Chapter 9
Chapter 9
sosa kanta jikin ta sai tsuma! Yake,, aikuwa yaran da suke gurin suka rud'u da fad'in *"Kama b'arawo suburbud'e shi sa shi a mota Oga Singam!!!!!!* babarsu Alawiyya ta dunga dariya tana fad'in "Ladidi sai dai idan baki zo guri ba, ubangiji Allah ya tayar miki da wannan k'uruciyar iya haka". *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/26, 11:14 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿8* Sai wajan magariba sannan film din ya k'are, suka futo daga d'akin huuuuuuuu! Sun rud'e da fad'in *"Kama b'arawo suburbud'eshi sa shi a mota Oga Singam!!!!"* Ladidi ce shugabar su, in ta fad'a su fad'a,, haka kowa ya nufi gidan su yana wannan wak'ar da Ladidi ta k'irk'ira gurin kallo, da wak'ar a bakin ta ta shiga gida,, Mai koko ta bita da kallo cikin mamaki tace"Babu sallama sai wak'a Ladidi"! Dariya ta fashe da ita ,tace"Iya kin same"? Mai koko ta girgiza kai cikin mamaki,, "Wallahi wani film muka kalla gidan su Alawiyya me mugun kyau!! Gaskiya afton d'ab bala'i ne, uhmmm! Kin ga yanda yake suburbud'an " yan iska kuwa!? Ta k'yalkyale da dariya tana Sosa kanta ta cigaba da cewa"Iya nake fad'a miki har wani take ake masa,, saboda tsabar jarumta,, na tambayi Iliya ya sunan afton yace bai sani ba,shine na tsara masa wannan wak'ar. *Kama b'arawo suburbud'e shi sa shi a mota Oga Singam!!!"""* ta k'arashe wak'ar tana wata mahaukaciyar dariya, tamkar wata shashasha, Dariya Mai koko tasa tace"Aikam wak'ar tayi dad'i Ladidiya ta Mai koko,, ke dai kina son kallon hindiya" Ladidi ta dunga dariya taji dadin yabon da Mai koko tayi mata tace"Shiyasa ai nake so Kawu ya siya mana kayan kallo wallahi" Iya tace"Ke kin san bazai siya, nice zan siya miki amma sai kin nutsu kin daina shashanci da rashin ji gami da fada da maza" da gudu taje ta rungume ta tana Fad'in"Iya na daina insha Allahu, yaushe zaki siya mana" tace"Ki bari in d'auki a dashi na, zan siya miki amma fa sai naga kin nutsu". Ladidi tayi ta murna Iya tace"Kije ki yi alwala kiyi sallah, sai ki zo kici abunci" ta mike da saurinta sai farin ciki take Mai koko zata siya mata kayan kallo ******* Zaune yake a cikin wani had'addan bedroom kana ganin tsarin shi kasan na hotel ne, wanda ya had'a abubuwan more rayuwa da jin dad'i kai daga nin tsarin hotel din kasan ba na k'ananun mutane ba, ko a american ma sai wane da wane,, waya ce a hannusa, magana suke da Dady d'insa Yace"Dady ina tafe a wannan satin insha Allahu" daga d'ayan b'angaran G.Abbas yace"Wace rana zaka zo kason ina son zuwa in duba gidan gona ta a Kano ko" Dariya Hakeem yasa yace"Dady har ka samu guri ka fara aiki bani da labari" ?Dady yace"Sai kazo zaka gani, guri mai kyau can wani k'auye ne,, k'aramar hukumar Ungwago,, gonaki hud'u na had'a a gurin, babu abunda ban dasa ba,, ga gurin kiwo da gurin hutawa, gurin ya tsaru sosai" "Kai Dady har ka kwad'atamin son zuwa wallahi, insha Allahu mun gama komai anan, sun bamu izanin tafiya, inan tafe ranar Monday" Dady yace"Sai ka zo,, ai tuni su Salim suka je suka ga guri" b'ata fuska yayi yace"Dady kayi min laifi" Dariya yasa, Hakkim ya cigaba da cewa"Nine ya kamata na fara zuwa na gani na sa albarka" Dady yace"Kai dasu duk d'aya ne, kasan don baka gari ne". "Na sani Dady ai in nazo can zan gudu inje in huta" Dady yace"Zakaji dadin hutawa kuwa domin gurin yayi". Hakkim yayi ta sa Albarka Dady yana amsawa da amin, sukayi sallama cikin so da kaunar juna Wanda Allah ya kimsa tsakanin iyaye da "yayansu. ****** D'alha ne ya shigo gida a gajiye,, Iya da Ladidi na zaune tsakar gida kan wata tabarma Duk ta zare ta zama saura, kibiya ce a hannun Iya tana tsefewa Ladidi kai sai mita take kan kwarkwatar dake kanta wacce tak'i jin magani Babban abun takaicin ma shine duk rabin kan ya cire wani guri da gashi wani guri babu,, ga uban amo sani da k'wan kwarkwata abun k'yank'yami,, tace"Wannan kan naki gwara kawai a aske shi kowa ya huta, ni kam ban tab'a ganin kwarkwata me naci ba,kamar taki" Zumb'ura baki tayi tana k'okarin fuzge kanta tana fad'in"Ita bata yarda ba aske mata kai,, cikin wannan halin D'alha ya same su,, ya zauna gefen Iya yana mai da nuffashi,, Iya tace"Sannu da alama ka shawo rana, Allah yasa nagama abunci" Girgiza kai kurum yake, yace"Wallahi kuwa, Iya talaka shine babban abun tausayi a duniyar nan,, raza zafi haka zaka futa nema wataran ma ka futa baka samo ba" tace"Sai hakuri ai, Allah dai ya bamu rabo me amfani" Ameen yace" mik'ewa tayi tana fad'in"Bari in kawo maka ruwa da abunci""" Kallon Ladidi yake cike da takaici yace"Don ubanki babu sannu da zuwa ko, kin iya zuwa ki karb'i kud'in makatanta babu fashi""" Hannunta ta d'ora kanta ta soso ta soso ta ciro kwarkwarta har guda biyu ta ajiye kasa ta sanya farce ta kashe, abunta,, yace"Ba magana nake miki ba"" kallonsa tayi babu tsoro tace"Kawu Sannu da zuwa " Tsaki yaja yana fad'in"Kazamiyar banza kawai" Iya ta zauna tana aje masa langa, me d'auke da Dambu na tsaki yaji gyad'a da alayyawu tace" Kayi mata addu'a mana k'uruciya ce" Kofin ruwa ya d'auka ya kai bakinsa sai da ya sha sosai ya aje yace"Iya nagaji da ganin wannan k'azantar ta kwarkwata, yanzu ina futa zan siyo reza ayi mata k'wal kwabo idan kwarkwartar taga babu gashi, tayi nata guri". Tace"Wallahi nima shawarar da na yanke kenan" Ladidi ta mike da gudu ta shiga d'aki tana rusa kuka,, D'alha yace"Kyayi kya gama askin shine mafuta... Ya cigaba da cin abuncin sa. Sai da ya cinye Tass yayi hamdala ga Allah, mik'ewa yayi ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna yana fad'in "Iya kin San wani abu kuwa" ? "A'a sai ka fad'a" yace"Yanzu da zan dawo dake ta sabon titi na biyo. Wallahi gonarmu da ta Jatau da ta Malam Manu me mutuwa, wani me kud'i ya siya ya had'a guri guda ana ta aiki a gurin sosai gurin yayi kyau , yanda naji masu aikin gurin suna fada wai gidan gona za'ayi mishi gorin hutawa da gurin kiwo gurin noman kayan marmari, kin San b'angaran Manu biyu ne akwai gurin da yake noma kayan marmari goba d'ata Lemo da sauransu,, to naga an kewaye gurin da wani k'arfe za'a cigaba da aiki ,nace"Allah ya huttashe dani na shiga in dunga sarowa cikin sauk'i". Iya tace"Alhamdulilahi, aikuwa ka huta wallahi"'" ammafa ni lamarin masu kud'in nan na bani mamaki, haka kurum saboda kudi na cizon su sai su k'irk'iri abunda bai dace ba, a maimakon su raba kud'in ga mabuk'ata" *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/27, 10:30 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39