Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

daga gurin. Da sauri ya sake ta ta fad'i kasan gurin ya mik'e da sauri yana duba jikinsa. Saboda fargabar da suke ciki babu Wanda ya damu da fad'uwarta a gurin itama bata damuba ta mik'e zumbur tana sharb'e hawayen fuskar ta. General ya k'araso kusa da ita cikin taushin harshe yace." Yi hakuri kinji Aminatu kinga ni ai na fada miki ba allura za ai miki ba kin tashi hankalin ki da namu kiyi shiru ki fada min me kike so in siya miki." Ya k'arashe maganar sa lokacin da suke zama kujerar dake fuskantar ta dactor. Tsabar takaici da b'acin rai yasa Hakkim kasa cewa komai ya bude kofa ya futa a fusace.!! Dactor ya gama rubuce-rubucen sa ya d'ago yana kallon General yace." Alhaji gaskiya ta samu matsala daga kunnen ta na hagu, Wanda ya dumd'e ba taji sosai ta bangaran sa,amma insha Allahu in an bi doka zai dawo dai-dai yanzu zan dorata kan magani kuma kullum za'a dunga kawo ta ana mata wankin kunnen tsahon sati uku, insha Allahu idan akayi haka za'a samu maslaha." General ya d'aga kansa cike da takaici yake Neman Hakkim a gurin sai ga babu shi girgiza kai yayi ya maida kallonsa gurin Dactor yace." Babu damuwa dactor INA so ka tsaya min kan yarinyar nan domin bana so ta rasa wani Abu me muhimmamci a rayuwar ta mussaman ma kunne domin jikin dan Adam yana da muhimamci duk abunda ake buk'ata zan biya insha Allahu a kula min da ita." Dactor yace." Insha Allahu za muyi iya iyawar mu Matsalar daga yarinyar ne Allah yasa ta bamu hadin kai." General yace." Insha Allahu babu Matsala." Dactor ya mik'e tsaye yace." Muje pharmacy zan had'a mata magani gobe misalin takwas na safe sai a kawo ta domi fara yi mata wankin kunne." Duk suka mik'e suka futa a reception suka zauna Dactor shi da wata nurse suka nufi dakin magana. General ya dinga laluben inda Hakkim yake bai ganshi ba Yusuf ya kalla da fuska a daure yace." Ina Hakkim yake.? Kai a sunkuye Yusuf yace." Ya tafi sanjo kaya." Cike da mamaki General yace." Kamar yaya ya tafi sanjo kaya wato yana nufin mu tsaya jiran shi ya tafi da mota sai sanda ya ga damar dawowa ko me.? K'asa da kai Yusuf yayi cike da girmamawa. General yace." Ya kyauta ai." Suna zaune Dactor ya dawo hannunsa rike da Leda me tambari da sunan hospital din nasu cike da mugunguna nasha dana digawa a kunne dactor ya mik'awa General yana fad'a masa yanda za'ayi amfani dasu. Nan General ya karb'i numbar account ni dactor din domin ya turo musu da hakkin su sukayi sallama suka futa. Hakkim ne ya shigo asibitin cikin mota General ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Kayiwa kanka k'iyamun laili wallahi da ka bari mun bi motar haya sai na b'ata maka rai." Shiru yayi yana sunkuyar da kai kasa ya sanjo kaya yanzu yana sanye da wata lafiyyyare shadda geznar sai maiko take brown ce babu hula kanshi sai sumar shi tasha gyara da alamu sai da ya sake sabon Wanka kafin ya dawo. General da kansa ya budewa Ladidi kofar ta shiga su Iya da D'alha suka shiga sannan ya shiga, Yusuf ya zauna kusa da Hakkim ya ja motar Dady na d'agawa Dactor hannu. General ya zurfafa a tunanin yaya za'ayi wannan bayin Allah su yarda da shawarar da ya yanke kan Ladidi, zuciyarsa a dake ya kalli Mai koko da tayi tsumu! Cikin hijabi tana shan Ac mota sai zare ido take yace." Iya akwai shawarar da na yanke kan Aminatu. " Mai koko ta kalle shi tace." To Alaji ai babu komai ka fada min naji ai kana da kirki kai kam ko ajikin masu kud'in samun kamar ka sai an tona lallai albasa batayi halin ruwa ba wancan yaron naka me zuciyar kafurai da rashin imani." Tafad'a tana hararar Hakkim dake driving Takaici kamar ya kashe D'alha Ji Iya da wata magana don Allah ya juyo yana kifta mata ido Iya ko ganewa ba tayi ba ta cigaba da surutun ta daga ni tana cike da jin haushin Hakkim din. Sai da General ya Bari ta gama surutun nata sannan yace." Dama cewa nayi me zai hana Aminatu ta dawo hannuna saboda shan maganin ta kan k'aida idan yaso idan lokacin da dactor din ya d'iba ya cika sai ta dawo gurin ki ko yaya kike CE." General ya karashe maganar a tausashe domin ya lura tsohuwar yar taratsatsi ce. Mai koko ta kalli General baki na rawa tace." Me kake cewa Alhaji."!!!!!!? *Inga ruwan comment da dogon sharhi kan book din nan idan ba haka ba tammm! Zan mai dashi........ Ba sai na fada ba kun San sauran ehe, ko ta ina ina ga ruwan comment na zuba Lol😄* *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿26* General yace." Iya cewa nayi ki bar min Aminatu a hannuna domin tafi jin dadin karb'ar magani cikin nutsuwa kinga lalurar tata tana buk'atar hakan ,zamu zauna da ita a gidana na nan garin tsawon lokacin da dactor din ya fad'a insha Allahu komai zai yi dai-dai." Girgiza kai Mai koko tayi tace." Ayyo! yanzu na fahimci inda ka dosa Alaji, ni kam ban amunce ba domin bazan iya baku ladidi ba ta zauna tare da wanda yayi yunk'urin nakasta ta." General yace." Maganar ki haka take Iya amma wannan karon ina me tabbatar miki da cewar idan Hakkim ya kuskura hannunsa ya sauka kan Aminatu da sunan duka to babu shakka zan dauki k'wak'warar mataki kansa." Girgiza kai Iya tayi tace." Oh!-oh! Ni kam ban yarda ba Alaji kawai ka bamu magani ai naga lokacin da likita ya ke nuna maka yanda za'ayi amfani dashi sai in dinga bata." Shiru motor tayi kowa na tunani a zuciyarsa hak'ika General bai ji dadin rashin amincewar Iya ba. D'alha ya juyu a nutse yana kallon General yace." Allah kada ranka ya b'aci kan hakan hak'ika nasan zuciyarka daya ka fad'i haka za mu baka Ladidi kamar yanda ka buk'ata tunda ba nisa zakuyi da ita ba kuna cikin garin nan sai in dinga kawo Iya tana ganinta kullum ina ganin haka yayi ko."? General yace." Haka yayi samari naji dad'i kuma daka fahimce ni sosai da sosai." Iya ta kalli D'alha cike da takaici gani tayi fuskarsa a murtuke sai tayi shiru bata kara cewa komai ba sam bata son b'acin ransa kasamcewar shi kadai ne da ita a halin yanzu. Cike da mamaki suka ga motar ta tsaya gidan gonar dasu ke hira a kwanaki,

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39