Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

koko ta fara rarrashin ta da dadad'an kalamai, tace."Kinga d'azu munyi magana da Mairo mai dashi cewar zata bani d'auka ta uku shine nace da ta bani zan shiga kasuwar burni na siyo miki kayan kallo" Ladidi tasa dariya tana fad'in"Nagane wayo zakiyi min, ni sai na fad'a a rijayar ma" tayi taga-taga!! Kamar zata fad'a!Mai koko ta rafka salati zaninta na k'okarin fad'uwa tayi waje da sauri ko ina zata oho"! Dariya Ladidi take mata, ta buga tsalle ta futo daga bayan rijiyar, can wani guri da ya rushe Cikin gidan taje ta b'oya dake tunda gurin ya rushe babu mai zuwa gurin,Mai koko ta dawo ciki tare da wasu mutane biyu ita a nufinta su taya ta bawa Ladidi hakuri, wayam! Babu ita a gurin, Wani irin salati Mai koko ta kurma tayi bakin rijiyar gadan-gadan tana fad'in"Shikkenan ta fad'a cikin rijiya dama nasan Halin ladidi kome tace zatayi sai tayi, kuka ta farayi tana kara zura kanta cikin rijiyar, sai akayi sa'a tarwad'ar dake cikin rijiyar suka dunga motsi a ciki, kuka sosai Mai koko take tana fyace majina tace"Kunyi tsaye meye amfanin ku, kuzo Ku shiga Ku d'auko ta,Idan ma mutuwa zatayi ta mutu a gabana" Kallon juna sukayi suka kama hanya futa suna fad'in"A'a Mai koko bari dai mu garzaya mu kira miki sarkin ruwa, wannan yarinyar me k'wamk'wamai watak'ila ma su suka jata ta fad'a ciki, haka kawai mu shiga su kama mu, domin ita suna iya sakin ta, tunda tasu CE"Mai koko ta saki baki har suka fuce. Suna futa d'aya yace."Allah yasa ma su kaita bakin ruwa su d'auke kayan su kowa ya huta da masifa". Mai koko ta lek'a rijayar tana fad'in"Mai yasa zakiyi min haka Aminatu mai yasa zakiyi min ke kad'ai nake kallo a matsayin Aminu shine zaki fad'a rijiya Haba Ladidiya kiyi hakuri da halina da halin Kawun ki, majina ta fyace! da gefen zaninta sai zura kanta take cikin rijar tana sambatu! Ladidi ta lek'o daga kanta ta wata 'yar kafa sai dariya take yiwa Mai koko ganin yadda take kuka tana fyace majina dariya har sai da ta kwanta. Kafin kace kwabo labari ya bazu a cikin unguwar Ladidi ta fad'a rijiya wasu suyi jaje wasu suyi ko murna suke cewar an rage mugun iri, D'alha na gurin sana'ar sa labari ya riske shi, babu shiri ya tawo gida ko kayan sana'ar bai d'auko ba, Mai koko kuwa ganin kamar tana son fad'awa cikin rijiyar yasa mak'otan ta suka nufi gudansu da ita sai sambatu take, hakan ya bawa Ladidi damar futowa daga mab'oyar ta tayi waje a guje! Kanta ko d'ankwali babu,wani abun mamaki da al'ajabi idan ka kalli gashin nata sai ya baka tsoro domin Duk ya dunk'ule ya cure guri guda yayi wata muguwar dauda ga tsakin kwarkwata da amosani man burjiki! Wani gurin sal-sal babu d'igon Gashi wani gurin da akwai, ita kanta idan tana sosawa ciro gashin take da hannunta ta yar. *Ni kaina sai da nace Ladidi da kin sani kin bari anyi miki aski domin shine mafuta a gare ki* Can hanyar titi ta nufa tana fafara gudu kamar mahaukaciya, ko da wasa babu wanda ya ga gilmawar ta. Sarkin ruwa tare da jama'ar gari suka shiga cikin gidan, jin ance ga Sarkin ruwa nan yazo yasa Mai koko futowa daga gidan da take da sauri duk tayi wujuga-wujuga, suka had'u da D'alha sai gumi yake zabgawa babu wanda yace da Dan uwa sa komai suka afka cikin gidan, To duk iya lalube Sarkin ruwa yayi amma bai ga Ladidi ba kusan awarsa guda a cikin ruwa ya futo yana fad'in"Da Ladidi tana cikin rijiyar nan to ko da na ganta domin na baje basira ta sak'o da loko, kogo da kogona babu inda ban duba bata ciki". Guri yayi Tsitt!! D'ai-d'ai jama'a suka fara futa suna surutu cewar "dama tuntuni suna zargin yarinyar " yar ruwa ce to gwara da suka d'auke kayansu kowa ya huta. *********** Tafiya suke suna hira irin ta abokai sai dariya suke ma junansu Salima na bayan mota da waya a hannunta tana chat fa friends d'inta, sam bata jin abunda suke cewa to suma k'asa-k'asa suke hirar su, har suka shigo Kano suka d'auki hanyar K'auyan d'an kunkuru Yusuf yace"Har na fara jin wata iska me dad'i wallahi" Dariya Hakkim yayi yace." Sai ma ka shiga garin sosai zakaji dad'insa shiru babu hayaniya sai manya bishiyu masu bada iska mai dad'i". Wani dank'areran get nake hangowa tunda nesa nan naga Hakkim ya nufa da mota, wasu mutane dake tsaye bakin gurin suka bud'e masa get d'in ya shiga da motar ciki, sai da yayi tafiya sosai sannan ya samu guri yayi parking Yusuf ya futo daga motar yana fad'in"Wow kaga guri sai kace a k'asar waje Yaro" ? Murmushi Hakkim yayi ya kashe motar futowa yayi yana mik'a ta gajiya gurin kawai yake bi da kallo cike da sha'awa irin bokokin nan na k'asar waje hudu ne sai part biyu da gurin kiwo an kewaye shi na kaji daban na kifi daban na talo talo daban ko wanne an kewaye shi, gefan hannunsa kuma wasu manya-manya lambu ne a kewaye da raga k'ofar da mutum zai shiga tana can baya, da sauri yaja hannun Yusuf suka nufi gurin shiga Salima na binsu a baya tana tsalle da dariya fad'i take"Zanci d'ata in more abuna dama a abuja babu sai mutum ya sha wahala kafin ya samu. Suna shiga kowa ya kama gabansa domin kashe kwarkwatar idonsa , Hakkim ya nutsa sosai ciki, yaji motsi saman bishiya d'aga kai yayi da sauri, wata halitta ya gani ita ba mutum ba ita ba aljana ba, gabansa ya fad'i, dake namijin duniya ne sai ya dake yana hirji cikin zuciyarsa cikin jarumta yace"Ke wacece ke mutum ko aljana"? Ladidi ta tsura masa ido tana kallonsa,a zuciyar ta tace"Dube shi kyakyawa d'an burni yasa fararan kaya gaskiya yayi kyau"!! Buga mata tsawa! yayi a karo na biyu ya sake fad'in"Mutum ko aljan nace kun tsura min ido babu kyawun gani kuna kallo" Soso kanta tayi ta ciro kwarkwata har biyu, ta kalle shi ya kalle ta daga saman bishiyan ta sako masa kwarkwartar ta fad'o jikinsa, abunka da fararan kaya, aikuwa nan take suka nuna kwarkwata ga tanan tana bin gefen kafad'ar shi har guda biyu, tsalle! Ya buga ganin k'awaro baki na bin jikinsa ya bugeta cike da k'yamkyami ya tsartar da miyau! Ya d'ago kansa a fusace! Ganinta yayi mak'ale jikin bishiyar tana k'okarin sakkowa kamar me sufa, dura k'asa tayi yayi sauri matsawa baya gaban shi na bugawa! Amma idan ka kalli fuskarsa baza ka gane razanar sa ba,, cikin minti biyu ya gama k'are mata kallo, k'anjamammiyar yarinya mai k'irar muciya kanta wani gurin da gashi wani garin babu fuskarta a rame sai uban dogon hanci irin na aljani ga hannuta da k'afar ta k'ananu duk jijiya" hirji yake Cikin zuciyar sa, yace."Ke aljana ce ko mutum"? Kai tsaye tace"Aljana ce" Cikin tsawa yace"Bar nan yanzu don ubanki ko na zane ki, dagani ke ba aljana bace ibilishiya ce,me ya kawo nan har da hawa kan bishiya" ? "kar ka k'ara zagina" tafad'a idonta a kansa, a zabure! Yace"Ubanki uwarki kajini da

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39