Chapter 27
Chapter 27
gashi." Salima tace." Aikuwa naga alama gashinan ai.yanzu ungo wannan kayan ki sanya a jikin ki sai kizo muje farlo." Ladidi ta kalli kayan da Salima ta mik'a mata, ta sanya hannu ta karb'a da fuskarta da murmushi tace." Ina son mai sona nagode sosai wallahi ina son babanku." Salima tace." Dady ya gode, ai mu 'yan gidanan haka muke ba yabon kai ba duk Wanda ya zauna damu sai yaji yana son mu." Ladidi ta mike tsaye tana k'okarin saka kaya tace." Amma banda mutum daya a cikinku na tsane shi wallahi." Salima tace." Wai kina nufi Yaya Hakkim."? D'aga kai tayi tana saka riga a jikinta, Salima tasan dalilin da yasa tace haka sai ta basar da maganar kawai. Tace "baki saka vest a ciki ba." "K'yaleni haka wannan shimin takura min take." Ladidi ta fada tana zura siket a jikinta sosai Riga da siket na atamfa Ghana suka yi mata kyau tamkar an gwada jikinta kasan cewar Salima itama bata da wani jikin kirki bayan haka kuma bata da tsayi sosai ga yanayin dinkin 'yan matan abuja a matse shiyasa kayanta suka yiwa Ladidi cif. Tare suka futa farlo Ladidi sai hardewa takeyi na rashin sabo saboda siket din ya dame mata cinye sosai yanayin rigar yasa k'irgar danginta suka futo currr! Kamar gobar da bata gama nuna ba. Lokacin da suka futo Hakkim ya shigo yana zaune cikin kujera yana cin magani duk yak'i kula kowa. Ladidi na gano shi ta zabga masa harara tana zumb'ura baki sosai ta tsane shi.Hajiya Asiya ta d'an d'aga muryar ta yanda Ladidi zata ji sosai tace." Iyee! Aminatu ashe haka kike da kyau bafulatana dake, kin ga yanda kikayi kyau kuwa zo nan 'yata." Ladidi ta washe bakinta ba tun yau ba take son taga ana cewa tana da kyau da sauri ta je gurin Hajiya Asiya sai wata dariya take ta shashanci. Salim da Yusuf sai b'oye dariya suke kar suyi ransu ya b'aci gurin Dady Dan ma baya gurin. Ta zauna kusa da ita tace." Hajiya da gaske kike ni me kyau ce hehehehe."! Ta kyalkyale da dariya. Hajiya Asiya tace." Sosai kuwa wallahi son kowa kin wanda ya rasa." Dariya su Yusuf ce ta dawo da hankalinta Kansu ta daina dariyar haukan da takeyi ta kalli Hajiya cike da b'acin rai tace " kin ga sunayi min dariya ko.'' Rai a bace Hajiya Asiya tace." Wallahi duk Wanda ya kara yi mata dariya nan gurin ransa zai b'aci." Shiru sukayi dukaninsu Ladidi ta b'ata rai sosai tana tabkawa Hakkim harara shida bai ko kalli inda take ba A Karaf! Suka had'a ido dashi yana kishingid'e cikin kujera da airpic a kunne shi,zare mata ido yayi sosai wai taji tsoran shi,aikuwa itama ta zare masa nata tana zabga masa k'atuwar harara tare da murgud'a bakinta. Cike da mamaki ya yunk'ura ya tashi sosai yana kallonta itama ta kafe shi da idonta kwala-kwala, tsaki! Yaja me sauti k'asa-k'asa yace." Yarinya ita ba mutum ba ba aljan ba ba mayya ba dubi wasu ido kamar daffafiyar gurjiya." Babu Wanda yaji abunda yace a farlo saboda surutun da suke yi Hajiya Asiya ma nacan tana saka musu baki. Ladidi duk taji abunda yace da ita. Tayi k'wafa had'e da girgiza kanta itama a hankali tace." Dube shi wai shi Dan burni da hanci sai kace na butorami. Hahahahahahaha"!!! Ta shek'e da mahaukaciyar dariya. Duk suka juyo suna kallonta cike da mamaki sosai Hajiya Asiya tace." Aminatu Lafiyar ki k'alau kike dariya haka."? Bata fasa dariyar ba ta nuna mata tv da hannunta Hajiya Asiya ta kalli TV sai ga mage da b'era suna gudu sun sato nama a kicin din wata mata." Dariya tayi kawai tace." Aminatu kenan. Salim da Yusuf kuwa kus-kus suke DOMIN suna ganin al'amarin yarinyar kamar da almutsutsai a ciki. Gogan Ku kuwa, cikin zafin zuciya ya mik'e tsaye yana wani irin huci yayi ball da k'afafunta dake kan hanya y ma fuce yana Jan wani mutsiyacin tsaki!! Mtssssssss!! Kallo suka bishi dashi cike da mamaki.Ladidi ta cigaba da sheka dariyar ta har ya futa waje yana jinta. Zama yayi cikin wata rumfa yana sak'e-sak'e yau d'in nan zai bar garin nan. Domin zuciyarsa zata iya bundiga in yana kallon mummunar fuskar yarinyar nan me kama da Aljanu. *17/October/2009* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿28* *Saturday* *19/October/ 2009* ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ Girgiza kai kurum Hajiya Asiya tayi saboda tasan halin bak'ar zuciyar yaron nata, shiyasa basa shiri da Dadynsu wani lokacin saboda baud'ad'an ra'ayinsa, wanda shima General din ba baya bane gurin baud'ewa kusan ma shi Hakkim din ya gado. Ladidi kuwa gyara zama tayi tana kallon ta sai dariya take shekewa tun abun na basu mamaki yazo ya daina basu suka cigaba da hirarrsu nan General din ya sauko daga sama ya same su,ya shirya tsaf da shi cikin manya kaya ya kalli Ladidi yana murmushi yace." Aminatu kallo kike ne."? Cike da farin ciki tace." Eh Baba." Yace." Da kyau yanzu abunda za'ayi shine ki aje kallon muje mu dawo kin jiko." Ladidi tace." To Baba" Mik'ewa tayi idonta akan tv ta kasa daukewa." Hjy Asiya tace." Kuje Ku dawo ai yananan yana jiran ki." Dariya tayi kamar wata shashasha ta bi bayansu General tana waiwayen tv Su Yusuf kallonta kawai suke cike da mamaki.! Buge kanta tayi garin waige ta dafe gushin tana sakin ihu!! Duk suka maida hankalinsu kanta Hjy Asiya tace." Aminatu ho!! ki rage wannan k'auyancin naki don Allah." Ladidi ta fuce tana zumb'ura baki. Tana futa Yusuf da Salim suka kwashe da dariya dama saboda kar suyi a gabanta ne ta fadawa Dady Hjy Asiya itama tasa dariyar tana ta yasu. Yana zaune gurin hutarwar ya hangi futowar su, tun daga nesa yake k'arewa yarinyar kallo zuciyarsa na sak'a masa abubuwa da yawa a kanta, sosai yake jin zafin abunda tayi mishi farkon zuwan shi gidan. Yana jin wani irin haushin ta gami da k'yamarta domin shi ramar ta ma tsoro take bashi yarinya sai kace muciya sai kai da uban ido kwala-kwala jiki duk jijiya. Saurin d'auke kansa yayi da yaga Dady ya d'ago kansa yana dube-dube aikuwa karaf ya hango shi zaune. Daga murya yayi tare da kiran sunan shi. Ya amsa cike da ladabi ya taso. Ladidi na tsaye hannuta rike da murfin mota ta dinga banka masa harara tana ya mutse fuska duk cikin'yayan General shi kadai ta tsana tunda baya kaunar ta. Cike da bada umarni General yace." Ka shiga ka tuk'a mu zamu shiga kasuwa yanzu." Sunkyar da kansa kasa yayi yana sosa kai kamar munafuki yace." Dady da ina so in koma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39