Chapter 24
Chapter 24
muje ciki dactor ya duba ki kinji ko." Ladidi ta zumb'uro baki gaba. Yace." Dawa-dawa kike so mu shiga tare." ? Shiru tayi masa. Haushi yasa D'alha ya buga mata tsawa tare da fad'in." Idan baki sake ta wallahi sai Nazo nan na gaura miki mari." Mai koko tace." Kaga D'alha rabu da ita don Allah.Ina dalili nifa wannan asibitin be kwanta min a rai ba,asibiti ko ina sanyi hatta k'afar ka in ka aje ta a kasa sanyi ga wasu abubuwa a bango naji fa ana cewa wasu asubitin duk barna suke aikata wa. Gwara muje na Murtala kawai." Takaici ya hana D'alha cewa komai. General yace." Iya wannan hospital din ana biyan kudi sab'anin sa dana gwamnati kenan kinga ai baza mu bi wannan dogon layin ba, kiyi hakuri mu shiga tare dake babu abunda za'ayi mata." Mai koko ta kalli Ladidi tana yi mata magana k'asa-k'asa sannan ta sake ta suka mike General yayu gaba suka bishi a baya. D'alha ya nemi guri ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Hakkim kuwa takaici ya hanashi cewa komai yarasa me yasa Dady ya damu da al'amarin yarinyar nan wallahi. Shiko Yusuf Dariya yakewa Ladidi ganin yanda take ta kalle-kalle kauyacinta kawai take. Dactor suka gaisa da General cikin mutum ci yana tsokanar Ladidi bata San ma yanayi ba domin tana can tana kallon tv mak'ale a bango na wani India film na fad'a, amma ba fassarar hausa bace. Dariya ta kyalkyale dashi tace." Iya kalli wannan film din ki gani don Allah, na fada miki afton nan Dan bala'in ne hinefa singam da nake fada miki,hahahahahaha." General da Dactor suka saki baki suna kallon mara lafiya tayi tsalle gaban tv tana kallo tamkar zata rikito da ita daga sama. Wannan karon kunya ce ta kama Iya ganin abunda Ladidi take babu kamun kai,kokari kawai take tayi tsalle ta tab'o tv in da jarumi Ajay devgan yake ragargaza 'yan gidan boss da bundigar sa,Ihu!! Kawai ta kurmawa tana buga tsalle. Sosai dariya take cin General yana k'okarin dannewa sai da ta subuce. Ganin yana dariya yasa Dactor ya fara yi shima Suna kallon juna. Iya tana k'okarin kamo ta tana fuzgewa duk kunya ta ishe ta gashi tun farko dama bata iya sarrafa Ladidi. Dactor ne da ya gaji da abunda take ga jama'a a na jiran shi a waje yasa ya buga mata tsawa! Tare da fad'in." Ki nutsu yanzu ko in sa a zo a zuk'i jinin ki kuma inyi miki allura goma.'' Firgigit ta dawo nutsuwar ta jin zan can Allura sai taji kallon ya fuce mata daga rai mugun tsoran dactor ya shiga zuciyar ta simi-simi ta dawo kusa da Iya tana zare ido.! Iya tace." Ke kam anyi mara wayo wallahi ke da baki da lafiya kike tsalle-tsalle." Da sauri tace." Nifa lafiya na lau ni dai kice kar ayi min allura bana so." General yace." Ai dama ba allura za'ayi miki ba, dawo nan kusa dani dactor ya duba ki kaman matsalar kunnen ki,sai ya baki magani bazan bari yayi miki allura ba." A d'arare taje ta zauna inda yake nuna mata sai harara Dactor take yi, bai lura ba yana can yana aikin sa. Ya d'ago kansa a nutse yace Alhaji meye Matsalar ta ne." Iya da ba'a tambaya ta fara zayya no masa abunda ya faru." A hankali ya ambaci sunan Ladidi Wanda ya gani jikin kati wato Amina sai yaga bata dago kai ta kalle shi ba, da Ladidi ya kira ta da k'arfi sai ta dago kanta tana kallonsa. Mik'ewa yayi hannunsa rike da wani Abu,ganin yana zuwa inda suke ne yasa ta tsora ta ga wani Abu a hannunsa. Kafin General ya ankara ta buga tsalle, wajan kofar futa suka tsince ta tana kici-kicin budewa ta futa. General ya mike da sauri yana kiranta ko sauraron sa ba tayi ba Allah ya bata sa'a ta bude tayi waje da gudu.! Su Hakkim na zaune reception suka ga futowar ta kamar walkiya tayi kofar futa. D'alha gyangyad'i yake bai ganta ba, kasan cewar jiya baccinsa ragagge ne. General suka gani ya futo hankali a tashe yake fadin "Tana ina ne." Kofa ya kalla yaga gilmawar ta ta futa, ya bugawa Hakkim tsawa tare da fad'in" Maza tashi kaje ka dauko ta.wato kana kallo ta futa baka yi wani Abu akai ba ko."? Hakkim ya mike da sauri ya futa yana kunshe dariya yaji dad'i da Ladidi ta nunawa Dady wacece ita. General ya jin gina da hango yana sauke ajiyar zuciya gefe guda kuma yana mamakin halin yarinyar kamar aljana, yanzu ya fara sarewa da lamarinta. Hakkim na futa ya hango ta bakin get tana rigima da masu gadi, dole sai sun barta ta futa su kuma sun hanata saboda ganin yanda ta futo daga ciki tana fella guda sai kace me tab'in hankali. Kuma sunga lokacin da suka zo cikin mota sosai asibiti yake da tsaro. A hankali ya Isa inda suke dama tun kafin ya k'arasa yayi shiri ya tattate hannun rigarsa, yana isa ya sunkuce ta, sosai ya rike tamau! Ya had'e k'afafun ta da hannaye ta ya sab'a a kafad'arsa. Ladidi ta dinga ihu! Tana zandare masa a baya Hakkim ya rik'e hannuwan balle ta doke shi, sai ta kafa kanta a wuyansa ta gartsa masa cizo. Ko a jikinsa, bai sauke ta ba sai ya kaita har ofis din dactoe. Iya tace."Sannu na yaba da k'okarin ka samari da baka d'auko ta ba wallahi futa waje zatayi k'arshe mu rasa inda take, Maza danne ta likita ya duba ta." Hakkim ya b'ata fuska bai mata komai ba ya fara k'okarin futa sai suka ci karo da General da D'alha suna k'okarin shigowa, Dady yace." Koma muje ka riketa a duba kunnen nata. Babu yadda ya iya ya koma ya zauna kan wata kujera Ya jawo Ladidi tana turjewa ya rike tamau! A jikinsa Dactor yazo da Abu a hannunsa ya kunna hasken sa, ya kafa kunnen Ladidi yana dubawa. Ihu!!!!! Take kurmawa tun k'arfin ta,tana haure-haure da hannuwata da k'afafun ta tare da ya kushin Hakkim ko ta Ina.ganin hakane yasa D'alha zuwa gurin ya rike hannunwan nata tamau! Dactor ya cigaba da aikinsa. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿25* Hakkim zuciyar sa zafi take masa yana jin kamar ya saki Ladidi ta fad'i kasa saboda yanda take ta faman duk k'irjinsa duk ta ya kushe masa fatar hannunsa ga majinarta da miyau duk sun b'ata masa jikinsa, lokaci guda yaji zuciyarsa na tashi kyamkyamin Ladidi yake sosai.ya dinga kauda fuskarsa har dactor ya gama dube-duben sa ya matsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39