrish amma ba yanzu ba aduk lokacin da muka samu free time sosai zamu zauna ki bani shi tun daga farko har ƙarshensa,' "Insha allah aunty azmee na yarda dake sosai baxan 6oye maki komai ba," ta faɗi ayayin da take share hawayen ta, Bayan sun samu natsuwa su duka azmee taci gaba da cewa "Zaki fara zuwa school insha Allah....' Cikin mamaki sehrish ta ɗago ta kalle ta tare da cewa "Makaranta? Ni kuma? Aunty azmee taya za'a ɗauke ni a school bayan ko takardun kammala primary ɗin bani dasu na rasa su,' "Kada ki damu sehrish wannan ba wata damuwa bace, komai za'a iya yi maki shi insha Allah, kuɗi ne kawai ke magana, kuma ni zan tsaya maki harki samu don nasan muddin na tuntu6i koda kanal yusif ne da maganar zai iya sama maki hanya, bama shi ba junaid zai iya yi maki wannan hanyar cikin sauƙi ki fara daga ss1 daga baya kin zana Jsce in time ɗinta yayi,' Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish har tagaza rufe bakinta, aranta tana cewa nan bada jimawa ba nima zan fara zuwa makaranta kamar kowa ?Alhamdulillah 😇 Hannu azmee tasanya ta kar6i wayar hannun sehrish tana cewa "ina fata junaid ya nuna miki komai ko? "Eh harma ya tura mun wasu apps ɗin da zanyi amfani dasu," Azmee tace "okey, idan kina so kiyi amfani da data ko wurin yin browsing da sauransu just Wi-fi kawai zaki kunna, ' Jinjina kai sehrish tayi alamar

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47