Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

dake hannunta tace "Tashi ki fuce mun daga ɗakina ! Bansan ma uban me yakawo ki ba," Shiru hafsat tayi batare da ta motsa daga inda take ba, illa kawai ta zuba mata ido,"baxaki fuce mun daga ɗaki na ba"? ta faɗi fuska aɗaure, Sassauta murya hafsat tayi tare da cewa "Kiyi haƙuri mommy in na 6ata maki rai, zuciyata ce bata mun daɗi........' Aunty babba ta katse ta da cewa "don zuciyarki bata maki daɗi shine kika zo na wanke maki ita? Ko me? girgiza kai hafsat tayi tare da cewa "kusan hakane mommy, ni yanzu zuwa nayi ki taimaka mun na mayar ma matar nan kuɗinta, ta addabe ni da kira, narasa ya zanyi," Murmushi aunty babba tasaki tare da juyowa sosai tana fuskantar hafsat tace,"Na Amince zan baki kuɗin ki mayar mata, amma bisa wasu sharuɗɗa! In kin bi muzauna lafiya daga ni har ke!? jinjina kai hafsat tayi tace "ina sauraronki, wasu sharuɗɗa ne? aunty babba tace "Inaso ki amince da maganar Fitar da yaran nan daga cikin rayuwarmu !!!!!! ɗagowa hafsat tayi aɗan razane tana kallonta..............Murmushi Aunty babba ta saki kafin taci gaba da cewa "Abun da nake son ki fahimta hafsat, ko da mun bar Omar ya ɗauki yaran nan ya tafi dasu can gidansu, wlh baza su ta6a samun kwanciyar hankali ba, domin kuwa Ke kinsan wacece Ammi ta tsani mutumin da bai da asali ya ra6i jinin ta, koda Omar yakai su can wlh ba zasu tsira ba!domin kuwa Ammi na zuwa zatasa a Kore su daga gidan! don haka yakamata kiyi tunani akan hakan kwarama cikin ruwan sanyi mu rabu dasu Lafiya, Shiru Hafsat ta ɗanyi na wani lokaci kafin tace,"Yanzu mommy Idan na Amince, su kuma yaran Yaya rayuwarsu zata kasance?ina za akaisu? Ina tsoran Rayuwarsu ta salwanta ! Aunty babba tace "Hafsat don me zaki damu akan haka? ni in dai kin Amince zan sa akai yaran gidan marayu acan zasu samu kulawa, kuma dama can yafi dacewa dasu, in yaso sai mu runƙa zuwa muna kai musu Ziyara tare da tallafi koya kika ce? shiru hafsat tayi na wani lokacin sannan tace"Shikenan Mommy na yarda da hakan, Amma yaya Omar fa? In yazo yaya zamu ce mashi in ya tambayi twins ɗinsa? ɗan murmushi aunty babba ta saki ba ƙaramin daɗi taji ba jin yarda hafsat ta amince yanzu komai zai fi zuwa mata da sauƙi, taci gaba da cewa "Hafsat duk yarda zamuyi kada mu bari Abban ki yasan da yaran nan har izuwa gobe, Akwai wanda nayi ma magana zai zo gobe insha Allah, Shi zai kai su gidan marayun, Sannan maganar Omar tunda har yakai yanzu bai zo ba, inajin cewa tabbas akwai abunda ya tsaida shi wannan ba matsala bace kibar mun komai a hannuna ni nasan yarda zance mashi ya yarda.................. Jinjina kai hafsat tayi jikinta a matuƙar mace saboda sabon da tayi da Su hussana da jahad sam batason rabuwa dasu amma kuma babu yarda zatayi this is the Only solution !!! Ajiyar zuciya ta saki tare da kallon Mommyn nata tace "Shikenan Mommy, ni zan wuce ɗaki sai naji ki ............ Muryarta na rawa take magana cikin sauri ta ƴunƙura tare da miƙewa ta nufi hanyar fita ɗakin tana jin Muryar Aunty babba tana cewa "Yanzu zan tura maki da kuɗin ki mayar mata abunta, kar taja mana bala'e Hafsat bata ce komai ba saboda yanayin da ta shiga, cikin sauri ta fuce kai tsaye ta shiga bedroom ɗinta, Lokacin da ta shiga ta samu su hussana da jahad zaune saman darduma suna karatun Al'qur'ani da kansu, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya, cikin sauri ta faɗa toilet tare da rufo ƙopa tana faman shessheƙar kukan rabuwa dasu......................................... __________________SEHRISH__________ Sam bakin ta yaƙi rufuwa don Murya, tun ɗazu ta shimafiɗa uniform ɗinta saman gadonta tare da sandal ɗinta da kuma school bag ɗin duka, ta tasa su gaba sai kallonsu take yi,bakomai take tunani ba face yarda zata fara shiga school gobe Talata, irin wankan da zata ɗauka,tana daga zuƙunne saman gadon nata sae faman sakin murmushi takeyi, hannu tasa tare da shafa uniform ɗin data jera tana cewa "daga gani zasuyi mun kyau,oh ni reeshi yanzu zanyi new friends a makaranta, da na banza da na kirki, Allah dae ya haɗa ni dana gari, ba wanda zasu canza min tunani na ba, ina ƴar talaka dani," ta faɗi da ƴar dariya, Turo ƙopar Azmee tayi tare da shigowa tana cewa "Da alama yau sehrish kin manta da shiga kitchen ko? kin barni da aiki narasa dalilin dayasa kika zubama kayan makarantar nan naki ido,sai kace ba mallakin ki ba"? tayi maganar yayin da take ƙarasawa ciki, ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta fuskarta washe tace "Am sorry aunty azmee, Yanzun nan nake shirin fitowa wlh, na kammala salla ne shine nake ɗan ƙara binsu da kallo, girgiza kai Azmee ta ɗan yi kafin tace "maza ki tattara kayan nan, ki mayar dasu cikin wardrobe, Kizo maza mu kama aiki,' Sehrish ta amsa mata da Toh sannan ta miƙe cikin sauri ta sauko daga saman gadon, Tattara kayan Uniform ɗin tayi takai su cikin wardrobe, bayan ta kammala ta ɗauki mayafinta saman gadonta, tayarfa shi akanta dama riga da skirt ne ajikinta, Cikin sauri tabi bayan Azmee suka fuce izuwa kitchen, Cikin hanzari suka soma shirye shiryen fara girkin dare, suna cikin aiki Azmee nagaban gas tana tafasa nama, yayin da sehrish ke ta faman fere kayan lambu asaman Chopping board, Faɗowa junaid yayi cikin kitchen ɗin jikinsa na sanye da Kayan ball yellow sai faman zufa yake yi da alama shigowarsa kenan daga wurin ball, sam yagaza rufe bakinsa sai faman murmushi yake yi, "Wlh harka ban tsoro junaid, yarda ka faɗo suddenly,jibi jikin ka sai faman zufa kake yi," Sehrish ta faɗi tana nuna sa da wuƙar dake hannunta, Juyowa azmee tayi tana kallonsa batare da tace komai ba, "Zuwa nayi in tunasar maki cewa, gobe ni zan kai ki school da mota ta," ya faɗi yana faman sauke ajiyar zuciya,. Sai lokacin azmee tace "Salon wahalar da kai junaid, ka bari tahau school Bus mana,ƙwara tasa ba da bin motar makaranta tun yanzu, amma in kace zaka runƙa kai ta ɗawainiyar zatayi yawa, kuma kasan sarai Babban yayan ku baya so kana fita ko?.ta faɗi tana kallonsa,. turo baki junaid yayi tare da ɗan buga ƙafarsa yace "Nidai Aunty azmee zan kaita, just for tomorrow cos this is the first time da zata fara zuwa school ɗin yakamata tasan wasu abubuwan inaso zan nuna mata ne, tun da ni nasan school ɗin sosai...." gaba ɗaya kallon shi suke yi yarda yake magana cikin shagwa6a, yana faman bubbuga ƙafa Dariya azmee tayi don ta Lura rigimarsa ce ta tashi, dama aduk lokacin daya buga ball sosai yagaji alokacin rigimarsa tafi tashi, Sehrish tace "Shikenan junaid gobe kai zaka kaini school, amma yanzu kana buƙatar yin wanka ka ɗan huta,," ɗan murmushi yayi jin abunda tace "Amma ina jin yunwa fa sosai," ya faɗi yana kallonta "Shikenan kada kadamu yanzun nan zan kawo maka abinci," "Yawwa My lovely sis," ya faɗi tare da kama hanya ya wuce upstairs room ɗinsa, A tray ta shirya masa coffee tare da snacks, sannan

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47