Chapter 16
Chapter 16
dan wani gurin ma d'inkin ya soma zarewa gashi ta tattare sosai ta d'angale mata duk k'waurinta a waje ta saka, ta zura hijabin da take sallah ta tayar da sallah.Bayan ta idar ta tub'e hijab d'in ta aje shi kan gado, haka ta futo babu d'ankwali kai tsaye hanyar futa ta nufa, tunda ta doso gurin suka fara matsawa kowa na k'okarin ya bata hanya kar ta make shi, ball tayi da kofin Alawiyya dake bisa layi, Iya ta juyo da sauri tana fad'in." Kar Ku har gitsa layin fa.' Ladidi ta gani tana k'okarin futa,da sauri tace." Ina zakije a haka sai da nace ki d'aure kanki ke ku kunya ba kya ji." Ko kallonta ba tayi ba ta fuce abunta,girgiza kai kurum tayi ta cigaba da aikin ta tan addu'ar Allah yasa Kawunta na waje ya koro ta, aikuwa D'alha na tsaye da kayan sana'arshi suna gaisawa da mak'ocin su Yahaya,suka had'a ido dashi, sam bata tsorata ba. Ta fara k'okarin wuce shi,tsawa ya buga mata yana fad'in"Koma ki d'auro d'an kwallinki" Ido jazur! Ta koma ta cikin gidan, D'alha yayi sallama da Yahaya ya kama hanya ya tafi, lab'ewa tayi bayan k'yaure sai da ta tabbatar da yayi nisa sannan ta futo, tana ganin Yahaya yana gyara kwatar gidansa, ta galla masa harara, yana sunkuye bai sai abunda take ba, sai saukar Abu yaji a jikinsa, da sauri ya dago yana karkad'ewa sai ga tarkacan da ya kwaso daga kwata suna fad'owa k'asa, bayan rigarsa duk ya b'aci da kwata, waige-waige yake yana neman yaron da yayi masa wannan sha'ani, ido hud'u sukayi da ita, zabura! Yayi ya matsa gefe guda baki na rawa yace." Lad..ladid..katsaye shi tayi ta hanyar fad'in" Jiya har da kai gurin cewa na mutu har kuna shimfid'a tabarma da zama, to ban mutu, kuma duk sai na kashe Ku." Cikin Yahaya ya bada sautin kulululu!! Bakin sa sai motsi yake, zare masa manyan idonta tayi, ganin yanda yake gumi! ne yasa ta k'yalk'ale da dariya "hahahahahaaaa! fyallawa tayi da gudu ta barshi tsaye a gurin,saura kad'an ya saki futsari. Cikin mutuwar jiki ya zauna kan dakalin gidansa yana sauke ajiyar zuciya,sai zare ido yake. Babu inda tayiwa tsinke sai gidan gonar su Hakkim, tana isa ta tarar da an kewaye katangar da waya mai fasa k'afafu dan wani gurin ma har da k'ananun k'walabe, b'uya tayi wani gurin tana tunanin ya za'ayi ta shiga gurin. Can taji motsi an bude kofa, lek'awa tayi kad'an , d'an burni ta hango ya futo daga ciki jikinsa sanye da singlet da wando iya gwiwa 3quetar, suna magana da wani me wanki takalmi, tsura masa Ido tayi tana girgiza kai, a fili tace." Wannan girman jikin naka da wannan k'wanjin naka da wannan murd'ewar taka, duk baza su hanani in d'auki fansa akanka ba, hummm! Ko Kaine Singam gurin k'arfi sai na rama fasa min bakina da kayi." Tana kallonshi suka gama magana da me gyaran takalman ya koma ciki ba tare da kulle k'aramar kofar ba. Da sauri ta futo daga gurin b'uyan ta, kamar walkiya tazo ta shige ciki, Mai gadi nacan na fama da redi'o a hannu, wata bukka ta shiga ta b'uya Kansan kujerun hutawar dake ciki, tana kallonshi ya futo daga wani d'aki hannunsa ruk'e da takalma biyu ya kara futa waje, wuf! Ta futo daga farko inda take, ta afka inda taga ya futo, Sam had'uwar falon ba ya gabanta burinta kawai ta d'auki fansa, ba ta tsaya kalle kalle ba ta afka wani d'aki da tagani a bude, tana shiga ta fara zare ido motsin ruwa taji a band'aki, da sauri ta matse jikinta ta b'uya bayan gado. dama kar ku manta Ladidi bata da k'iba siririya ce sosai, Yusuf ya futo daga toilet yana goge jikinsa da towol, sauri sauri ya sanya kayansa. Ya tsaya gaban mirror yana shafa mai ajikinsa, Hakkim ya shigo d'akin hannunsa rike da takalman su an wanke su tas sai kyalli suke, Yusuf yace." Ka dame ni na tashi na shirya gashinan dai na shirya sai kayi sauri kaima." Zube takalman yayi a gefe guda, toilet ya nufa yana fad'in" Yanda kake da nauyin bacci idan ba haka nayi maka ba ai baza ka tashi ba." Yusuf yace.'' Son bacci da nauyin bacci har na kai ka." Shiru yayi masa ya shiga toilet din, shi kuma yana gama abunda yake ya futa farlor, Ladidi duk tana jinsu, tasan Hakkim ne ya shiga band'aki, futowa tayi daga inda take, ta zauna gefan gadon gami da tsurawa kofar band'ankin ido tana dakon futowar sa. Jikinsa d'aure da guntun towol ya futo cin yoyinsa duk a waje domin babu gajeran wando,a jikinsa dama da k'yar towol d'in ya ratsa masa jiki, yana futowa idonsa ya sauka a nata, tana zaune ta d'ora kafa d'aya kan d'aya, kanta sai k'yalli yake, sam! Bai gane ta ba, domin duk hattun ta sun sauya. Da k'arfi! Yace." Auzibillahi minashaid'anirrajim"!!!! Nan take ya fara karantun ayatul kursiyo, har yanzu idonsa na kallonta itama ta k'ura masa ido k'urrrr!! *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿16* Cikin abunda bai fi second guda ba ya ganta a tsaye kan allon gado,kafin yace me ta buga wani tsallen ta sauka kan dressing mirror, tuni kayan shafa suka fara fad'owa k'asa suna fashewa,ta sanya k'afarta guda ta fara ball da sauran suna fad'owa kan 'yan uwansu, d'aya k'afarta tasa ta baya ta daki! mirror d'in ya tarwatse! Dura k'asa tayi ta tsaya gami da rik'e k'ugu! tana kallon sa. Hakkim kuwa jikinsa duk ya jik'e da gumi! Tamkar ba daga wanka ya futo ba, zuwa yanzu yasan mutum yake tare dashi ba aljan ba,saboda lokacin da take ball da kayan shafar sa ya kalli k'afarta,sosai ya tsorata da ibilicin wannan hallitan mace ko namiji domin dai ya kasa gane wani jinsi ne, k'aramin towol d'in dake rataye a wuyansa ya ciro ya goge gumin goshin sa, ya jefar dashi k'asa,rai a b'ace ya durfafi inda take. Tana tsaye turmin danya tana sauraron isowar sa, sam ya manta da kwalaben da ta fasha,kwalba ta caki k'afarsa me mugun tsini kafin kace kwabo jini ya fara zuba yana bin tayal cije baki yayi cikin azaba! Ladidi ta kwashe da dariya "Hahahahaha" tana nuna shi da hannu,d'ago kansa yayi yana kallonta,shan kunu tayi tace." Ni ce wannan yarinyar ta jiya daka doka na fad'a maka dama sai na rama,ko shugaban k'asa ne ubanka. Hehehhaaha." Ta k'arasa maganar tana mahaukaciyar dariya. Cikin tsananin fushi ya cire d'aya k'afar tashi da niyar d'amk'ota, k'afar ta caki! Wata kwalbar turare me tsini! K'ara! ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39