Skip to content

Chapter 37

Chapter 37

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,224 words 0 views Progress saved
Download Book

ta tashi a jeme duk tayi rama abun tausayi. General yana bala'in tausayawa rayuwar yarinyar marainiyar gaba da baya tarin almutsutsai sunyi kaka gida a jikinta fatan shi ma Allah yasa su barta tayi aure. Kwantar mata da hankali yayi yace." Duk wani Abu da kika San zata gani hankalin ta ya tashi sai ki guje shi kuma shima Hakkim din ki ja masa kunne sosai ni kaina sai na gargade shi kan yarinyar babu ruwan shi da ita." Hjy Asiya ta mike jikinta duk babu kuzari Salima kuwa tafi kowa rud'ewa a gidan. **** Shi Hakkim da ake abun domun shi Sam ya manta da wata Ladidi soyayyar Sarah ta mantar dashi wata 'ya mace don haka da kuzarin sa ya sauka a k'asar tashi ta gado, fuskarsa cike da fara'a ya rungume Dan uwansa Salim da yazo daukar shi. B'ata fuska yayi yace." Bro me ya hana Dady zuwa daukana ne kamar yanda ya saba."? Salim yace." Wallahi kwana biyu yayi zazzab'i shine fa jikin NASA bai yi kwari ba har yanzu... Suna kokarin shiga mota Hakkim din yace." Shine ni saboda an raina ni aka ki fada min." Salim na driving yace." Am sorry bro laifina ne."! Kafadar sa ya buga yace." Zan hukunta ka kuwa." Salim yasa dariya yana bashi hakuri yace." Bro ka kara girma da kyau ba kamata yayi ka kawo mana big aunt. "!!! Hakkim yayi murmushi hade da fadin" kar ka damu tanan zuwa insha Allah." Salim yace."Alhmdullahi dama dady yana ta so yaga baby's a gaban shi." Cikin barkwanci Hakkim din yace. "Kai ka fara kawo masa baby's din mana." Salim yace." UmUm!!! Ai Kaine babbana." Dariya suka sa a tare cike da nishadi to a haka suka isa gida Cikin farin ciki da kaunar junan su irin na 'yan uwanta ka. *5/12/2018* *BintuUm@rAbb@le* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *πŸ…Ώ42* Hajiya Asiya ta tari Hakkim cikin kulawa da 'kauna irin ta uwa da d'anta, a parlor suka zauna ta cika gaban shi da kayan ciye-ciye birjik yace." Momy wannan delicious din duk ni kad'ai lallai kinyi kewa ta da yawa." Cikin jin dad'i tace"Dole my son nayi kewar ka sosai shekara guda ai dole in tar'be ka da muhimanci." Dariya yayi yace." Momy nazo miki da labari mai dad'i fa." Tace"Masha Allah gama cin abincin ka bani na sha." Murmushi yayi ya fara cin abincin sa cikin nutsuwa. Salim yace." Momy ni kin manta dani kenan." ? Tace" Ka bari tukkuna ya kammala sai kaci sauran." Cikin shagwa'ba yace." Momy ni bazan fi sauran ba sai kace wani al'majiri." Dariya suka yi masa dukanin su. Hakkim ya kammala cin abuncin ya dauki tissue ya goge bakinsa ya kalli Momyn sa yace." Wai ina dady ne."? Tace"Yanzu zai shigo yaje d'auko Aminatu a makaranta. " Cike da mamaki yace." Momy wacece Amina da har dady zai je d'auko ta a makaranta."? Ganin yanda ya 'bata fuska yasa Momy gyara Fuskar ya tace"Ladidi nake nufi ba ka dawo gidan ba tom babu ruwan Ka da ita don ba cikkakiyar lafiya ne da ita ba, don Allah kar ka shiga harkan ta." Jin ta ambaci sunan yarinyar da ya tsana duk duniya yace." Momy har yanzu baku maida yarinyar gida ba."? Tace"Wane gida kuma? Karma ka sake Dadyn Ku yaji wannan maganar daga bakin ka zai 'bata maka rai! Nima kaina abun sai ya shafe ni." Babu walwala a tare dashi yace." Momy kan yarinyar nan wallahi zan iya koma wa inda na futo nifa kallonta bana son yi wallahi." Salim yace." Aikuwa zaku yi fad'a da Yusuf domin budurwar sace Wallahi ka iya bakin ka." Hakkim ya kawo hannu ya gwa'be bakin Salim d'in ya goce da sauri yana dariya. Tsaki yaja cikin 'bacin rai yace." Yusuf bai da hankali wallahi ko meye abun so jikin 'kanjamammiyar irin wannan mtssss." Salim Yace. " sanin da kayi mata a da kenan, amma Yanzu indan ka ganta zaka sha mamaki." Mi'kewa yayi yana fad'in"Momy ni zan je in kwanta in huta zuwa anjima." Tace"To my son sai ka futo." 'Kokarin futa yake yi General ya shigo parlor Ladidi na bayan sa tana sanye da kayan makaranta. Baya ya matsa yana fadin "Dady barka da shigowa." Hannu general din ya mik'a masa suka yi musabaha kana yace." Dady na same Ku lafiya."? General yace." Lafiya Lou Alhmdullahi ya aiki? Ka samu lafiya kaje ka samu guri kayi Uwar 'kiba mu kuma nan ka barmu da zan can Ka." Dariya yasa yana Sosa kansa yace."Dady ban in na kira wayar ka baka d'auka ." General d'in yace." Kai kasan dalilina ai kuma ka kiyaye babu ruwan ka da yarinyar mutane." Yafadi maganar babu alamun wasa a tare dashi. Yace." Dady ka kwantar da hankalin ka ni da wuri zan koma ma." Ciki general d'in ya shiga yana fad'in"Wannan kuma Matsalar ka ce ni dai na fad'a maka." Ladidi ta 'kura masa ido kurr! Tana mamakin irin Uwar 'kibar da yayi ya 'kara haske abunshi. Had'a ido suka yi shi da ita, yaji gabansa ya fad'i! Ta maza yayi ya maze yana danne zuciyar sa yace." Kauce ki bani hanya." Harara ta watsa masa kana ta matsa daga bakin 'kofar. Futa yayi niyyar yi ya sanya 'kafarshi dake cikin takalmi sahu ciki ya take mata 'kafa cike da mugunta.! Aiko tsigar jikinta ta fara mi'kewa ta fara jin wani irin jiri 'kara ta 'kwala!! Ta zube a gurin tana fuzge-fuzge! Ihun 'karar ta ne ya dawo da shi parlor sai ya tadda ita a kwance 'kasan tayel su General sun rufu a kanta suna yi mata tofi ita kuma sai fuzge-fuzge take wata irin kumfa na futowa daga bakinsa. Dariya abun ya bashi amma ya dake ya 'karaso gurin yana le'kenta aikuwa ta zaburo! Da sauri tayo kansa.! Cikin jarumta ya tsaya a gurin Hajiya Asiya cikin tsoro take fad'in"Ka futa da sauri! Maza! Ka futa Kaine basa son su gani." Cike da mamaki! Yace." Momy su waye."? *10/12/2019* *BintuUm@rAbb@le* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *πŸ…Ώ43* Kafin ya rufe bakinsa Ladidi tayi wani yun'kuri inda ta buge General da yake tsaye a kanta yana tofa mata addu'a duk da tazo bakinsa, kan Hakkim tayi gadan-gadan! Ganin da gaske take tayo kansa zata d'afe jikinsa da sauri ya buga tsalle yayi gefe guda cike da al'ajabi abunda yake faruwa tabbas Yarinyar aljanu take yi domin dai duk lafiyayan mutum ba zai dinga wannan buge-bugen ba. General yaje ya dauki wayarsa da sauri! Ya kira wayar Malam yace." Maza yazo babu Lafiya to da yake gidan malam din babu nisa dasu minti goma ya shigo cikin parlor yasan tunda aka kirashi abun ya ci tura, kan Ladidi yayi dake kwance tsakiyar parlor tana wani irin matagugu kumfa na futa daga bakinta ga idonta duk ya jirkice gashin kanta ya ya mutse! Duk me imani a lokacin sai ya tausaya mata, Hakkim dake tsaye bakin 'kofa yaji ta bashi tausayi babu shakka aljanu

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39