Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

_______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿9* Kawu D'alha yace"A'a Iya ba duka masu kud'in suke da Wannan halin ba, wallahi akwai masu kirki da taimakon jama'a" "Gaskiyar ka,, akwai sosoi" Mai koko tafad'a haka dai suka cigaba da hira kafin aka kira sallahr magariba D'alha ya nufi massalaci, Ladidi take tai wa magana tayi mata banza sai shek'ar kuka take,, itama sai ta k'yaleta kawai ta dauro Alwala domin yin sallah. ********* Monday, 12:00pm jirgin su Abdul Hakkim ya sauka,, Dady da Salim da Salima sai ware ido suke suna jiran suga futowar sa,, A hankali ya dunga saukowa, kana kallonsa kasan yana cikin farin ciki,k'ayataccan murmushi ne d'auke a kyakykyawar fuskarsa mai cike da kyau da kwarjini gami da nutsuwa,, yana sanye da suit Wanda sukayi masa bala'in kyau, k'afar shi sanye da rufaffan takalmi blck sai shaining yake,, kunnen shi mak'ale da eir pix,, hannunsa guda k'atuwar wayar sa ce, d'ayan kuma trolly d'insa ce yana jan ta, Salima ta rugu da gudu, tun kafin ta k'araso ya maida wayar aljuhu, ya bude hannunwan sa,, rungume juna sukayi, dariya take tana yi masa barka da zuwa,, da murmushi a fuskarsa yake amsawa yana d'an dukan bayanta, Salim ya k'araso gurin cikin farin ciki yace"Broth barka sannu da zuwa, trolly din ya k'arba daga hannunsa, Hakkim ya dafa kansa yana fad'in"Broth na dawo lafiya ammafa na zo da sabuwar reza sai na aske wannan gashin naka da yayi tozo a tsakiyar ka,, bakaji broth na hana ka irin wannan aski na "yan iska"" Salim yasa dariya yana fad'in"Humm Babban yaya kaima fa irin sa ne a kanka" Dokan kansa yayi yace"A'ina ya zama ina naka,, nawa daban naka daban" 'yar dariya Salim yasa yana Sosa kai, haka suka k'arasa bakin mota inda Dady yake tsaye yana sakin wani kyatattacen murmushi ganin yadda iyalinsa suke so da kaunar junan su,, rungume juna sukayi Hakkim yace"Dady na same ku lafiya"? "Lafiya alhamdullahi sai dai munyi kewar ka, da sa idon ka" Dariya yasa yace"Gani na dawo zan d'ora inda na tsaya mutukar naga ba dai-dai ba""" Dady yace"Ai naga alama gashinan har kafara wa Salim k'orafi" dariya sukayi gaba d'anyan su, suka bude mota suka shiga,, Direba yaja suka tafi. ******** Kwanuka da kofuna ne a jere, tun daga cikin gidan har zuwa soro, kowa naso layi yazo kanshi, har da maza a tsatstsaye a waje suna jira a mik'o musu, yawancin su masu wuce wa ne,, shine take d'aura musu a Leda,, duk wannan aikin ita kad'ai takeyi tayi-tayi da Ladidi ta futo ta taya ta tak'i dake yau alhamis babu makaranta, tana cikin daki tana jin haushi, saboda ko yau da safe sai da Kawunta ya kara maganar aske mata gashi, shine take gaba da Mai koko tak'i kula ta,, hayaniyar yara ce tayi yawa kowa yana ganin kamar za'ayi masa zure,,, da sauri ta bankad'a labule ta futo, fud'um-fud'um, kai tsaye hanyar futa ta nufa,, Sam Iya ba taga futuwar ta ba dake ta juya baya,, tana zuwa inda jerin kwanunkan suke, sai ta fara d'ebo na k'arshe tana mai dasu gaba, na gaba ta dawo dasu baya,, ta hargitsa layi,, Iliya yana tsaye yaga kofunsa ya dawo baya yace"Ke Ladidi mayar min dashi inda yake sai da kika ga an kusa zuwa kaina zaki hargitsa layi" kai tsaye tace"Bazan mayar ba" ruk'e k'ugu tayi tana kallonsa,, a zuciye ya nufi inda kofunsa yake yaje ya dawo dashi inda yake,, aikuwa bai gama ajiye shi ba,, ta d'auka tayi wurgi dashi waje,, takaici yasa Iliya kai mata duka, itama ta kai masa,, kafin kace kwabo fad'a ya rincab'e a tsakaninsu,, wata yarinya ce ta futo hannunta d'auke da kwano Wanda yake cike da koko sai turiri yake,an sallame ta,, babu zato Ladidi ta ingiji ta kokon ya kife a jikinta, yarinyar ta kurma ihu!!!"Wayyo Allah na""" Iya ta saki ludayin hannunta da sauri ta nufi soro,, Me zata gani, Ladidi da Iliya ne suke kokawa katitir! Duk da Iliya yake namiji wanda ya girmi Ladidi da shekaru kusan biyar, ya kasa yin galaba a kanta, duka take kai masa ta ko ina tana k'okarin tad'o k'afarsa da tata k'afar, in ka kalleta a lokaci sai ka rantse da Allah ba Ita bace, duk kamaninta sun sauya,sai naushi take kai masa tana cakumar sa,, Mai koko ta rasa gurin wanda zata nufa,, ga Aminoni tana Ihu!!! Koko ya k'ona ta,, ga Ladidiya can tana d'aban albarka. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/27, 5:17 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _ALHERIN ALLAH YAZO INDA KIKE_ *NANA AISHATU KADUNA* _Hak'ika ina jin dadin comment dinki ubangiji Allah ya bar kauna,Aishatu inai miku fatan alkairi a rayuwar ki🥰_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿10* Da k'yar Iya ta taimaka wa Aminoni ta cire rigarta ta goge mata jikinta tana ta faman yi mata sannu, ita ko sai sosa inda yake mata zafi take tana kuka,, baki na rawa Mai koko tace"ina ne yake miki zafi" ? Aminoni ta nuna mata k'irjinta da gefen hannun ta,aikuwa tana dubawa taga gurin yayi jajazur har ya soma tashi, cikin gida ta shige da sauri tana salati,,,,, zuwa yanzu mazan dake waje sunji abunda yake faruwa nan suka shigo suna aikin raba fad'a inda Ladidi ta dunga Kai musu duka tana zaginsu duk girman su kuwa, da yake duk sun san halinta,suka k'yaleta k'okarin su fuzge Iliya da tayi masa rik'on tsauri,, Iliya da ya samu ta sake shi sai yayi waje yana maida nuffashi,, ita ko Ladidi gefe ta koma tana haki! Bakin ta bai mutu ba, tana ta zagin Iliya da masu roban fad'a,, futa sukayi suna mamakin rashin kunyar ta,, bakin kofar ta tsare tana kallon Iliya tace"Wallahi baza a siyar maka da kokon ba, don haka kasan inda dare yayi maka,, bai ce mata komai ba d'auki kofunsa ya tafi,,, cikin takaicin na bata lokacin sa da yayi gashi gidansu duk sun fi son kokon Iya saboda ta iya ga gard'i da tsabta fari tass dashi yana k'amshin citta da kaninfari. Mai koko ta dawo hannunta dauke da wata roba ta kad'o omo a ciki tazo tana shafawa Aminoni a jiki tana mata sannu, Aminoni kad'a kai kurum take tayiwa Ladidi Allah ya isa babu a dadi domin babu damar ta fada a fili,, rigar Ladidi ta sanya mata, ta dauki kwanon kokon ta zubo mata wani,, har waje ta rakata tana mata sannu,, mutanan dake waje ta tsaya tana bawa hakuri, sannan ta koma ciki, ko takan Ladidi bata bi ba, ta cigaba da sallamr mutane,, haka suka hak'ura da hukuncin da Ladidi tayi musu na farko ya koma k'arshe na k'arshe ya koma baya ********** Hajiya Asiya na zaune kan kujera tana jiran isowar su,, tayi kwalliya tsab da ita ta shiryawa shalelen ta daining shi kadai kawai ake jira,,, tana jin shigowar mota gidan ta furta Kalmar "Alhamdulilahi, idonta a kofa har suka shigo,, da sauri ya cire hannunsa daga na Salima ya rungumeta yana fad'in" Mamana I miss you!!" Shafa kansa tayi tana murmushi tace"Nima haka

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39