Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

yake faruwa kinyi cirko!Cirko".! Jiki a sanyaye Mama tace." Gashinan a tsaye ya janyo mana tashin hankali nan ta warware masa duk abunda ya faru. Wani irin bahagon mari! Ya kaiwa Hakkim jikinsa na tsuma! Yace." Abunda ka je kayi kenan shiya dama ka takura dole Kaine zaka fara zuwa."? Hakkim ya dafe kuncinsa ransa a mugun b'ace! Yau shi mahaifinsa ya Mara kan wata "yar iskar yarinya 'yar kauyen k'auyau! Nan take yaji wata muguwar tsanar Ladidi cikin zuciyarsa. General ya cigaba da cewa." Duk irin jan kunnen da nayi maka kan yarinyar ashe baka ji ba, kanan da muguwar zuciyar ka, OK shikkenan ka sani mutukar yarinyar mutane ta mutu ko ta nakasa ta dalilin ka babu shakka! Zan barka da Matsalar ka ne domin ni ba abunda ya shafe ni bane ko me hukuma zatayi maka tayi maka, ni zan bada tawa gudumawar." Salim ne ya shigo ya tarar da tashin hankali Mama na kuka Salima na kuka gogan na tsaye idonsa yayi jazur General sai surfa masa bala'i yake, nan Salim ya tambayi abunda yake faruwa Yusuf ne ya warware masa komai. Shima ya kad'u sosai kuma ya rausayawa Dan uwansa saboda yasan b'acin ran mahaifin su bashi da kyau mugun mafada ci ne. General ya kalli Mama cike da bada umarni yace." Ku shirya muna yin sallahr La'asar zamu dauki hanyar Kano dole ne muje mu ga halin da yarinyar ke ciki, duk inda take za binciko min ita." Mama tace." To Allah ya kaimu." Sama ya hau ya barsu suna tunanin abunda zai faru a gaba addu'a kawai suke Allah yasa yarinyar bata mutu ba. Hakkim yq mike ba tare da ya kalli kowa ba ya zura takalmin shi ya futa ransa a dugunzu me, ya lura da Dady ya dauki serious kan al'amarin, wato Sam!shi ba'a duba irin b'arnar da yarinyar tayi masa abun ya kai har da duka abunda bai tab'a faruwa ba tsakanin shi da mahaifinsa tunani yake wane irin hukunci ya kamata ya yanke kan yarinyar. ******** Ladidi kwance cikin jini gefen kunne ta ya fashe yana digar da jini gashi ya kumbura leb'anta ya kumbura had'e da saman idon ta,duk hallitun fuskar ta sun jirkita tana kwance bata san in da take ba, hanya ce da ba kowa ne yake bi ba sai masu kiwo sune suka bi tare da dabbobinsu shiyasa har yanzu babu Wanda ya kawo mata dauki. D'an Fulani ne ya shigo gurin tare da d'anshi Mati da dabbobin su, sai da suka zo dabda ita sannan suka fahimci mutum ne a kwance ,Mati yayi saurin birkitoto kawai sai yaga Ladidi d'iyar yayarsa Amina, me rasuwa, cike da tsoro ya kira mahaifin nasa yana fad'in "Baffa zo ka ga Ladidiyar Mai koko ce....... *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿20* Da sauri d'an Fulani ya k'araso gurin, hankalinsa a tashe yace." Maza d'auke ta muje gida nasan ana can ana neman ta." Mati ya sab'ata a kafad'a bata san inda kanta yake ba, suka nufi gida. Mai koko na aikace-aikacen ta na gida kawai taga an shigo da Ladidi a kafad'a, da sauri ya yar da tsintsiyar hannunta tana salati, Mati ya shimfid'eta a tabarma da sauri ya nufi gidin rijiya ya jawo ruwa cikin wata roba ba tare da b'ata lokaci ba yazo ya kwara mata a fuskar. Minti biyar tsakani ta saki wata wawar ajiyar zuciya, nuffashin ta ya dawo amma kuma bata bude ido ba. Mai koko ta dinga share hawaye cike da tausayin ta tace." A'ina kuka ganta kuma waye ya fasa mata baki har ya zubar mata da jini."? Dan Fulani yace." Inda kika ganta muma haka muka ganta kwance hanyar titi bata san inda kanta yake ba. Amma nafi tunanin wani tayiwa rashin kunya ya gwada mata rashin imani." "Shiyasa kullum nake gargad'inta da rage haikewa manya domin nasan watarana dole ta had'u da wanda zai hukuntata." tafad'a tana goge hawayen ta da gefan zanin ta. D'an Fulani yace." Ai tun farko an fada miki abunda za'ayi mata a huta kink'iji, ni kinga tafiya na Dade da sanin duk lalatar da yarinyar take kece kike daure mata gindi,ni babu abunda zance sai dai ince Allah shi kyauta." Yana gama maganar shi ya kad'a kansa ya futa, Mati ya rufa masa baya Mai koko tabisu da kallo cike da takaici ya share hawaye tace." Duk dan kunga marainiya ce shiyasa kuke mata haka, wallahi idona idon wanda yayi wa jikata wannan b'arnar sai na rotsa masa kansa shima." Ta fada cike da jin haushi da takaici, Ladidi ta fara motsa idonta a hankali -a hankali ta bude tana kallon Iya, tayi saurin dafe kanta tana rumtse ido! Da sauri Mai koko ta rike hannun tana yi mata sannu, da k'yar tace." Iya bani ruwa insha wayyo kaina!!!! Iya ta mike da sauri ta d'ebo mata ruwa. Ta tashe ta zaune tare da karata a jikinta ta fara bata ruwan. Kad'an tasha ta kauda kanta. Mai koko tace." LADIDI ina kikaje waye yayi miki wannan dukan. "? Kamar da dutse take magana. ta kara maimaita maganar tata. Ladidi batasan ma tanayi ba hannunta ta tab'a tare da fad'in ." magana nake miki fa." Da k'arfi tace." Iya me kika CE." Itama Iya sai ta bud'e murya sosai tace." Cewa nayi waye ya doke ki haka har ya kumbura miki fuska tare da zubar miki da jini."? Kuka ta fashe dashi tace." Wani d'an burni ne ya doke ni babu abunda nayi masa kawai don na zo wucewa Iya Allah kuwa sai narama bazan barshi ba." Cike da takaici da jin zafi tace." Ai nima bazan barshi ba,sai nabi miki hakkin ki, domin bazai shigo garinmu yaci albarkaci na kuma ya doke ki har da zubar miki da jini kowa daga ya tashi muguntarsa sai yace ke,to sai nabi miki hakkin ki, ko dame yake tak'ama kuwa.". Kuka sosai Ladidi take, hankali Mai koko ya kara tashi, tunda taga Ladidi na kuka tabbas tana jin jiki. ********* K'arfe biyar shaura kwata sun shirya tsaf! suna tsatsaye a harabar gidan suna jiran futowar general, kana kallon fuskokinsu kasan suna cikin damuwa, mussaman Hajiya Asiya. General ya futo cikin sauri yana d'aura agogo hannunshi, duk ya bisu da kallo, yace." Ina Hakkim d'in yake." Yusuf ya sunkyar da kanshi yace." Bai futo ba." Cikin b'acin rai! General yace." Maza jeka kira shi,Hakkim yana so mu sanya k'afar wando guda dashi wallahi." Salim yace." Dady kayi hakuri " ko kallonsa baiyi ba ya shiga mota Mama da Salima suka bude suka shiga. Minti biyar tsakani sai gasu nan sun futo Hakkim

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39