Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,233 words 0 views Progress saved
Download Book

doke su, har wad'anda suka girme ta dokansu take,,Malami ya doke ta tayi masa Allah ya Isa,aikuwa ya dawo wa da mai koko ita yace"Tana hana su karatu in taje dokan yara kawai takeyi ta hanasu karatu gashi in an doke ta tayi Allah ya Isa shi kam bazai iya ba" Mai koko tace"Kaje ai ba kai kadai bane me makaranta na kai ta wata, sai da akayi wata shida tukkuna sannan ta kaita wata makarantar nan ma bata canza zani ba,, tana zuwa makarantar karatun yara ya lalace domin duk gurinta suke komawa suyi ta wasa duk tsawan da malam zai musu basa jinsa. Nan ya fahimci zuwan Ladidi ne jawo haka, tunda da yana iya tankwara su, aikuwa sai ya ware ta a cikinsu in tayi futina yaci ubanta, ita kuma ta zage shi, gashi duk dukan da za'ai mata bata kuka sai dai idonta yayi ja, malam da yaga ba zai iya ba ya tattarata ya mayarwa da mai koko ita,, abunda ta fadawa malamin farko haka ta fada masa,, shekara guda bata zuwa makaranta, sai wasa da yawo kusfa-kusfa D'alha bai tab'a Ankara ba, dake da wuri yake futa baya dawowa sai gab da magariba, ya dawo ya wuce ta makarantar Allo yaga an tashi yana ta daga kai yaga ta inda Ladidi zata b'ullo bai ganta ba, sai yayi tunanin ko ta tafi gida, yana tafiya ya hangota kan katangar wani gida ta mike tsaye tana ta tafiya tana k'yalkyala dariya kanta babu d'ankwali, sai diddigagen gashinta da kwarkwata ta cinye rabi ta bar rabi, duk k'wanta nan burjik!! Kira ya kwala mata"Ladidi"!! Da sauri ta juyo jin muryar Kawunta ta hantsilo k'asa ko a jikinta ta mike da gudu tayi gida,,, girgiza kai yayi ya bi bayan ta. Sosai ya dunga fad'a Mai koko tace"Ai sai ka d'auke ta ta kaita da kanka ko wace makaranta aka kai ta sai su koro ta saboda tsabar bakin ciki sun tsani marainiyar Allah" Yace"Halin ta ne ya jamata zan kai ta, wata makatanar da kaina Wallahi da kaina zan dunga hukunta ta" Shiru mai koko tayi masa ya gaji ya shiru, ita ko Ladidi na bayan ta tana zumb'ura baki gami harare-harare ta tsane shi tunda kullum cikin takura mata yake. Washe gari da safe D'alha ya sa ta a gaba suka nufi makaranta ya damk'a ta a hannun Malam yace"Gatanan yayi mata hukunci in tayi laifi, kuma ya kula da karatun ta." *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/24, 10:29 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*KU SONI TA ZARCE💝💝💝 NIMA NA NASO KU TA ZARCE❣❣❣IN HAR KUKA KUFCE! 😡😡A KANKU NI ZAUCE! 🤢 IN KUNJI😍😍*_ 😃😃😃😃😄😄😄😃 I will always saying thank you to my people love you so much,, muna tare insha Allah😘 *🅿6* D'alha ya kama hanya yai tafiyar sa, gurin sana'ar sa, tunda malam yayi mata gurin zama cikin yara take ta faman zabga masa harara sosai yayi mamakin yarinyar ko da yake dama yana da labarin ta sosai,, sai ya d'auke kansa kawai yayi kamar bai ganta ba,, ya cigaba da koyar da yara, yarinyar dake kusa da ita ta zura hannu ta mintsina yarinyar ta fashe da kuka, Sai tayi saurin cire hannunta tana kallonsa yana kallonta,, ya gane itace yarinyar ya kira da hannunsa, gurin zama yayi mata,, Ladidi taji haushin haka, tayi shiru tana zumb'ura baki, lokacin tashi nayi yayi musu addu'a duk suka mike sai ta d'auki takalmi wata ta b'oye, to yaga lokacin da ta d'auka, murmushi yayi ya kira yarinyar ganin tana kuka, Ladidi ya kira, taje tai masa k'erere aka yace"Bata takalmin ta" Zumb'ura baki tayi tace"Baya gurina fa" "Naga fa sanda kika d'auka kika b'oye bata kinji ko,, ni nasan kyautar da zanyi miki" Shiru tayi yace"Zan baki alawa" Aikuwa sai ta futo da takalmi da ta b'oye kasan zaninta ta jefawa yarinyar, da sauri ta d'auka ta sa, ta kalle shi, kai tsaye tace"Bani alawar" yace"Dama ba karatu kika zo ba" ? Daga kai tayi" yayi murmushi yace"To don Allah kiyi karatu ki nutsu kinga Kawun ki ya kawo ki kiyi karatu nayi miki alk'awarin bazan Doke ki ba kamar yarda ya fad'a" baki ta tura tace"Ko ka dake ni ba zafi zanji ba" dariya yasa yace"Nasan da haka ai,, shiyasa ma bazan tayar da hankalina ba". "Ni dai bani alawa ta" fad'a tana Sosa kanta,, Hannu ya zura cikin aljihun sa ya ciro Alawa guda biyu yace"Kullum nayi miki alk'awari zan dunga baki mutuk'ar zakiyi karatu in kin zo makaranta kuma zaki nuttsu ki daina tsokanar "yan uwan ki" Karb'ar Alawar tayi tayi tafiyar ta, ta barshi da baki a sake, girgiza kai yayi ya d'auki allon nata yana dubawa, duk girman ta, tana Alam tarakaifa. Wanda basu kai shekara goma ba ma sun shiga sabbi,, ita tana zaune, haka kawai yake tausayin yarinyar, yana fa yara guda biyar duk kamarta shiyasa in yaga yara na k'uruciya yake musu addu'ar shiriya Wannan shine silar zaman Ladidi a makaranta ko tayi nufin tsokona ko gudun makaranta sai ta fasa saboda alk'awarin alawar da Malam Salihu yayi mata, shi kuma kullum baya fashi, ana tashe zai bata,, gashi Yanzu tayi nisa a karatu ta kusa izu d'aya. Babu laifi tana gane wa. *WANNAN SHINE TOSHEN LABARI* Da Asubah D'alha ya futo da niyar zuwa massalaci, da cocilan a hannunsa yana haskawa, sai ya ga Mai koko na k'okarin saukowa daga bainci da alama itama tashin ta kenan, Cikin mamaki ya tsaya yana kallonta yace"Iya me kike anan"? Shiru tayi masa ta mike tana Sosa jikinta, yace"Da alama nan kika kwana meye dalili"? Cikin b'acin rai tace"Wannan ja'irar yarinyar ce ta rufe min k'ofa jiya babu yadda banyi ba ta bude min amma tak'i"D'alha mamaki sosai yake yace"Tak'i bude miki k'ofa me makon ki min magana shine zaki kwanta a soro cikin sauro Iya sai kinje zazzab'in cizon sauro ya kama ki"? K'okarin shiga cikin gidan take tana fad'in"Kai dai magana ta wuce, ai kayi tafiyar ka" Gyad'a kai kawai yayi ya wuce yana mamakin son da Iya takewa Ladidi wannan son shi a ganinshi cutar wa ne, domin shi yake k'ara lalata yarinyar. Har yaje massalaci yan sak'e-sak'en hukuncin da zai d'auka kan Ladidi domin ko me Iya zatayi sai ya doke ta ya rantse. Bayan an idar da sallah sun futo,, Halliru mai Fura ya tsaida shi suka gaisa,gani yayi Halliru na sha masa kunu yace"Malam Halliru lafiya ko" ? Halliru ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in"Idan kaji kira daga mai gari kar kayi mamaki" Cikin mamaki D'alha yace"Me ya faru" Rai a b'ace Halliru ya kwashe duk abunda ya faru ya fad'a masa,, innalillahi wa'innailahi raji'un shine abunda D'alha yake ta Nanatawa yace"Don girman Allah Halliru kayi hak'uri wallahi in banda ka fada min ban san abunda yake faruwa ba, itama Iya ina tabbatar maka da cewar bata sani ba kayi hakuri don Allah kar ta kaimu ga zuwa gurin mai gari, wannan tonan asiri ne" Halliru ya sha kunu yace"Inyi hakuri kamar yaya? Kana nufin in

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39