Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
Download Book

iri-iri ne akwai masu taimako akwai kuma mugwaye ya lura wadanda suke kan Yarinyar mugwaye ne sosai ta bashi tausayi ganin yanda duk hallitun ta suka jirkice Malam na rike hannun ta guda ta nitsu ta daina abunda take yi. Addu'a ya fara tofa mata a jikinta da fuskarta tsawon minti ashirin suka ji wata irin murya na magana. "Ka bari! Bama so kana takura mana damu da jaririyar muuuuu."! Malam yayi gyaran murya ya fara magana kamar haka. "Kunce bakwa so ayi muku addu'a kuma kun'ki ku rabuda yarinyar nan ta samu Lafiya yanzu me ya kawo Ku ko kuma kun manta da al'kawarin da kuka daukar min na cewar zaku k'yale Yarinyar nan tayi rayuwar ta kamar yanda kowa yake yi." Cikin sha'kakkiyar murya suka ji ance "Mu ba laifin mu bane ga mai laifi can."! Duk suka juya suna kallo Hakkim dake tsaye bakin 'kofa yana cike da mamaki ana magana da Aljani a cikin gidansu lallai dady ya dauko wa kanshi masifa. Malam yace." Dole kuyi hakuri dashi tunda yayanta ne kuma Dan gida ne don dai baya gari ne kwana biyu Idan kuma kunki hak'ura tom ni zan 'kona Ku komai yawan Ku baku fi k'arfin ayar Allah ba." Wani irin siririn kuka suka ji ladidi tana yi tana sha'kewa sannan suka ji wata irin murya ba irin ta d'azu ba tana magana kamar haka "Kada ko 'kona mu domin mune garkuwa a jikinta mu musulmi ne kuma muna tsare ta daga sharrin jinshi mu masu cutarwa muna so kujawa Jariri kunne ya futa daga sabgarmu da ta jariryarmu domin kullum muna kusa da ita muna bibiyar lamuranta shiga hankalin sa damu babu ruwan sa damu."!!! Malam yace." Kuma babu ruwan Ku dashi kuma kar Wanda ya sake ya ya kulla masa wani sharrin a cikin wallahi sai na 'kone shi kurmus! Shiru na tsawon minti biyar babu Wanda yace komai Ladidi suka gani ta fad'i a gurin rigib! Bacci mai nauyi ya dauke ta! Malam ya mike tsaye yana kallon general da yake kallon Ladidi cike da tsananin kauna da tausayin ta, hak'ika da yana da yanda zai yi da ya cire mata wad'annan kafuran aljanun da suka dame ta suke wahalar da ita gami da hanata sakewa sosai yake tausayawa Yarinyar a rayuwar sa. Malam yace." Yana da kyau Ku kula kuma ku kiyaye abunda zai bata mata rai mussaman kai." Yafad'a yana kallon Hakkim dake tsaye bakin kofa yana mamakin al'amarin. Ya cigaba da cewa"Kaji 'korafin su akanka yake don haka ka kiyaye abunda zai sa su kusanto jikin yarinyar har ta kaisu ga bata wahala irin wannan domin ni daku Duk mun san cewa Jinnu ba karya bane kuma wadanda suke jikin yarinyar manya ne yana da kyau a kiyaye 'bata mata rai ko kuma ayi mata abunda bata so insha Allah ni nayi alk'awarin duk sai na rabata da mugwayen cikinsu da izinin Allah." General yace." Insha Allah za'a kiyaye kuma dama ta kwana biyu basu matsoba wannan ma tsautsayi ubangiji Allah yayi mana tsari dafa sharrin su." Malam yace." Ameen yana kokarin tafiya ne general ya Ciro kudi masu yawa ya bashi da kyar ya karba yana fadin"Shi ba don kudi yake taimakon yarinyar ba kwai yanayi ne don Allah. General din yace." Shima ya sani kyauta akwai ya bashi, cike da girmama juna suka yi sallama. Sosai general yayi wa Hakkim fada kan ya futa daga sabgar Ladidi ko don gudun abunda ka iya zuwa ya dawo, to shima Hakkim din nashi 'bangaran ya fahimci komai kuma yanzu ya gane cewar duk abunda Ladidi take yi ba yin kanta bane junnu ke sata yayi alk'awarin futa sabgar ta har abada tunda dai shi dady din yaji ya gani zai riketa a haka Shikkenan Allah ya taya shi rik'o. Ladidi bata farka daga bacci ba sai kusan daf da magariba sannan ta farka jikinta duk ya mutu ko ina nayi mata tsami tunda taji ta farka da mugun ciwon kai tasan tayi iska!!! Tana share hawaye ta mike ya shige d'akinta Wanda aka mallaka mata a gidan, zama tayi gefan gado tana kuka domin itama har ga Allah ta tsani wannam abunda take yi don dai babu yanda zata yi ne addu'a take cikin ranta Akan Allah ya yaye mata. Ko da Hjy Asiya ta futo daga daki taga babu ladidi a parlor nan ta fahimci ta farka daga bacci kicin ta shihe kawai tana girgiza kanta gefe guda Kuma tana tausayawa yarinyar da irin tata kaddarar. Ladidi kuwa ruwa ta hada mai zafi tayi wanka duk Dan taji dadin jikinta ta fito daure da alwala ta shirya tsaf ta futo parlor lokacin babu kowa sai ta zauna kan kujera tana jiran kira sallah magariba Salim ne ya shigo parlor ya ganta ita kadai yace"Menna 'yan mata ta gidan Yusuf bada kanki a sare." Hararasa tayi ta dauke kanta shi kuma yasa dariya yana fadi'n komai abunki Yusuf zaki aura." Ita dai shiru tayi masa shi kuma ya shigeta yana cigaba da tsokanar ta har Hjy Asiya ta futo daga kicin. Tace"Sarki tsokana kazo zaka dame ta ko."? Yace." Shigowa ta. kenan wallahi Mama yau ina Salima take ne tun safe ban ganta ba." Hjy Asiya tace"Ta yini gidansu kawarta amma dai yanzu tace min tana kan hanya." Hakkim ne ya shigo parlor yana sanye da JS a jikinsa sunyi masa kyau sosai ya taje Lafiya yar suman kansa Salim yace"Yauwa broh zo ka bani tsaraba ta da kayi min alk'awari." Hararasa Hakkim Yayi har ya 'karaso tsakiyar parlor ganin Ladidi a zaune sai juya daining ya nufa yana ya mutse fuska. *16/12/2019* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *πŸ…Ώ44* Zama yayi kan kujerar daining Hjy Asiya ta futo daga kicin ta ganshi fuska ta saki a nutse tace "Dama yanzu nake shirin aikawa a kira ka domin d'azu naga ba wani abincin kirki kaci ba." Murmushi yayi a hankali yace."Ni kam na koshi mama kar ki ce sai naci wani abunci yanzu cikina zai fashe." A shagwabe ya fad'i maganar. Ladidi dake zaune a can parlor tana jinsu tab'e bakinta tayi tana mamakin sa gotai gotai dashi yana shagwaba a ganinta shirme ne. Hajiya Asiya tace"To Shikkenan bazan matsaba maka ba ai cikin Kane yanzu dai bani labarin domin dai tun d'azu nake tsumayin ka." Hakkim ya lumshe idonsa da ya tuno da Sarah yace." Mama nayi budurwa fa kuma insha Allah ita zan aura domin na yaba da d'abi'unta." General ne ya karaso gurin Hajiya Asiya tace"Yawwa ga dady nan ayi maganar dashi amma dai gaskiya naji dadin wannan al'amari.' General yaji duk abunda suke tattaunawa amma bai ce musu komai ba cin abincin sa kurrum yake. Hajiya Asiya tace"Dady kanajin mu fa da Hakkim ka'ki cewa komai." A nutse yace." Allah ya sanya alkairi Abdul girma yazo." Dariya hakkim yayi yace."Dady da wuri fa nake so ayi komai a gama." General yace." Ai babu matsala ni Zan sanya ayi min bunkice kan Yarinyar Allah ya kaimu lokacin." Hakkim yaji dadin hadin kan da ya samu gurin mahaifin nasa ya San kuma ko da

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39