Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

dace babu ita, ya nufo gida cikin gajiya da sarewa, zuciyarsa ta raya masa yaje ya duba gidan kallo, hanya ya kama yana tafiya yana addu'a a zuciyar sa,, da tafiyar ta ya gane ta,, b'uya yayi sai da tazo ta wuce sannan ya futo ya bi bayanta, abunda yasa ya b'uya shine yasan halinta in ta ganshi tana iya guduwa,, tana shiga soron gidan yana shiga,, ya sanya k'arfi ya k'wade mata k'eya d'ankwalinta ya fad'i kasa, ta rusa ihu! Wannan karon Iya bata hanashi dukanta ba, fad'i take " Kara mata ja'irar yarinya gantalalliya ta tayar mana da hankali" Ladidi ta buga wani uban tsalle ta afka cikin gidan tana kurma ihu!! Kamar Wanda aka kona mata jiki da ruwan zafi,, d'akin Mai koko ta shige ta zura sakata tana ihu! Tun k'arfin ta. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/24, 10:59 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿5* D'alha yace"Gashi kinji daga bakinta ko? can na gano ta ita kad'ai kan hanya tana tafiya ko tsoron dare ba tayi" Mai koko tace"Yanzu dai kayi hakuri mubar maganar sai da safe dare yayi" K'wafa yayi cike da takaici ya yar da abun dukan ya shige d'akinsa. Iya ta sassauta murya tana fad'in"Bude min kofa kinji ko,, bazan bari ya doke ki ba" Ladidi najinta tayi mata shiru,, "Na ce dake ya tafi d'akinsa ki bude min kofa nace ko" Banza tayi mata,, Sauraye sai cizon Iya suke babu abunda take so illa ta kwanta don tayi muguwar gajiya, rarrashin Ladidi take ta bude mata kofa,, k'eme-k'eme tak'i budewa, gyara kwanciyar ta tayi ta lumshe idonta bacci na fuzgarta, tana jin surutun da Mai koko take sam bai dame ta ba,, b'acin rai da takaici suka saka zuciyar Mai koko kamar ta buga gashi ko "yar tabarma babu a tsakar gidan ballantana ta shimfud'a ta kwanta,, ga duhu ga sauro ga danshin ruwa, bata so ta daga murya saboda dare kar D'alha yaji soro ta nufa a hankali ta kwanta kan dogon bainci da masu siyan koko suke zama tana addu'a a zuciyar ta, Allah ya shirya mata Ladidi. *TUSHEN LABARI* *K'auyan d'an kunkuru* k'auye ne dake cikin jahar kano,, ya had'a da Fulani a ciki amma ba sosai ba,, k'auye ne da yake da albarkar gonaki da filaye gami da manya-manyan bishiyun mangwaro ko ta ina,, Malam Labaran manomi ne wanda yake da gona guda d'aya yake noman d'orawa da gero a ciki,, da Abunda ya dogara kenan dashi yake ci da iyalinsa yake sauran bukatu, yana da mata d'aya da yara biyup duk maza, matarshi sunanta Furera, mace mai Neman na kanta tunda aka kawo ta gidan Mijinta take sana'oi iri -iri , domin ta dogara da kanta, dansu na fari sunan shi Aminu yana da lalurar sikila sai Dan uwanshi D'alha shi lafiyan sa lau, abunka da k'auye San basu maida hankali gurin ciwon dansu ba, sai dai in ciwon ya motsa masa suyi masa jike-jike su bashi, Cikin hukunci ubangiji ya mike ya cigaba da rayuwa kana kallo Aminu kasan bashi da koshin lafiya tare suke tafiya gona da mahaifin sa,, ko sunje can ma baya iya aikin koma, D'alha ne me karfi,, Malam Labaran yana da aboki D'an Fulani gurin zuwa kiwo suka hadu dashi,, inda Allah ya had'a jininsu ta kaisu ga had'a yayan su aure Aminu da Amina "yar Dan Fulani itama tana d'auke da irin lalurar Aminu, dake d'an Fulani ma'abocin jin redio ne, ya tab'aji suna fada cewar idan masu irin cutar zasuyi aure su dunga auran jinsu su, nan Labaran ya amunce, ya kuma Sanar da Aminu da Hurera duk suka amunce suna fatan alkairi,, lokacin yayi aka d'aura aure cikin aminci Amina ta tare gidan Mijinta Aminu inda gurinsa yake kewaye da langaga sai dai in zata shiga band'aki take futowa babban tsakar gida,, wata hudu da auran su, ciwon Aminu ya tashi kafin ayi wani yunk'uri ya galabaita mutuk'a jikinsa kamar babu jini ya dashe Tass,, wani makocinsu ya basu shawarar zuwa birni domin a duba shi, to suna cikin shirin tafiya ne, Allah ya amshi Abunsa , mutuwar sa ta girgiza mutane mussaman matarsa Amina tayi kuka har ta gaji " yan uwa na tasaunta tayi hakuri,, bayan sadakar uku kowa ya watse akabar mutan gida da kewar Aminu mutumin K'warai kenan, bayan sadakar ar'ba'in ne aka gano cewar Amina na da ciki, aikuwa Mai koko ta dunga kula da ita sosai har lokacin haihuwa yazo,, inda Amina ta fara zubar da jini abunda ba a so kenan ko mai lafiya balle mai sikila, hankali a tashe aka d'auke ta sai asibitin birni *(Murtala muhamad hospital)* ganin tana cikin halin taimako ne yasa suka shiga da ita dakin operation,, suka ce mijinta ya sa hannu aiki za'ayi mata,, Dan Fulani na kuka da rokon Allah ya sanya hannu Labaran ma ya sanya, to tun kafin a shiga da ita ta rasu,ganin cikin na motsi yasa suka shiga da ita cikin gaggawa aka Ciro yarinya mace, mai kama da uwarta. Cikin halin damuwa nurse ta futo ta sanar dasu halin da ake ciki, sosai suka shiga rud'u da tashin hankali daga bisani suka hak'ura suka barwa Allah, suka karb'i gawar Amina suka tafi domin yi mata suttura, mai koko na rungume da jaririya tana kukan zuciya. ***************** Mai koko ta d'auki son duniya ta Dora shi kan Amina da taci sunan mahaifiyar ta, dama kafin su baro asibitin sun duba ta sosai ko itama tana d'auke da ciwon sikila, Allah mai yadda ya so yarinya lafiyanta Lou sai dai k'ankanta, amma inda ans bata madara me kyau zata murmure. Malam Labaran bai yi shawara da kowa ba yaje ya sanya gonar shi a kasuwa nan take aka samu mai siya kasan cewar gonar tana da kyau kuma tana da fuska akayi ciniki aka bashi kudinsa, ya nufi asibitin cikin gari duk abubun buk'ata ya siyowa Amina ya siyo mata madara masu kyau, da kaya niki-niki ya shigo gidan, Hurera tai yi mamaki sosai nan ya zauna ya warware mata komai, tace"Malam da kayi shawara dani da baza ka siyar da gonar ka ba" yace"Saboda haka shine mafuta asurinmu ya rufu, Kinga madarar nan tana da tsada idan ba haka ba bamu da kud'in siya, kuma ko d'aukar me shayarwa mukayi dole mu biyata, tace"Hakane kuma to Allah ya rufa mana Asiri,, nan Hurera ta kara k'aimi gurin Sana'a har ta kafu da sanar Koko da safe,, shi kuma D'alha yake sana'ar sai da D'ata goba da mangwaro asirinsu na rufuwa,, Dake ranar lahadi aka haifi Amina yasa Mai koko take ce mata Ladidi shikkenan mutane suka rike suma suke kiranta da Ladidiya,, shekararta uku a duniya Allah ya amshi ran Malam Labaran ciwon kai tafarar daya,, Mai koko nauyi ya kara yi mata yawa, dake jaruma ce, sam bata karaya ba, ta cigaba da neman kud'inta, da kanta ta kai Ladidi makarantar allo tun tana da shekaru hudu,, tana zuwa cikin yara zaka ji gurin ya kaure da kuka Ladidi Duk ta

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39