Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,228 words 0 views Progress saved
Download Book

ya faru tsakanin ka da yarinyar nan? Wallahi hankalina ya tashi sosai domin ta dad'e kafin ta farfad'o,haka kurum daga zuwanmu guri zakayi kisan kai saboda zafin zuciya". Hakkim ya juyo yana fuskantar sa, cikin kaushin murya ya fara fad'a masa abunda ya faru. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." Gaskiya kam yarinyar ba tayi maka dai-dai ba,amma kai ma bai kamata kayi mata irin wannan dukan ba,saboda yadda na lura da ita kamar irin yaran nan masu lalurar k'wak'walwa kasan k'auye ko d'ansu na cuta basa mai da hankali sai abu yayi tsanani, sannan zaka gansu sun nufi asibiti hankali a tashe." Zuciyarsa ce fara sanyi ya zauna kan kujera guda Yusuf ma ya zauna kusa dashi, yace." Ka bari kawai Yaro wallahi zuciyata a lokacin ji nake tamkar na kashe ta na huta da b'akin ciki." "Kayi hakuri don Allah ka rage zafin zuciya." Yusuf yafad'a yana dukan kafad'unsa. Salima ya k'walawa kira, tana can ta shagala da kallon yadda aka tsara falo da kayan jin dad'i da more rayuwa, har ta kunna kallo tanayi taji kiran big broth amsawa tayi ta mik'e da sauri, tana zuwa yace." Ki shiga kchin kiyi mana abunci." "Angama big broth" tafad'a cike da bin umarni, kai tsaye kichin d'in ta nufa, gashinan komai akwai na amfani nan take ta fara aikinta. ********** To can gidan su Ladidiya kuwa Mai koko ta saddak'ar ta fawwala wa Allah cewar Ladidi ta mutu cikin rijiyar don haka mutane sun cika gidan ana yi mata ta'aziyya, Jama'a sun kewaye ta, tana zaune da carbi a hannu ga idonta yayi jajazur! taci kuka ta k'oshi, D'alha na waje da mutane zazzaune kan tabarma, sam yak'i yadda cewar Ladidiya ta mutu cikin rijiya k'wak'walwar sa tafi tunanin yarinyar tana can gurin gantalin ta, shiyasa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zurga-zurga yake a gurin. Duk Wanda yazo gurin sai ya hau yi masa gaisuwa, ko kallon su baya yi ********* Tafiya take fakam-fakam!! sak'e-sak'e kawai take a zuciyarta da tunanin d'aukar fansa kan, d'an burni,sunan da ta sama sa kenan, wallahi bai dake ta a banza,sai ta rama duk hanyar da zata bi ta sani, leb'anta ta tab'a da hannunta, cire hannuta tayi tana girgiza kai! a fili tace."Wallahi he na rama idan ubanka ne shugaban k'asa he na rama, nima sai na fasa maka baki,hummm!! Zaka san ka tab'o Ladidi jikar Mai koko, bana barin takwana kuma bana manta ranar d'aukar fansa." Da tafiyar ta ya gane i tace jiki na rawa ya k'wala mata kira,"Ladidi" da sauri ta juyo tana waigen idan taji ana kiranta. Kakanta ne D'an fulani, yake tawo wa inda take, yana can gurin kiwo labari ya same shi na mutuwar ta,shine ya tawo cikin tashin hankali! Abun mamaki kuma sai gashi ya ganta a hanya, yana k'arasowa inda take ya damk'i hannuta, bai ce mata komai ba suka fara tafiya, zub'uro baki tayi tace." Ni ka sake ni ka rik'e min hannu da k'arfi ai gida zani ba wani guri ba." D'an Fulani yayi mata shiru, shi dai k'okarin shi kawai yaga ya danganata da gida,hankalin kowa ya kwanta. Tun daga nesa jama'ar dake gurin suka hango tawowar su, sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, da suka tabbatar da cewar itace sai kowa ya fara zura silafas d'insa yana guduwa, D'alha ya juya yaga wayam! babu kowa a gurin, girgiza kai kurum yayi yana jin wani d'aci cikin zuciyarsa wato Ladidi ta zama abun tsoro kenan? D'an Fulani ya d'amk'ata a hannunsa yana fad'in"Gatanan can wajejan titi na gano ta tana tafiya ita kad'ai." D'alha ya sauke ajiyar zuciya yace."Alhamdullahi, dama ni jiki na bani yarinyar nan tana raye,amma jama'ar gari suna ta fad'in ta mutu a cikin ruwa,Allah nagode maka daka bayyana mana ita ko hankalin Mai koko ya kwanta." Sai sanan Ladidi ta tuna da abunda ya faru d'azu tsakaninta da Mai koko, dariya ta kece dashi,hahahaha! D'alha ya gaura mata mari! Yana fad'in"Rufe miki don buhun ubanki, shashasha, shakatafe, naga ranar da zakiyi hankali dai" D'an Fulani kuwa a'lamarin Ladidi ya fara bashi tsoro,don haka yace."D'alha mu shiga cikin gidan sai mu San abun yi." Kai tsaye cikin gidan suka shiga. *Tofaa ko ya zata kasance idan jama'ar gidan sukaga Ladidi Wanda suka dauka ta mutu cikin rijiya,ko yaya Mai koko zatayi in taga Ladidi? To Ku cigaba da bina dai cikin labarin domin in warware muku* *COMMENT VOTE AND SHARE* [10/2, 5:54 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *ALHAMDULLAHI* *HAUWA S ZARI'A* _Maman Usuwan_ *Ina taya ki murnar kammala littafin ki HAKA ALLAH YA NUFA _KADDARA TACE_ ALLAH YA KARA BASIRA YASA SAKON KI YA ISA INDA KIKE SO* ____________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM* *🅿14* Suna k'okarin shiga da ita cikin gidan tana turjewa D'alha ya kwad'e mata k'eya yana fad'in "Zaki wuce muje ko kuwa,? Kin tayar wa da mutane hankali, gidan buhun ubanki zaki je ne" Ihu! Ta kurma, wanda yasa Mai koko da sauran jama'ar gidan mik'ewa tsaye da sauri sukayo waje suna salati! Kafin su rufe bakinsu, sai ga Ladidi an shigo da ita tana turjewa! Mai koko ta bude baki zatayi magana D'alha ya katse ta hanyar cewa." Don Allah kar Ku tsorata da ganin ta, dama na fada muku tana raye bata mutu ba, ga shi a can bakin titi d'an Fulani ya gano ta,wanda shima labari ne ya riske har inda yake kiwo cewar ta mutu." Mai koko ta k'araso gurin da jiki a sanyaye zuwa yanzu itama ta fara tsorata da al'amarin Ladidi, da muryar ta wacce tasha kuka ta gaji tace. " Ladidiya dama baki fad'a rijiya ba, me yasa kika yi min haka Ladidi"? Turo baki tayi tace." Nifa ban fad'a rijiya ba, kinga gurin dana b'uyar miki fa" Mai koko tabi hannuta da kallo, cike da mamaki da al'ajabi Matan da suke tsatstsaye a gurin, duk suka tsure sai zare ido suke burin su kawai su bar gidan, Mai koko tace." Me yasa to duk aka duba ba a ganki ba"? Shiru tayi mata, D'alha ya dubi matan dake tsatstsaye, yace." Ko wacce tana iya tafiya" aikuwa kafin kace kwabo duk sun zura takalman su, suna bangazar juna suka futa daga gidan, ko wacce cikin ta ya d'uri ruwa. D'an Fulani yace." Ku zauna zamuyi magana ta fahimta" Mai koko taja hannun Ladidi suka zauna kan tabarma. D'alha suka zauna gan benci, D'an Fulani ya kalli Mai koko a nutse yace." Al'amarin yarinyar nan ya soma bani tsoro saboda haka na yanke wata shawara." Mai koko tace." Ai kana da iko akanta tunda kai ka haifi mahaifiyar ta." Yace." NA yanke shawarar cewa gobe insha Allahu

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39