Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
Download Book

akwai k'ananun k'usoshi saboda tsaro (Security) Hjy Baito masu gadi sakin baki suka yi suna kallon hatsabiban cin yarinyar. Cikin rarrashi Hjy tace"Aminatu ki rufa min asiri ki sauko don girman Allah kar ki kashe min aure na." Ko kallonta Ladidi ba tayi ba, k'okarin dirga k'asa take k'afafunta har sun fara fidda jini. Hjy ta kalli Salima dake tsaye tsoro ya cika mata ciki tace"Maza je ki kira Dadynku nasan dai yau sai ta Allah, bazai tab'a karb'ar uzirina ba." Salima ta wuce cikin gidan da sauri. Rarrashin ta suke sosai kan ta sauko kar ta jiwa kanta ciwo Ladidi ko sauraran su bata yi, kokari kawai take ta sauka k'asa. Hawaye Hjy Asiya ta fara sharewa tana fad'in"Ashe tsautsayi ne yasa muka d'auko ki muka kawo ki anan Amina ki rufa mana asiri idan kika fad'o daga wannan ginin ai idan baki mutu ba, to babu shakka sai kin kakkarye." Ganin tana k'okarin zura k'afar ta k'asa yasa d'aya daga cikin masu gadin gidan ya futa da gudu, domin ya tare ta ko da zata fad'o. Raba k'afafunta tayi d'aya cikin gidan d'aya a wajan gidan, ta kalli Hjy Asiya tare da turb'u ne fuskarta tace'Wato kun kawo ni nan gidan domin Ku yanka min kai ko? Hahahahaha na gane ku ai." Hjy Asiya ta fara rantse-rantse muryar ta na rawa! General na hango ya tawo a sukwane! Tun daga nesa yake hango abunda yake faruwa, wani irin zufa ne ya tsinke a jikinshi kamar ba daga wanka ya futo ba. Ya k'arasa gurin da sauri yake fad'in"Aminatu me akai miki? Sauko kinji ki fad'a min me kike so in siya miki kar ki fad'a kasa Aminatu."! Dariya tayi tana kallonsa tace"Baba duk na gane Ku wato kun kawo ni kuyi cinikin kaina ko hahaha to kafin Ku siyar dani ni zan siyar da kaina, domin fecewa zanyi sai inga Wanda zaku siyar." General ya sharce gumin dake tsatstsafo mishi a goshi duk ya rasa me zaiyi, Salima ya kalla da sauri yace." Kira min Hakkim a waya kice masa duk inda yake yazo yanzu-yanzu." Da sauri ta koma Cikin gidan domin ta dauko wayar ta. Har yanzu Ladidi na tsaye kan Katanga tana kallonsu suna kallonta Da wayar a hannunta ta futo tana laluben numbar Bigbrth kamar yanda suke kiran shi, "Dady wayar tak'i shiga." Tafad'a bakinta na rawa.General ya karb'i wayar da sauri yana k'ara gwada kiran. Cikin sa'a ta shiga,Hakkim ya dauka had'e da Sallama, Dady yace"Kana ina ne."? "Dady muna tare da Salmanu muna k'arasa shirye-shirye mybe ma, ba a gida Zan kwana ba." General yace."Kwana a gida ya kama ko domin mun shigo garin yanzu haka ma muna gida, maza! Ka bar Abunda kake yi kazo, yarinyar nan tana kokarin jawo min bala'i." Yace." Wace yarinya Dady." ? Kashe wayar general yayi ba tare da ya amsa masa ba. Da sauri ya mike hade da d'aukar key d'insa sukayi sallama da Salmanu ya futo cikin sauri ya shiga motar sa, hade da fuzgarta da gudu. Tunani yake a mota me Salima take kokarin ta aikata Wanda har ta tayar da hankalin Dady haka, shi Sam! Bai kawo cewar Ladidi ba ce. *BINTA. U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *10/November/2019* ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ ```Shirafa'u 'yayan Nana kusa ni cikin masoya``` _________________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *πŸ…Ώ35* Tun da ya shigo da motar layin nasu hango abunda yake faruwa. Cikin mamaki ya k'araso da motar tare da yin parking ya futo da sauri idanunsa a sama yana so ya gazgata abunda idonsa yake nuna masa. Tabbas Wannan aljanar yarinyar ce,kenan Dady da ita ya tawo garin abuja. Tambayar kanshi yake babu amsa. Haladu mai gadi ya k'araso kusa dashi bakinsa na rawa yace." Allah ya taimake ka ka taimaka mana ka sauko mana da wannan hatsabibiyar yarinyar daga sama ga Hajiya can tana zubar da hawaye... Hakkim bai karasa jin abunda Haladu yake fad'a ba ya wuce da sauri! Cikin gidan ya shiga. Dady ns tsaye sai magiya yake zabgawa LADIDI kan ta sauko daga saman gurin, Momy da Salima na gefe suna matsar hawaye. Daga kansa yayi yana kallon Ladidi dake tsaye tsakanin wayoyin dake kewaye da gurin ta raba k'afafun ta gida biyu d'aya a cikin gidan d'aya a waje. Sosai yake mamakin yanda a kayi ta hau gurin tunanin yake ya za'ayi ya fuzgota daga gurin, futa yayi waje da sauri, Haladu na tsaye hankalinsa na sama yana gadin LADIDI ko da zata fad'o sai ya tare ta. Cikin ikon Allah hankalinta na cikin gidan General ya dauke mata hankali gurin magana, Hakkim yace da Haladu yayi masa dokin wuya aikuwa haka aka yi dokin wuya yayi masa jikin duguwar gatan gar akwai guraran rodi da a had'a dasu ba gurin gini nan Hakkim ya kama cikin dubara ya haure katangar hannunsa suka cake da k'ananun k'usosi jini ya fara zuba! K'afar ta guda ya fuzgo da k'arfi ta kifo jikinsa suka fad'o k'asa tare. General da sauran mutanan gidan suka runtumo da gudu suna salati domin su duk a tunanin su ta fad'a ne kamar yanda take fad'a musu. Sai suka gan ta kwance saman ruwan cikin Hakkim, Wanda yake mata wani irin mugun kallo na tsana idonsa yayi jawur!! Ga hannunsa yana d'igar da jini. Ladidi idanunta a k'ek'ashe take kallonsa, babu alamun risina a tare da ita,Hakkim ya mike a zafafe! Ya watsar da ita a gurin. Ta mike da sauri hade da d'ibar k'asar gurin kamar yanda ta saba ta watsa masa a jikinsa ta runtuma da wani irin gudu ta dauki hanya ...... Da gudu ya bi bayan ta, General ya zube a gurin hade da dafe kansa Cikin tsantsar tashin hankali. Salima tace"Dady dama na fada maka wannan yarinyar zata iya d'ora wa mutum hawan jini Dady tun kafin ta jawo mana wani bal'in gwara gobe a mayar da ita gudansu. Hajiya Asiya kuwa ta daina matsayar hawayen yanzu abun tsoro yake bata sosai take zargin yarinyar da motsuwar k'wak'walwa idan ba haka ba kuma to tabbas da akwai aljanu a kanta. Gudu take kamar wata filfilwa, Hakkim ya k'ure gudunsa domi ya tadda ita Sam baya son ta futa titi a haka yasan ba k'aramin kunya bane a ganshi yana falfala gudu kamar wani zararre. Duk iya gudu irin na Hakkim kasa cin mata yayi, ya sare mutuka yanzu ya kara tabbatar wa da cewar yarinyar annoba ce a gare su. Cak!!!! Ta tsaya jin haushin karnuka wan! Wan! Wan!wan! Haushin ya cika gurin. Tana haki! Ta waiwaya bayanta ta hango Hakkim ya kusa cimma ta, ta kalli gabas kudu a rewa babu gurin b'uya ga karnuka sun taso mata, ihu!! Ta kurma hade da d'ora hannunta a kanta tana fad'in"Wayyo Allah Mai koko Wayyo na Iya shikkenan mun rabu da juna sun kawo ni gidan yankan kai, Dama sai da kika ce kar na zo nace sai Nazo shikkke....... Bata karasa ba ya k'araso gurin yana wani irin huci! Ya sanya hannunsa ya kwad'e mata bakinta da. Mugun k'arfi Bakin ya fashe da sauri! Ta sanya hannunta ta Dan gwalo jini daga bakinta. Wani razanannan

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39