Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
Download Book

yace." Babu laifi samari." D'alha ya shiga gida cikin sauri. Gogon ku na tsaye jikin mota ya harde hannuwansa a k'irji jira kawai su shiga gidan ya kara yin ido hudu da marakaunyar yarinyar nan yaga tayi ladaf ko kuwa. Minti biyar D'alha yayi ya dawo da sauri yace." Bisimillah Alhaji ku shigo daga ciki." Bayan sa suka bi. Yaran unguwar dake tsaye na kallonsu suka biyo su yuuuuuuu! D'alha ya buga musu tsawa, suka koma gefe,wasu na cewa Ladidi ce taje ta jawo futuna. Mai koko na zaune gefan tabarma ta lullub'e jikinta da mayafi. Sukayi sallama suka shiga gurin zama ta nuna musu tana musu Barka da zuwa cike da mamakinsu Suka zauna babu kyankyamin komai domin gidan tsaf yake tun safe tayi shara da wanke wanke ko ina tas iskar Safiya na kadawa Gaisawa suke cike da mutumchi, General yace." Ina fata nan ne gidan su wata yarinya Ladidi." Mai koko tace." K'warai kuwa nan Alhaji ina fatan ba wani abun tayi muku ba." Cike fa tausayi yake kallonta yace." Mine dai mukayi mata laif............ Kafin ya gama maganar shi Ladidi ta bayyana a gurin, ta tsaya tsakinyar ta barmar idonta kan Hakkim! suka kurawa juna ido. Ihu!!! Ta kurma tana nuna shi da hannunta tace." Iya!!! Gashinan shine ya dinga dukana kamar zai kashe ni wallahi Iya shine, Allah ya kawo shi gidanmu mu dauki fansa domin bazan barshi ba." *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿23* Cike da mamaki General yake kallon Ladidi. dake tsaye Kansu D'alha mata tsawa ta matsa daka kan mutane amma kamar kara ingizata ake tanayi kamar zata kaiwa Hakkim duka. General ya kalli Yusuf da alamun tambaya. Yusuf yace." Itace yarinyar Dady." Sosai General yayi mamakin kankantar ta ya kalli Hakkim cike da takaici yace." Meye abun duka jikin wannan k'aramar yarinyar."? Sunkuyar da kansa kasa yayi. Yana jin tsoron kar dady ya tsinkashi a gaban mutane. Ladidi ta ruga kicin da gudu! Duk suka bita da kallo. D'alha kamar yasan abunda zatayi ya mike da sauri zai bita.sai gata ta futo hannunta rike da doguwar muciyar da Iya take dama koko tayi kan Hakkim da gudu. Hakkim yasan gurinsa ta nufo sai ya shirya tsaff ta d'aga muciyar da k'arfi zata maka masa.ya rike ta da sauri yw fuzgota sai gata ta fad'o jikinsa,cike da mugunta ya wurgar da ita gurin kanta ya bugu da bango ihu!! Ta kurma tana fadin." Wayyo kaina."!! D'alha yazo ya daga ta cike da jin haushi ya kwarfa mata mari yana fad'in." Ashe rashin lafiyar naki na k'arya ne." General yace." Yi mata a hankali samari." D'alha yace."Alhaji baka San halin yarinyar nan ba ne." General yace." Koma meye dai ni ta burge ni tunda take k'okarin k'watar 'yan cinta ga Wanda ya cuce ta, saboda rashin imani kamar Hakkim da shekarunsa da komai ya zage k'arfin shi kan yarinya k'arama kamar wannan." Mai koko tace." Alhaji bamu game me kake nufi ba."? General yace." Wannan da yake zaune shine ya sumar muku da ita jiya nine kuma mahaifinsa Nazo domin in nemi afuwar Ku." Iya ta mike tsaye da sauri ta gyara d'aurin zaninta tace." Ko dana ji ahwo!!! Shiyasa naga yana sinne kai tamkar b'arawo a hannun mata,wato dama kaine kake k'okarin kurman tamin da jikita. ? Babu shakka Ladidi ta kurmance sai munyi sha'ra'a dakai." Wani mugun haushin Matar yaji a zuciyarsa yace." Da zata kurman ce ma ai da kowa ya huta da alak'ak'ai." Ladidi ta taso da sauri tana rike Iya tana kuka take fad'in." Iya kar ki barshi nima bazan barshi ba." General yace." Innalillahi wa'inna ilahi rajinu. Ashe abun yayi tsanani haka,shiyasa zuciya ta kasa amunta nace dole sai Nazo naga halin da take ciki. Tabbas dole ki dauki hukunci Iya amma ki zauna muyi mgn dake ta fahimta. " Mai koko ta koma ta zauna tana maida nuffashi Ladidi ta jawo jikinta ta rungume ta tana rarrashin ta. Haushi duk ya tuk'e D'alha ya kalli General a nutse yace." Alhaji ka kwantar da hankalin ka don Allah ni nasan duk abunda ya faru da dalili haka kurum shi bazai kamata ya doke ta ba." General yace." Haka kake gani samari inace gashinan a gabanka ya wurgar da ita da mugunta ta buga kanta a hango ko baka gani bane."? D'alha yace." Nagaji Alhaji ai kana ganin abunda tayi masa ko."? Shiru General yayi yana girgiza kansa. D'alha ya bugawa ladidi tsawa tare da fad'in" yimana shiru shashasha kawai kin bude baki kina kukan banza da wofi." Iya tace." K'yaleta tayi kukan ta to kaji."!!!!. General yace."ina me bawa zuciyoyin Ku hakuri sosai domin narasa dame zan fara a halin yanzu amma kafin wani hukunci ya biyo baya ina rokon Ku da muje mu kai yarinyar nan asibiti a duba ta, domin hankalina ya tashi da jin maganar da kikayi." D'alha yace." Dama yanzu zamu tafi asibitin cikin gari." Mik'ewa General yayi yace." Maza Ku futo muje Allah ya kiyaye gaba." Mai koko ta zura mata hijabinta tana goge mata fuska suka futa To gurin shiga motar ma Ladidi ki tayi ta dinga turjewa wai bata yarda ba gurin yankan kai za'a kaisu a siyar musu da kai. Da k'yar Dady ya rarrashe ta ta shiga motar. Hakkim kamar ya Dora hannu aka Dan takaicin ta. *Comment vote and share* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿24* Cikin gari suka futa General yace." Zamu samu pravite hospital anan kurkusa sai mu tsaya kawai ba sai mun je babban asibiti na Murtala ba." D'alha yace." Za'a samu Alhaji." Yace." Sai mu tsaya anan kawai a duba ta." Cikin birget suka samu hospital.Hakkim ya kashe mota duk suka futo suka shiga ciki. Idan da kud'in ka babu wahala da kaskantar da kai da zakayi,D'alha yayi mamakin yanda ma'aikatan asubitin suke karrama Alhaji sai rawar jiki suke.nan ka yanki kati likita na ofis General yace." Da Ladidi tazo su shiga tare. Mak'ale kafad'a tayi tana b'uya bayan Mai koko, murmushi yayi yace." Zo

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39