Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

abuja ne yanzu shirin da nake kenan wallahi." Wani kallo General din yayi masa yace." Ka koma abuja kayi me."? Kansa ya Sosa yana shirin kirkiro k'aryar da za shirga. General din yace." Kaga Malam bama son rashin abunyi kawai ka shiga mota kamar yanda nace.ai na gano abunda zai sanya ka koma abuja yau din." Cike da takaici Hakkim ya bud'e kofar mota mazaunin dravar ya shiga yana jin wani kunci da takaici a zuciyarsa Wato shi ya zama dravar kenan ? Shi da yazo Hutu an mai she shi dravar saboda tsabar bashi da galihu dravar ma na kucakar yarinya 'yar k'auye me kwarkwata gami da karzuwa, ya zame masa dole ya bar garin nan.domin ya fuskanci Dady ya shirya tsaf! Gurin ganin ya kuntata masa. Suka hau titi sosai sai gudu yake Ladidi ta tsira da k'arfi tace." Baba kace dashi ya daina gudu nan da yake tsoro nake wallahi." General yayi saurin kallon Hakkim yace." Ka kula mana ka rage gudu sai shilla mu kake kamar zamu tashi sama." Hakkim bai san sanda ya daki kan motar ba saboda tsabar takaici wato yanzu Dady shima umarni Yarinyar take bashi. General yace." Kai meye haka kuma? Kai da aka ce ka rage gudu zaka daki kan mota ." Hankalinsa ya dawo cikin wayancewa ya Sosa kansa bai ce komai ba ya rage gudun da yake yi. Shi ko General ya juya ya cigaba da hirarasa dasu Ladidi wacce Salima take ta zolayarta ita kuma sai zantuka take mata irin na shashanci. A hankali yace." Dady mun futo cikin gari wace kasuwa zamu shiga ne." ? General yace. " anya kuwa zamu shiga kasuwa yanzu dubi lokaci 1:00 na rana muje Sahad stor kawai duk abunda ake bukata za'a samu." Bai ce komai ba ya juya kan motar zuwa Shahad Sto zuciyarsa na masa zafi DOMIN ya fuskanci Ladidi za'ayiwa siyayya. Parking yayi inda aka tanada suka futo shi kuma ya gyara zama cikin motar bashi da niyyar futowa.General yace." Ka futo mu shiga tare mana." Girgiza kansa yayi tare da fad'in "Dady Ku shiga kawai bana bukatar komai." General yace." Sai ka futo fa domin ni banga amfanin zamanka cikin motar ba." Hakkim bai iya musu ba bare ga mahaifinsa sai ya bude mota ya futo kawai yana jin taikacin takura sa da Dady yayi abunda ba halinsa ba. Suna shiga ya samu kujera ya zaune fuskar nan a murtuke,wayarsa ya Ciro yana latsawa . Dady suka wuce ciki shida su Salima.Ladidi sai K'auyan ci take zubawa sosai jama'ar da suke ciki suka dinga kallonta kamar sun samu TV Dady sunyi gaba shi da Sallma bai San ta tsaya a baya ba, tana hauka ganin wani takalmi me mugun tsini da jakarsa cikin wani glass sai d'aukar ido yake kokari kawai take ta bude glass din ta Ciro takalmin fad'i take." Yeeeeeh kan uban can kunga wani hegen takalmi kamar jirgin sama wallahi sai na d'auko hi." Hannunwanta biyu ta sanya tana k'okarin zuge glass din sai wata mahaukaciyar dariya take. Aikuwa kan kice kwabo jama'a sun fara Ciro wayoyinsu suna mata video suna dariya, wata mata tazo ta riketa tana fadin "Ki tsaya mana a zo a bude miki." Bangaje ta tayi ta fad'i a gurin.daya daga cikin ma'aikatan gurin ya k'araso da sauri yana mata magana, ko kallonsa ba tayi ba ta cigaba da abunda takeyi. Cikin zafin rai ya k'araso gurin ya juyo da ita a zafafe ya shimfid'a mata wani bahagon mari! Ji kake Tass! Tass! Har sau biyu. https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *23/October/2019* *29* Wani uban ihu! Ta kurma Wanda ya jawo hankalin mutane da dama dake cikin gurin ciki kuwa harda General da Salima dake can b'ngaran kayan tea Salima na had'awa, da sauri General ya aje kwalin Milo dake hannunsa domun ya fahimci Ladidi ce take kurma ihu!! Yana zuwa yaga dandazon mutane sun kewaye ta, ga Hakkim a tsaye a kanta yana zazzaga mata masifa tare da zaginta da fada mata munanan maganganu. Cike da b'acin rai ya k'arasa gurin yace." Wai me yake faruwa ne? Take wani ma'aikacin gurin ya fara fad'a masa duk abunda ya faru, ya kalli Hakkim ransa a b'ace yace" kan ta aikata haka ka dake ta.? Shiru yayi yana kauda kansa yaso Dady bai zo gurin ba ya wulakanta ta cikin jama'a. Genaral ya kalli jama'ar gurin yace" kowa ya tafiyar sa" aikuwa suka watse daga gurin. Ya kalli ma'aikacin dake tsaye a gurin yace." Ka ciro mata takalmin da jakar tunda tana so." Yace." Angama Alhaji." Hakkim tsantsar takaici da b'acin rai yasa ya bar gurin a fusace! Dady ya bishi da kallo yana girgiza kansa. Ladidi ya kalla dake zaune a kasan gurin hannunta dafe da kuncinta sai zumb'ure-zumb'uran baki take yace."gashi nan za'a d'auko miki takalmi ai kina so ko"? Daga kanta tayi ta mik'e tsaye tana buge jikinta General yace." Duk abunda kika gani kina so anan ki fad'a a d'auko miki kar ki kara saka hannu saboda kar kiyi musu b'arna" d'aga kanta tayi, zuwa yanzu itama ta fahimci wautar da ta. tafka, Bayansu ta bi simi-simi duk jikinta yayi sanyi da ganin yanda jama'a suke kallonta wasu na ta b'oye dariyar su wasu kuwa tana kallonsu suna bude wayoyinsu tasan abunda tayi suke dubawa suna dariya kunya duk ta ishe ta taji takaicin zagin da Hakkim yayi mata cikin mutane. Salima ce ta dinga zab'ar mata kaya masu kyau da dogayen riguna gami da undis kayan kwalliya mayafai masu kyau da tsada, tsaf suka kammala Dady ya biya kudi Salima ta fara yunk'urin d'aukar kayan General ya dakatar da ita tare da fad'in" ta kira Abudul a waje." Jiki a sanyaye ta tafi yana zaune cikin mota tace Broth Dady na kiran ka" fuskarsa a murtuke yace." Me zanyi masa dallah Malama kauce ki bani guri" da sauri Salima ta bar gurin, tana komawa tace" Dady gashinan" wani ma'aikacin gurin ya k'araso tare da fadin " Alhaji wannan aikin mu ne" ya fara d'aukar kayan yana futa dasu wajan mota suka biyo bayansa Boot ya bud'e masa yana zubawa General ya kalli Hakkim dake faman d'auke kansa yace." Kaje ka taya shi d'ebo kayan mana" Wani iri yaji a zuciyarsa wai me Dady yake nufi ne? Shi ko General yana sane yake masa haka domin ya k'untata masa ne. A hankali ya futo daga motar ya shiga ciki, su kuma suka shiga motar Hakkim ya dinga futo da kayan yana zubawa a boot zuciyarsa na masa zafi da rad'adi. Sai da sukayi saura sannan ya bar masa ya k'arasa General ya futo da kudi

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39