Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

zata kaiku har *Dausara* sai ku tsaya dai-dai majalisar Yahaya kuce ina ne gidan Iya Mai koko insha Allahu za a nuna muku nan ne gidansu Ladidi." Yusuf ya zura hannu a aljuhu ya Ciro gudar dubu daya ya mik'a masa, yana godiya, Da sauri ya karb'a yana zabga masa godiya Motar yaja suka k'ara gaba. ****** D'alha da Yahaya na zaune a kan dakali suna hira Duk 'yan majalisar sun tashi, nan D'alha ya samu damar fad'awa mak'ocinsa Yahaya abunda ya faru da Ladidi Sosai Yahaya ya jimanta al'amarin yace." Yanzu kana nufin jarin ka zaka rusa kan yarinyar nan D'alha ka k'yaleta kawai tunda tana ji kad'an kad'an sai nake ganin kamar wahalar da kanka zakayi kan hakan.' Ajiyar zuciya D'alha ya sauke yace." Wallahi Yahaya ina mutukar tausayin rayuwar Ladidi marainiya ce bata da uwa babu uba sam bata san su ba bata da gatan kowa sai ni sai Ubangiji kaga kuwa dole in tsaya kan lafiyarta domin nasan amana ce a hannuna." Yahaya yace." Da ina da wasu kudi a aje dana ranta maka gaskiya bana so ka taba jarinka." "To yaya za'ayi insha Allahu zai farfad'o." Haske mota suka hango tun daga nesa yana haske su. Yahaya yace." Baki mukayi daga burni kenan.'? D'alha yace." Da'alama dai." Ido suka zubawa motar har ta k'araso inda suke. Yusuf yayi parking suka futo a tare. Suna isa kusa dasu suka mik'a musu hannu suka gaisa, Hakkim yace." Da Allah muna neman majalisar Yahaya ne." D'alha yace." Gatanan ga Yahaya nan yana jin ka." Yace." Gidan Iya mai koko muke nema." Da hannu Yahaya ya nuna musu kofar gidan. Hamdala Yusuf yayi yana jin farin ciki, yace." Nan wata yarinya Ladidi take." Yahaya yace." K'warai kuwa ince ko lafiya."? Hakkim ya juya ya da niyyar shiga mota a cikin zuciyarsa yace." Tunda anga gidan kome me sauki ne, gwara inje in kwanta in huta ko na samu Dady ya k'yaleni." Bayani Yusuf ya tsaya yana musu Hakkim ya kunna Mota da k'arfi yake masa hon!!! Yusuf yace." Kuyi hakuri Insha Allahu gobe zamu zo da safe kome ye sai ayi." Yana gama maganar yaje ya bud'e mota ya shiga, Yusuf ya fige ta suka bar gurin. Cikin takaici yace." Duk wannan abun bazai kai maka ba, don ma ka samu ina taimaka maka na tabbata da kai kadai ne sai dai ka kwana a kauyen nan kana tambaya baka samu ba, shine kake k'okarin tafiya ka barni. " Shiru yayi masa yana draving, Yusuf ya dunga masa mita hat suka Isa masaukinsu. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿22* Motar su na barin gurin. D'alha ya mik'a da niyar shiga gida yana mik'awa Yahaya hannu sukayi sallama kowa ya shiga gida. Cikin bacci taji kamar murya D'alha yana tashin ta, ta mike zauna tana gyara d'aurin dankwalinta. Hasken Fitilar kwai ta karo tace." Lafiya kake tashina bacci na yayi nisa wallahi." D'alha ya zauna gefen katifar da take zaune yace." Wasu mutane ne suka zo yanzu, wai suna Neman Ladidi." Bude ido tayi sosai gabanta na fad'uwa tace." Wace Ladidi kuma,wacce yinin yau bata futa ba balle ace tayi Wani Abu." Kwantar da hankalin ki Iya suma basu ce tayi komai ba, sun dai ga gidan sun ce gobe zasu dawo da safe." Iya tayi jigum! Tana kallon Ladidi dake shararar baccinta tace." Kaganta nan ta sha wahala kafin bacci ya d'auke ta, motsi kad'an sai tace kunnenta." D'alha yace." Da'alama ai kunnen ba k'aramin bugu akayi masa ba." Iya ta share hawaye cike da tausayin jikar tata tace." Ko waye wannan ba k'aramin azzalimi bane wallahi. " Shiru D'alha yayi domin baya so ya tanka maganar yasan laifin Ladidin ne. Mik'ewa yayi yana mata sallama, har zai futa ta tsayar dashi tana cewa." Kace gobe babu koko ko."? "Eh kin san zamu futa da safe sosai domin mu kama layi,sai dai hanzari ba gudu ba, mutanan da zasu zo." Iya tace." Hakane kuma dole mu jirasu domin muji da abunda zasu dashi." ****** Lokacin dasu Hakkim suka koma gida babu kowa a farlo sai General kawai duk sun je sun kwanta, yana zaune yana jiran dawowar su Ko zama bai bari sunyi ba yace." Kun samu inda take.? Yusuf yace." Eh Dady mun samu saboda dare yasa muka ce mu bari gobe da safe sai mu koma." Dady ya mike tsaye yana kallonsu yace." Allah ya kaimu gobe nima dani za'aje domin inga inda yarinyar take." Shiru sukayi kai a kasa sai da ya wuce tukkuna suka dago Kansu, Hakkim ya zube. Cikin kujera yana shafa kansa yayi wata muguwar gajiyq Yusuf kuwa tv ya kuna ya zauna yana fadin ." duk yanda kake ganin ga gaji ni nafi ka gajiya wallahi." Hakkim yayi masa shiru yana lumshe ido, mik'ewa yayi ya nufi firji domin d'auko Lemo ko ya samu ya samu sassauci a zuciyarsa. ****** Da safe da k'yar Iya ta taimakwa Ladidi tayi wanka domin jikin nata ya kara d'aukar zafi mussaman gefen wuyanta wanda da k'yar take iya motsa shi, har dan kumbura yayi. Tana zaune cikin wani leshi wanda ya gaji da kodewa yayi haske sosai dinki riga da zani ne da d'ankwali Iya ma ta shirya tsaf hijab dinta na aje a gefe D'alha ya shigo ya tarar dasu suna karyawa iya na lallaba ta tasha koko, tana kin sha, saboda zafi da take ji gurin hadiyar abu shiyasa ma ko kosai ba ta Ciba. Iya tace." Har yanzu basu zo ba ko." Daga kai D'alha yayi Yace. " gashi yanzu k'arfe takwas ba." Tace." To ai sai muta fi domin ba zamu tsaya su katse mana abunda mukayi NIyya ba." Yace." Hakane kuwa hankali na ya kara tashi da yanda naga yarinyar ta tashi da jiki yau." Iya tace." Yanzu da k'yar take hadiyar koko dan taki cin k'osai ma." Kallonta D'alha yake cike da tausayi..... Sallama suka ji daga waje D'alha ya mike da sauri ya futa ***** Gaban shi ne ya fad'i ganin hamshakin mutum jingine da mota, fuskokin su Hakkim yake karewa kallo yana so ya fahimci ko sune mutanan na jiya. A hankali ya k'arasa kusa dasu ya dan rankwafa gami da fadin." Barka da zuwa ranka ya Dade." General ya mik'a masa hannu fuskar sa a sake yace." Barka kadai samari fatan mun same Ku lafiya. " D'alha yace." Lafiya lau Alhaji." Hannu ya mik'awa su Hakkim sukayi musabaha ga juna yace." Hala kune bakinmu na jiya da daddare ko."? Yusuf yace." Mune wallahi." D'alha yace." To bari in shiga gida in sanar da mahaifiyata dama yanzu muke shirin futa." General

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39