Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

ihu! Ta kurma Wanda har sai da gurin ya amsa! Dan dai unguwar ma ta masu hannu da shuni ce ko wane gate a gark'ame da irin unguwar yaku bayi ne da tuni ai gurin ya cika da 'yan kallo. Blet din jikinsa ya cire ya fara zabga mata a jikinta kamar Wanda Allah ya aikoshi, dukan ta yake babu sassauci ita Kuma tana ihu! Hade da zaginsa tana yi masa Allah ya Isa. Bai fasa dukan ta ba har sai da yaji bakinta ya mutu ta kwanta a gurin tana nishi hade da ne kare kanta sannan ya mai da blet din jikinsa, ya bar gurin a fusace. Motar su Dady ya ci karo da ita tsananin b'acin ran da ya ke ciki bai sa ya tsaya ya saurare su ba ya wuce abunsa. Tun daga nesa suka hangota kwance hasken Fitilar motar ne ya nuna musu General ya kara sauri har suka Isa inda take kwance nuffashin ta na futa sama-sama a gigice general ya dauke ta ya shiga motar da ita. Hajiya Asiya ta dawo mazaunin dravar ta kunna motar, da sauri General Yace. " Maza mu tafi babban asibiti yarinyar ta suma."!!! Hajiya Asiya ta k'ara k'arfin motar tana fad'in *"Innalillahi wa'inna ilahi raj'inun* *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *Fadima Ummul hasnaini ya tsokar jikin Habibi* ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *πŸ…Ώ37* D'aya daga cikin likitocin dake duba LADIDI ne ya futo yana goge gumin fuskar sa, General ya mike da sauri tare da tarar gabansa hankali a tashi yace." Dr ya jikin yarinyar ne."? Cikin yanayin damuwa Dr ya kalli General yace." Gaskiya yarinyar tayi dogon suma sosai duk iya bakin kokarin munyi domin ta dawo hakan bai yi wu ba, but kwantar da hankalin Ku, zata dawo normal insha Allahu daga nan zuwa gobe." General ya share gumin dake tsatstsafo masa a goshinsa hankalin sa a tashe yake fadin"Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Dr ya gyada kansa cike da jimami yace." Yarinyar ta furgita ne kuma anyi mata dukan mutuwa sosai ta jikkata gaskiya duk Wanda yayi mata wannan duk bashi da imani, yarinya k'arama anyi mata duka irin na masu laifi." General Yayi shiru domin bashi da ta cewa Dr ya girgiza kansa kawai ya bude ofis d'insa ya shige. General zubewa yayi a gurin hankalinsa ya tashi mutuka yanzu yake da ya sanin dauko yarinyar ganin tsautsayi yana nema ya haushi. Hajiya Asiya tazo ta zauna kusa dashi tare da dafa kafad'ar shi muryar ta a sanyaye tace." Dady ka kwantar da hankalin ka insha Allahu komai zai zo da sauki na lura yarinyar bata da cikkakiyar lafiya, sai futuna da ibilici ina ganin Idan komai ya dai-dai ta mai zai hana ka kirawo Liman ya duba ta sosai nasan Idan akwai wani jinnu da suke damunta to zai fada kaga sai mu san ta inda zamu fara." General ya dago kansa yana kallon matar tasa Yace. " Babu babban Mara hankali irin Hakkim da zai kama d'iyar mutane ya dinga jibga kamar Wanda Allah ya aiko shi, yanzu idan wani Abu ya samu yarinyar ba fata nake ba, in je in ce da iyayen ta me."? Hajiya Asiya tace." Dady ka manta Halin yarinyar ko? Ni a ganina abunda Hakkim yayi mata shine dai-dai in ba haka ba baxa ta tsaya ba, yanzu idan ta gudu ta ina za mu fara neman ta cikin wannan gari mai girman gaske." General girgiza kansa kawai yake tabbas shawarar da matar shi ta bashi itace abun dubawa tunda ya Riga ya dauki amanar rike yarinyar tsakani da Allah kuma ya dauko ta daga gurin iyayen ta Dole yanzu duk wani nauyi ta yana kansa. Hakkim kuwa ranshi a masifar b'ace ya koma gida diract part d'insa ya wuce Salima ta biyo shi a baya tana tambayar sa ladidi wata irin shegiyar tsawa ya buga mata, wacce ta sanya ta rugawa da gudu part dinsu. Ya ja tsaki ya wuce part dinsa . takalmin shi bai cire ba ya kwanta rigingine kan bed dinshi yana sakin ajiyar zuciya kana ganinshi kasan a cikin b'acin rai yake, ya rasa wane irin mutum ne Dady dinshi daka ganin sarki fawa sai zak'i, haka kurrum ya d'ako musu alak'ak'ai cikin gida, Ladidi Annabo ce,domin shi kwata-kwata baya yi mata kallo mai hankali ta yaya zasu yi rayuwa da mahaukaciya, dole ma ya bar garinan. Domin bazai iya zama inuwa guda da yarinyar ba, yana jin wata irin tsanar ta cikin zuciyar sa. Kusan awar shi guda a kwance yana sak'e-sak'e daga bisani ya mike jikinshi duk babu dad'i ya fada toilet dinshi ruwa ya hada mai dumi yayi wanka, ya futo daure da towol mai girma wani rataye a wuyan shi, ko mai bai shafa ba, ya zura boxer hade da singilet yayi kwanciyar shi kan bed yana lumshe idon sa, wayar sa ce ta fara ringing yana dubawa yaga Dady ne , gyada kansa yayi yace." Dady kai ka jawo wa kanka wannan masifar wallahi babu ruwana, gobe iwar haka ma ni na bar garin." Har wayar ta tsinke ba dauka ba, wani kiran ya k'ara shigowa hararar wayar yayi, yace." Nasan kan yarinyar zai yi min magana yanda na kwanta ina hutawa ta,wallahi bazan tashi ba." Juyawa yayi hade da gyara kwanciyar sa. General ya kira wayar yafi sau biyar Hakkim bai dauka ba, kuma yana ji, Dan ma kar ya kashe wayar ne General din ya fuskanci wani Abu shiyasa ya k'yale ta, gobe yana tambayar sa yasan k'aryar da zai shirga masa, amma shi babu yadda za'ayi ya tada hankalin sa, kan wata banzar yarinya kidahuma 'yar kauyen k'ayau. General da Hjy Asiya haka suka kwana cikin tashin hankali da damuwa, b'angaran Hakkim kuwa baccin sa ya shirga babu abunda ya dame shi, a subar fari ya tashi, yayi wanka kamar yadda ya saba ya wuce masjid, k'arfe shida shaura ya shigo gidan, ya fara shirinsa domin Sam baya so Dady ya dawo ya tadda shi gidan, yasan wata masifar ce, cikin wasu suit ya futo black and White sunyi mishi kyau sosai ya matse wuyan shi da necktie lafiyayar sumar shi tasha gyara sai kyalli take, kafarshi sanye da helf cover black sai shaining yake yi yayi kyau sosai kalar fatar shi ta futo kamar wani black america haka ya futo hannunsa rike da wata k'aramar jaka. Salima da Baito mai aiki suna Palo Baito na gurin daining tana gyarawa Salima kuwa na zaune kan kujera cikin damuwa kana kallonta kasan bata yi baccin kirki ba, ta na ganshi ta sauke ajiyar zuciya hade da fadin "Broth barka da Safiya ." Nazarinta yake ganin yanda tayi figai-firgai yace." Barka kadai, ni zan wuce idan sun dawo ki Sanar musu, bakinta na rawa tace"Bro ladidi fa har yanzu bata farfad'o ba." Wata irin muguwar tsawa ya buga mata tare da fadin"Don Ubanki ni ina ruwana! Da zaki wani dame ni ki damu kanki, ko wa ya siyi rariya yasan zata zubda ruwa kuje Ku k'arata da ita tunda kune kuka dauko ta ni nayi tafiya, wallahi ko da wasa kika kara

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39