Skip to content

Chapter 36

Chapter 36

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

wayarku babu Wanda ya kirani yaji ya na sauka lafiya." Hjy Asiya tayi 'yar dariya tare da fad'in"Nasan kana cikin koshin lafiya my son, duk laifin ka ne, kaje ka sumar da yarinyar mutane ka gudu yanzu inda bata dawo nutsuwar ta ba me zaka ce umm? Don Allah ka rage zafin zuciya myson." Yace." Momy daga taimako sai ace na sumar da ita, ni wallahi da zaku bi tawa da Ku mai da yarinyar nan domin Zata jawo muku masifa." Hjy ta kalli gen dake kallon TV tana jin tsoron kar yaji abunda hakkim din yake cewa, da sauri ta katseshi ta hanyar fadin"Kai ka fiye Abu myson babu wani Abu insha Allah." Yace." Shikkenan tom ni dai babu ruwana inanan." Dariya Momy tayi tana tambayar sa aikinsa yace." Alhmdullahi Momy komai ya kammala muna aiki har sun bamu gurin zama. " Momy tace"Tom Allah ya taimaka yayi jagora ." yace." Dady ne."? Gashinan zaune." Yace." Yawwa bashi wayar mu gaisa. " general ta mik'awa wayar ya karba a nutse suka gaisa dashi ya tambaye shi aiki kamar yanda Momyn shi ta tambaye nan yayi masa fatan alkairi sannan suka yi sallama. **** *K'auyan d'an kunkuru* Tunda Ladidi tq bar K'auyan Dan kunkuru hankulan jama'ar garin ya kwanta kowa ya sake yana rayuwar su nan suka k'ara tabbatar wa da cewar Ladidi annoba Ce a garin, wasu kuwa fad'i suke ai Mai koko ta tura Ladidi birni domin tayi iskanci ne wasu kuwa saboda jahilci cewa suke yi ai Mai koko da D'alha sun siyar da Ladidi saboda su hutawa da masifa kowa da abunda yake cewa. D'alha ya samu aiki a cikin birni sai ya daina sana'ar sai da d'ata da gobe yana zuwa cikin gari yayi sati d'aya biyu uku ya dawo gida, Mai koko kuwa har yanzu tanan tana sana'ar kokon ta, tayi kewar Ladidi ta gaji wani lokacin in ta tuna da ita har hawaye take yi tana tunanin ko a wane hali take ciki oho, gashi D'alha baya zama amma tayi alk'awarin wannan dawowar in yayi dole zata turasashi ya kai ta inda Ladidi take ta ganta. **** Yau watan Ladidi biyar a abuja za kuso kiga yanda ta sanja tayi wata kiba mai ban sha'awa farar fatar ta ta murje, duk wannan ramar babu ita sumar kanta ta futo sosai domin har tafi ta da, sai dai ko da wasa bata bari a tab'a mata kanta da sunan kitso duk ranar da akayi tsautsayin tab'a kan kuwa aljanunta sai sun buge ta yini suke yi Abu d'aya dole sai an kira malamin dake tsaye a kanta yazo yayi mata addu'oi sannan suke gusawa ta kwana tana bacci sai don kanta ta tashi. [11/28, 9:34 AM] BintuUmarAbbale Shiyasa suke taka tsantsan da abunda zai bata mata rai indai tace bata son Abu to Dady zaiyi ta fada kar ayi mata shi, lokacin general ya sanya Yusuf dake gari ya nemo mata makaranta mai tsada akayi komai da komai general da kanshi yake kai ta ya dauko ta duk da cewa akawai direbobin sa kusan uku, shi dai bukatar sa Aminatu ta samu nutsuwa, cikin ikon Allah da taimakon Liman Ladidi ta samu ta nutsu ta daina shirme da shiririta yanzu kallo ma bai dame ta ba kullum in ta dawo daga makaranta suna tare sa Salima tana nuna mata abunda bata gane ba. Yusuf dake shirin kai kud'in aure yaji duk duniya babu yarinyar da yake so kamar Ladidi yana mamakin asitaccan kyawun ta don a k'auye ta ke ne shiyasa komai ya b'uya, sai ya zamana bashi da gidan zuwa sai gidan su Hakkim yana fakewa da cewa yazo gaishe da General ne, nan kuwa Ladidi yake karewa kallo dukaninsu basu gane ba, lokacin suka yi wata irin sha kuwa da Ladidi itama in bata ganshi ba ta dinga cigiyar sa kenan..... Yusuf ba kullum suke waya da Hakkim sai jefi-jefi domin wani lokacin shi hakkim din bashi da time kullum suna aiki yafi samun sakewa Duk weak end sai su sha hirarsu a waya yayi ta tsokanar sa cewar ina bagidajiyar budurwar sa, shi kam Yusuf dariya yake yana fadin "Na wuce babinta yanzu na sanja wata zukekiya zan turo maka hotonta ma ka gani." Hakkim mamaki yake sosai yace."Yanzu duk irin son da kake wa Naja'atu ka daina kalli ka cika mayaudari." Yusuf dariya yayi yace." Na samu wata wacce ta fita komai da komai akan me bazan rabu da ita ba." Tsiya Hakkim yake masa yace ." ka turo min inga hoton yarinyar da ta rusa gwamantin Hafsa a zuciyar ka." Yusuf Yace. " zan turo maka amma ba yanzu ba." Haka suka yi sallama cike da barkwanci da kaunar juna. *28/11/2019* *BINTA U ABBALE* *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *πŸ…Ώ41* A takaice dai sai da Hakkim yayi shekara guda sannan ya dauki Hutu ya fara shirye-shiryen zuwa gida Lokacin ya kara wani kyau da waye wa.... Ya fara soyayya da wata Aboki yar aikinsa 'yar Ghana Sarah kenan tun da taga Hakkim ta kwallafawa ranta shi. Tun Yana share ta har dai yaji ta kwanta masa da ya fuskanci tana da nutsuwa da kamun Kai sam bata iya shirme irin na 'yan matan ZAMANI ba. Yaji zai iya auranta ko don kyawawan haleyen ta. Ganin ya dauki Hutu yasa Sarah itama ta dauki Hutu a rana daya suka tafi filin jirgi sukayi sallama da juna kowa ya nufi kasarshi cike da kewar juna. Labarin zuwan Hakkim gidan yayi mugun d'agawa Ladidi hankali domin mata mance dashi ba s gidan sosai yanzu ta tsani abunda zai sake hada ta dashi ko da can ma rashin hankali ne amma yanzu ji take bata da babban makiyi kamar shi.... Duk taki sakewa a gidan Sai nukufurci take yi, Cikin su babu Wanda ya fahimci abunda take wa fushi Hjy Asiya dai hankakin ta ya tashi tana jin tsoron kar aljanu su buge ta domin duk ranar da ta tashi da fushi da nukufurci yini take tana tayar da aljanu sai an dauki malamin ta sannan suke gusawa, sai ta samu mijinta tayi masa maganar. General yace." Na fiki damuwa da zuwan Abdul saboda nasan abunda zuwansa zai haifar tunda kina gani tunda aka fara zancan zai zo take fushi ki duba ki gani tafi wata biyar iskar ta bata tashi ba, nasan idan ba'ayi wasa ba zuwan sa zai haifar da matsala." Hjiy Asiya cikinta ya d'uri ruwa domin tana masifar jin tsoron iskokin Ladidi kala-kala suke hawa suke sauka kuma ko wanne idan yazo da budirin sa yake zuwa domin akwai ranar da ta fara tun k'arfe goma na safe basu sake ta ba sai goma na dare akwai wani Wanda ya hau yace a cikin daran nan aje a samo masa k'adangare mai kala hudu har da fad'ar irin kalolin kamar haka *1 bulu* *2 shanshanbale* *2Yalo* *3 Orange* Take Hjy Asiya ta fahimci ko wane k'adangare yake nufi guduwa tayi d'akinta ta bar general yana ar tabu dasu... Cikin daran ya kira Malamin dake mata tofi yazo sannan fa suka gusa tayi ta bacci kamar mattaciya

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39