Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

sosai! Suka fara kallon-kallon ita dashi, idonta yayi bala'in ja na azaba! Shims nasa idon sunyi jajazur! Ko da yake dama tunda suka futo haka nasa yake, a zafafe! Yace." Ke dan ubanki ya sunanki."? Cikin shak'ewar nuffashi tace." Ba dai Ubana wallahi meye ruwanka da sanin sunana,kuma zaka san ni ka Mara." Yace." Sai dai uban wa.". Ko nuffasa bata bari yayi ba tace." Sai dai ubanka." Murmushi yayi kana ganinsa kasan zaiyi mugunta, sakin ta yayi ta fad'i gurin tana mai da nuffashi, ta zabura zata mike yq maida kafarsa kan tata, blet din jikin shi ya Ciro, ya fara lafta mata, Ladidi ta fara ihu tana neman d'auki. Salima na cikin mota tana kukan tashin hankali tana jin tsoran kar yayan ta yayi kisan kai! Dukan Ladidi yake ko ta ina tana ihu! Wanda babu hawaye, da wuya tayi wuya sai ta fara sharb'en kuka tana cigaba da zaginsa,Salima ta bude mota a tsorace tazo ta rike shi tana bashi hakuri ya bangaje ta tafad'i a gurin,ya cigaba da laftar Ladidi har sai da yaga bakin ta yayi shiru, duk da haka bai saurara mata ba sai da yaga ta daina nuffashi sannan ya k'yaleta! Ya maida belt d'insa gami da matsawa gefe guda yana mai da nuffashi. Yusuf ya k'araso gurin hankali a tashe, Ladidi kawai yake bi da kallo cikin tsantsar tashin hankali ya jefar da tayar yayi kanta yana salati. Salima ya kalla bakinsa sai motsi yake, ita kam kuka kawai take, Hakkim kuwa tayar ya d'auka ya fara sanyawa babu abunda ya dame shi. Suna can durk'ushe kan Ladidi sukaji karar mota a Kansu,da sauri suka mike Hakkim ya kunna mota yana k'okarin tafiya ya barsu, jiki a sanyaye suka bude motar suka shiga cike da tausayin Ladidi da bata san a wace duniyar take ciki ba. Sai da suka hau titi sosai Yusuf ya samu bakin magana yace." Yanzu sai da ka aikata abunda kayi niyya kan yarinyar nan, wato duk irin maganar da Dady yayi maka baka d'auka ba ko."? Hakkim yayi masa banza fuskarsa a had'e take har yanzu, wani gefen kuma ya dan samu sassauci tunda ya hukunta yarinyar yana ganin gaba idan ance mata gashi a guri baza ta zo gurin ba. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." To wallahi ka sani kamar Dady yaji wannan labarin, kome zakayi sai na fada masa." D'aga kafad'u yayi alamun bai dame shi ba. Cikin b'acin rai suka isa Abuja. Mai gadi ya bude musu get yana musu bar ka zuwa, Yusuf ne kawai ya amsa, Hakkim ya shige da mota ya gyara parking, futowa yayi ya nufi part d'insa, Yusuf da Salima suka nufi cikin gidan. Mama na zaune a falo tana kallo taji sallamar su ta dago kanta cike da walwala da farin ciki ta amsa, Salima ta tawo da gudu gurinta, rungume ta tayi ta fashe da kuka! Mama ta kalli ya Yusuf ta ganshi duk a furgice tace." Yusuf me ya faru ina Abdul yake." ?Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kan kujera yana goge gomin dake tsatstsafo masa, yace." Lafiya ba lafiya ba Mama." Salati Mama tasa tace." To ai sai kayi min bayani. Salima ta bude baki zatayi magana Mama tace." A'a bake na tambaya ba." Shiru tayi tana ajiyar zuciya. Yusuf ya warware wa Mama duk abunda ya faru tunda ranar da sukaje har yau da zasu dawo. Mama ta dinga salati tana sallallami, tace."Wai wannan zuciya ta Abdul ina zata kaishi yanzu idan ya kashe musu yarinya fa." ? Yusuf yace." Wallahi Mama na tsorata da al'amarin domin ni gani nake ma kamar ta mutu." Salima tace." Wallahi nima haka." Mama ta mik'e tsaye da sauri! Jikinta sai rawa yake wayar ta ta d'auko ta kira mijinta yana dagawa tace." Kazo gida babu lafiya." Ba ta jira abunda zai ce ba ta kashe wayar. Tace." Yusuf je ka kira min shi yanzu.' Yusuf ya mike da jiki a sanyaye ya nufi part d'insa. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿19* Lokacin da Yusuf ya shiga d'akin samun sa yayi zaune gefen gado d'aure da towol a jikinsa da alama daga Wanka ya futo, yana zaune yana danne-danne a waya babu abunda ya dame shi. Cikin takaici Yusuf yace." Sai kazo Mama na kira,wato kai kanan kana danne-danne a waya babu abunda ya dame ka ko." Dago kansa yayi yana kallonsa yace." E babu abunda ya dame ni, d'in, so kake in tada hankalina kamar yanda ka tada naka ko me."? Yusuf yace." Zakayi bayani ne wallahi ni kaga tafiya ta, idan kaga dama kaje kiran da ake maka." Tsaki! Yaja ya d'auke kansa Yusuf ya futa cike da jin haushin sa. K'ananun kaya ya sanya a jikinsa Wanda suka masa kyau sosai ya fesa turare, me sanyin kamshi wayarshi ya d'auka tare da eirpix d'insa ya futa. Mama na tsaye a farlo tana kai kawo hankalinta duk ya tashi, yayi sallama ya shiga, Salima ce kawai ta amsa masa yana kallon fuskar Maman shi yasan tana cikin tashin hankali da damuwa, k'okarin zama yake ta dakatar dashi ta hanyar fad'in." Kar ka zauna domin zama bai kama ka ba." Tsayawa yayi yana sunkuyar da kai kasa, tace." Ka kyauta Abdul nace ka kyauta da abunda kayi." Shuru farlon yayi, tace." Kullum ina gargadin ka da ka rage zafin zuciyar nan taka kana mai da abun wasa, duk naji abunda kaje ka aikata a garin mutane ka sumar da yarinyar mutane har sau biyu kan abunda bai taka kara ya karya ba ko."? Dago kansa yayi yana kallon Maman yace." Mama kin San abunda yarinyar nan tayi min kuwa? Nasan Yusuf ne zai ce miki babu abunda tayi min domin ya kareta, idan da tsautsayi lokacin da ta fasa kwalabe na taka da narasa k'afafu me za kuce ko kuma in kwanta jinya me tsayi kinga ta cuce nu, wallahi Mama ibilicin yarinyar nan ya wuce tunanin me tunani shiyasa na hora ta yadda gaba baza ta kara yiwa wani Abu makamancin nawa ba." Mama tace." Kaine kake ganin haka, Abdul kasan halin mahaifin ku dai ba kai kadai abun zai tsaya ba har dani, babban abunda ya tada min hankali yanda Yusuf yace ka hana ya tsaya ya ceci rayuwar ta kayi mata dukan mutuwa tana kwance bata san inda kanta yake ba." Sunkuyar da kansa tayi har yanzu baya nadamar abunda ya aikata ga Ladidi. General. Ne yayi sallama ya shigo cikin sauri, duk ya gansu a tsaye, hankalin sa ya kara tashi, wata irin tsawa! ya buga musu har da Maman yace." Ku fada min abunda

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39