Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,261 words 0 views Progress saved
Download Book

my Son nayi kewar ka, sati biyu kacal sai suka zama kamar shekara a gurina" lumshe idonsa yayi yana jin d'umin mahaifiyar sa mai so da kaunar sa,, G.Abbas yace"Idan ya koma can da zama kuma yaya zakiyi gwara ma ki sawa zuciyar ki sauk'i" Hakkim ya zauna hannusa rik'e da nata yana kallon Dady din yace"Wallahi Dady saboda Mama zan iya hak'ura nifa da man bai wani dame ni ba,gwara in zauna a k'asata" Dady yace"Aikin gama ya Riga ya gama tunda kaje ka saka hannu lokaci kawai ake jira"" Hajiya Asiya tace"Tashi muje kaci abunci na mussaman" cike da farin ciki suka nufi gurin cin abunci dukan su.. Bayan ya gama cin abunci part d'insa ya nufa a gajiye ya fad'a toilet yayi Wanka ya futo daure da towol a jikinsa, ko mai bai shafa ba,ya zauna gefan gado yana latse-latse a wayar sa,, kira ne ya shigo yana dubawa yaga babban abokinsa Yusuf d'aga wayar yayi tare da fad'in "Ya akaiyi ne yaro"? D'ayan b'angaran Yusuf yace" Ganin kan hanya nasan dai yanzu all ready kana gida" Hakkim yace"Ina gida hutawa kuma zanyi karkazo ka dame ni da surutun ka na ala tsine" Yusuf na k'okarin kashe wayar yace"Idan nazo kar ka bude min kofa" Kitty!ya kashe wayarsa, Hakkim yasa Dariya yana fad'in"Lallai wannan bai da mutumci ni ya kashewa waya, anyway zai zo ya same ni""" mik'ewa yayi ya d'auko boxer da singlet Cikin kayansa ya saka ya fesa turare ya koma ya zauna inda ya tashi, latse-latse ya cigaba dayi da wayarsa.. Bugun kofa Yusuf yake yana jinsa ya share shi,, kiran wayarsa yayi ya kashe,wato ya rama kenan, Yusuf ya fi minti goma a tsaye sannan yaje ya bude masa kofa,, ya shigo cikin jin haushi yace"Wallahi mugun Dan wulakanci ne kai fa" kai tsaye yace"Waye yace ka kashe min waya, abunda na tsana a rayuwa ta" Yusuf yace"An kashe d'in, dallah kai kowa sai ka gwadawa iko da mulki to ni baka isa ba""Dariya Hakkim yake masa ya bashi hannu suka tafa,, Yusuf ya zauna yana fad'in"To yane akwai labari ne"? Tab'e baki yayi yace"Ni da na dawo ni za'a bawa labari ai" Gyara zama yayi yace"Aiko akwai labari fa""""" kallonsa yayi yana kanne masa ido,, doka ya kai masa yana fad'in"Bana son iskanci fa" Sosai Hakkim yake dariya yana fad'in "Ai nasan zance gizo baya wuce na k'oki labarin ka kullum akan abu d'aya ne,, kan wannan bak'yauyiyar budurwar taka da komai bata Iya shafawa ba"" Yusuf ya b'ata fuska yana fad'in"Bana son iya shege gwara ni ina da budurwa kai kuwa fa,ka tsaya tsoron mata dube ka don Allah gemai-geman da kai to wai in kayi auran ya zakayi da ita"" ? Ya k'arashe maganar yana dariya ta shak'iyan ci,, a kufule Hakkim yace"Uwar ka zanyi da ita d'an iska" dariya Yusuf yake har da kwanciya yace"Kullum sai sweet heart d'ina ta tambaye ka,,wai kazo ta baka kanwar ta" Duka ya kaima sa,, da sauri ya goce yana cigaba da masa dariya"" cikin jin haushi yace"Idan kaje kafad'a mata ni nafi k'arfin k'azamar kanwar ta"" Yusuf yace"Aikuwa zan fada mata wallahi,, kullum in muna hira ko a wayane ina bata labarin ka da yanda kake tsoron mace sai tai ta mamaki ita tana ganin kamar k'arya nake, a wannan zamanin akwai namiji me tsoron mace kuwa,nace ta kwantar da hankalin ta zan kawo mata kai har gida"" hararasa yayi yace"Taje tayi ta mamaki, kuma Wallahi idan baka daina bata labari na,, na rantse maka da Allah har a d'aura auranku bazan jebe". Yusuf ya mike zaune yana fad'in "Na daina ni da da nake so gobe ma ka rakani gurin ta""" tab'e baki yayi yana fad'in"Sai dai ka bari sai na dawo domin zan tafi Hutu ne"? "Ina zakaje Hutu kaji d'an iska"" Hakkim yayi wani k'ayattacen murmushi yana fad'in "Kano zani Dady yayi gidan gona wani k'auye shine nake ta zumud'i""" Yusuf yace"A'a kace zamu huta yaushe zamu tafi"? Kallonsa yayi yana fad'in "Zakaje ne"? Gyad'a kai yayi yace" K'warai kuwa""" kashewa sukayi suna dariya yace"Gobe nake so mu tafi"" Yusuf yace "Yayi Allah ya kaimu". *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/28, 10:16 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *Ayi hakuri errow⚠⚠* *🅿11* Cikin kyakyawan shiri ya futo daga part dinsa , kai tsaye part d'in Mama ya nufa cikin nutsuwa yayi sallama, Mama da mai aikin ta Jummai suna tsaye suna shirya daining ta amsa fuska a sake take fad'in "Har ka shirya kenan"? K'araso wa yayi inda suke, da murmushi a fuskarsa yace" Tuntuni na shirya yanzu ma Yusuf nake jira,banason tafiyar rana" Mama tace"Yusuf ma zashi ne"? Zama yayi kan daya daga cikin kujerun cin abunci yana fad'in"Jiya daga ji ina zancan yace shima zashi" Salima dake zaune can falo tace"Babban yaya nima zani don Allah" hararata yayi yace"Babu inda zani dake" Mama tace."Kai kuwa kaje da ita mana dama sunyi Hutu". Yace. "Mama kin san ko kwana zamuyi kuwa"? Girgiza kai tayi tana fad'in" Sai ka fad'a". "Sati biyu zamuyi fa" Mama tace"To meye a ciki ka tafi da ita kawai" shiru yayi baya son musu da Maman shi, Gen.Abbas ne yake saukowa daga bene yana sanye da jallabiyya ruwan toka hannunsa rike da Jarida ta Daily trus, idonsa farin galashi ne, zama yayi suna gaisawa Mama ta fara had'a musu Kalaci, bayan sun kammala Hakkim yace."Dady na fa shirya" Gen. Yace. Na gani ai daga dawo wa zaka k'ara tafiya jiya munyi waya da masu aikin komai ya kammala, mybe yau zasu bar gurin amma dai na fada musu su zauna sai kazo". Yace. "Dady yanzu ma Yusuf nake jira tare zamu tafi". Salima ce ta futo cikin shiri sai murna take hannuta rike da trolly d'inta ya loda uban kaya, Dady yace." Ke kuma fa"? Narai-narai tayi da ido, Mama tayi saurin cewa"Tare zasu tafi" ."Shine ta lodo kaya Cikin jaka kamar wacce zata bar gari" tsuro-tsuru tayi, Hakkim ya buga mata tsawa! Tare da fad'in"Maza je ki rage kayan nan idan ba haka ba wallahi inki zuwa dake". Da gudu ta koma dakinta ******** Ihun!! Ladidi ne ya cika gidan,inda har daga waje ma ana jinta, sai zageye tsargidan take tana buga tsalle Mai koko na bin ta sai ta kamata,hannuta rike da sabuwar reza cikin takardar ta,fad'i take" Baki tsaya ba ko Ladidi ki daina wahalar dani, gwara ki tsaya a aske miki gashin kema kya huta da wannan azababbiyar kwarkwatar da ta dame ki". Ladidi tace"Wallahi ba zaki min aski ba,haka kurum sai kice sai kin aske min gashi ne,ina ruwanki da kwarkwatata ki bar min kayata mana, Mai koko tayi kanta da sauri zata damk'e ta, ta buga wani uban tsalle! Sai gata ta tsallake rijiya da baya!! A gigice Mai koko take salati, babu shiri taje ta aje rezar tana fad'in"Kinga na aje rezar futo daga bayan rijiyar Ladidi"mak'e kafad'a tayi tana fad'in"Wato in futo ki kamani,wallahi na gadama sai in fada rijayar ma" Sanin rashin hankali da gab'unta na Ladidi yasa Mai

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39