Skip to content

Chapter 39

Chapter 39

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,140 words 0 views Progress saved
Download Book

yayi bunkice ya samu labarin cewar Sarah tubabbiya ce bazai hana auran ba sanin halin dady nasa Yana da saukin kai da bawa kowa damar za'bar abunda yake so. ****** Yau kwanan Hakkim uku da dawowa kuma tun ranar da abun ya faru bai kara shiga harkar Ladidi ba wani sa'in ko parlor ya shigo ya tadda ita a zaune a futa yake yi saboda Sam baya bukatar abunda zai hadashi da ita, To itama Ladidin nata 'bangaran hakane kwata-kwata idan yana guri bata sake wa a gidan shiyasa duk sanda taji motsinsa a parlor bata futowa har sai ya futa. Yusuf ya dage fa da gaske yake yi shi son Ladidi yake general yasan da maganar haka ma mahaifinsa duk sun San da maganar shi dai general har yanzu bai ce komai ba yana dai kallon yanda Yusuf din yake shige da fuce a gidan da yanda yakewa Ladidi hidima suttura iri-iri wani ma ba na 'kasar bane ga k'atuwar waya ya siya mata. Hakkim kam kallonsa yake yana mamakin sa da irin ibtila'in da yake so ya d'aukowa kansa yarinyar da take da tawagar aljanu a kanta itace zai aura lallai Yusuf yaci kai. Shi kam Yusuf ya matsawa dadynsa dole yazo ya nema masa aure gurin general hakanan yazo a lokacin ne kuma general din yace." Ya bari tukkuna zai je ya nemi izini daga gurin iyayenta domin shima ba a bashi damar ya aurar da ita ba, Mahaifin Yusuf yace." To hakan yayi idan ka tashi tafiya sai muje tare." To da wannan suka rufe maganar. Hakkim yaso ya zuga Yusuf kan ya fasa auran Ladidi a cewar sa tana da girka girkan jinnu watarana yana ji yana gani zasu dame shi. Yusuf Yayi nisa a kaunar Ladidi yace ko bishiyar kuka ce a kanta shi yaji ya gani. Hakkim dariya yake masa yanayi masa kallon Mara hankali. Tunda mahaifin Yusuf yazo wa da dady wannan maganar yasa kansa cikin damuwa tabbas tsakanin Hakkim da Yusuf a gurunsa daya ne amma idan San samu ne shi kam yafi so Hakkim ya auri Ladidi saboda yanda Allah ya zuba masa kaunarta cikin zuciyarsa dole yayi wani abu akan lamarin. *18/12/2019* _BintuUm@rAbb@le_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *πŸ…Ώ45* Salima da Ladidi ne zaune a parlor suna hira lokacin Hjy Asiya tana kicin ita da mai aikinta Hjy Asiya Lemo ta had'a na zob'o tsaf ta kammala ta sanya a frji baito mai aiki ta hau gyara gurin ita kuma ta futo daga kicin din. Ladidi duk jinta take yi a takure a gurin sakamakon shigowar dodon ta Hakkim Wanda yake magana da Salima. Ganin zaman da take gurin bashi da amfani yasa ta mike da sauri zata bar gurin. Cikin bada umarni yace." Ki koma kiyi zaman ki ni futa zanyi ban ga dalilin da zai sanya idan kin ganni a guri sai ki ke damun kanki wannan zai nuna wa mutane cewar kamar wani abun nai miki." Ladidi ta wuce shi kawai ba tare da ta koma ta zauna ba, Salima ya kalla yace." Kin gani ko Yanzu idan dady zai gani zaice nine nake takura mata. Salima tace"Nima fad'an da nake mata kenan cewar ta dinga sakewa da kowa kai din ma yanzu ka gane bata da lafiya duk abunda take yi" Hakkim yace." Ni tuntuni dama na fahimci yarinyar tana da matsala ni kam yanzu babu ruwana da ita bare aljanunta su tashi ace nine." Salima tasa dariya tana fadin"Ni kaina yanzu na daina jin tsoro Wallahi da ne dai nake jin tsuro idan suka tashi." Ta'be bakinsa yayi ya zauna kan kujera tare da fafine"Je ki kawo min abunci yunwa nake ji." Salima ta mike da sauri ta nufi kicin. Ladidi kuwa na cikin dakin zugum tayi kan gado tana tuno fuskar Hakkim yanzu take ganin kyawunsa sosai taji zuciyarta na masa wani irin so cikin zuciyarta tace"Allah yasa dady yace ya aure ni da naji dad'i." Ita kadai take zancan zuci kafin ta kwanta kan bed din tana lumshe ido cike da soyyayr Hakkim din. **** Daddare bayan sun gama dinnar General ya kallesu a nutse yace." Zamuje kano 'kauyan d'an kunkuru zamu je mu dubo su Mai koko bayan haka kuma zan mu nemi izinin daga gurin waliyyin Aminatu." Hakkim yace." Dady Allah ya sanya alkairi ni kam bazan samu zuwa ba." General yace." Dole sai kaje baka da wani uziri da zaka kawo min na yarda dashi." Sunkuyar da kansa yayi yana sakin dariya,Salima da Salim kam murna suke yi zasu je gidan gona, Ladidi kam babu Wanda ya kaita farin ciki sunkuyar da kanta tayi cikin jin dad'i. Hakkim ya dinga mamakin ta sau kusan hudu suna hada ido dashi sai tayi saurin kauda kanta tana sakar masa murmushi abun ya daure masa kai sosai daga k'arshe sai ya fara tunanin ko aljanunta ne zasu motsa tashi yayi daga gurin yana tsaki a zuciyarsa yace." Haka kurrum ki dinga dariya kamar wata shashasha, waje ya futa ya zauna kan wata irin kujera ta huta waya ya futo da ita ya kira Rabin ransa Sarah, Ladidi kuwa haushi taji da ya tashi daga gurin tana jin dadin kallon kyakyawar surarar shi da muryarsa mai dadin sauraro ikon Allah ita kanta mamaki take yi lokaci guda Allah ya Dora mata sonshi da kaunar sa. **** Washe garin ranar suka shirya tsaf harda Yusuf suka tafi *Kano ta dabo timbin giwa kano ko dame kazo an fika!* Tun mota Ladidi take murna da dariya Hakkim nayi mata kallon Mara hankali lokaci lokaci yana jan tsaki mussaman Idan yaga irin rawar jikin da Yusuf yake yi a kanta. Shifa dan dady ya matsa masa ne da babu abunda zai sanya ya hada tafiya da Mara hankali sunan da ya sata mata kenan. Mai koko na zaune a tsakar gida tana sauraron redio kawai Ladidi ta fad'o gidan babu sallama tayi kan Mai koko tana ihu! Iya ta mike zaune da sauri tana murna da farin ciki sai shafa jikinta take tana mutsika idonta fad'i take "Yau wa nake gani a gabana Ladidi na ce ta zama babbar mace kai Alhmdullahi Allah nagode maka Ashe dai zan sake ganin ki Ladidi ta Mai kok...... Kafin Iya ta rufe bakin ta Ladidi ta fad'i a gurin tana turje-turje! sai burgima take yi a tsakar gida wata farar kumfa na futowa daga bakinta, hakan yayi dai-dai da shigowar su Hakkim gidan general yayi kanta da sauri hat suna buga karo da Mai koko wace take ta faman salati da sallalami! Hakkim Yusuf Hajiya Asiya Salima da salim duk suna tsaye suna kallon ikon Allah. *22/12/2019* _BintuUm@rAbb@le_

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39