Chapter 26
Chapter 26
da sauri Iya tace." Alaji nan ne gidan naka. " ? Da murmushi a fuskarsa yace." Eh nan ne amma ba'anan muke da zama ba ni da iyalina muna abuja, kwanaki na siyi gurin nan nayi gidan gona domin mu dinga zuwa hutu ni da iyalina." Caraf! Ladidi tace." Dama bana fada miki ba Nace gonarmu ce suka sace, mana shine daga zuwa zan tsinko mangwaro ya kamani yayi ta duka ni da gonarmu Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na rama." Hakkim tun sanda ta fara magana yake kallonta ta mirror yana jin wani kuttun bakin cikin da takaici ji yake kamar ya tsayar da mota ya futar da yarinyar waje, amma babu hali yin haka. Yanzu tunanin da yake yaya za'ayi ya bar garin domin dai bazai iya had'a guri da ita yana jin zai iya kasheta saboda yanda yake jin zafinta a cikin zuciyarsa. Dariya General yayi jin abunda Ladidi take fada ya kalli D'alha dake sunkuyar da kai cike da kunya yace." Hakane abunda ta fad'a 'yan samari."? D'alha ya sunkuyar da kansa kasa sosai yace." Hakane Alhaji mun siyar da gurin ne ni da mahaifina kafin rasuwar sa shekaru goma sha biyu da suka wuce,sai dai ba duka ne gurinmu ba." General yace." Ayya! Allah ya jikansa da rahama, ya kyauta makwancin mazan jiya hak'ika nasan babbar matsala ce tasa ya daga gonarsa ya siyar haka." D'alha yace." Hakane Alhaji. " General yace." Ku futo mu shiga ciki ai duk Iyalina na ciki sai Ku gaisa." Futowa sukayi dukaninsu, banda Hakkim shi tunda yayi parking gurin da aka tanada domin aje mota yayi fucewarsa ya barsu cikin motar. Kai tsaye sharararn farlo suka nufa dukansu, Iya sai kalle-kalle take na k'auyanci ita ko Ladidi dama ba wannan ne zuwanta na farko ba. Hajiya Asiya na hakimce kan kujera da romot control a hannunta tana neman tashar kallo, Salima ta Dora kanta a cinyarta suna hira, suka ji sallama. Hajiya Asiya ta amsa a nutse tana yi musu sannu da zuwa, Salima ta mike da sauri tana kallon Ladidi cikin tsoro. General yace." Bisimilh Ku zauna mana." D'alha ya zauna yana satar kallon farlo. Iya ma haka suka zauna guri guda da Ladidin ta. Cike da farin ciki Hajiya Asiya tace." Alhaji da alama waccan CE yarinyar."? Yace." Itace Momy kin ganta k'arama ko." Tace." Wallahi kuwa, zo nan kinji mu gaisa." Tafad'a tana mik'awa Ladidi hannu." Kin zuwa tayi sai da D'alha ya buga mata tsawa sannan ta tashi tana zumb'ura baki. Mama tace. " kayi mata a hankali mana." Ladidi ta k'arasa kusa da ita, da sauri Salima ta mike ta bar gurin jikinta na b'ari! Kusa da Dady dinta ta koma tana zare ido! Ya kalleta yana fadin." Ga 'yar uwa na kawo miki zata zauna damu sati uku ta karb'i magani Dan uwanki yayi mata lahani ke shaida CE kin gani da idon ki." Hajiya Asiya tace." Alhaji ban fahimci abunda kake nufi ba." Nan General ya warware mata duk abunda ya faru da abunda dector yace . salati kawai takeyi tana duba kunnen Ladidi tace." Oh ni Asiya yaro na nema ya jawo mana masifa." Mai koko ta kalla tace." Kuyi hakuri don Allah tsautsayi ne." Mai koko tace." A'a babu komai ai ya wuce. Sai dai ga Ladidi nan amana Ku kula da ita domin marainiya CE, zan dinga zuwa kullum ina dubata" Hajiya Asiya tace." Ai kar ki damu Iya insha Allah za kula da ita yanda ya kamata Allah ya bawa zuciyoyinku hakuri dai." D'alha yace." Ai magana ta wuce mu zamu tafi gida." Mik'ewa sukayi suna shirin tafiya. Abun mamaki sai naga Ladidi ko a jikinta ta nemi guri ta zauna gami da tsurawa TV ido fuskarta d'auke da murmushi sai motsu-mutsun dad'i take, TV din D'alha ya kalla sai yaga jarumi Salman khan da kayan 'yan sanda a jikinsa yana suburbud'an 'yan gidan boss! D'auke kansa yayi cike da takaici. Iya ta kalleta tare da fad'in."Ladidi mun tafi babu rakiya ne."? Inaa!! Ladidi na can ta na kallo tama manta dasu a gurin. *COMMENT* *VOTE AND* *SHARE* *16/October/2009* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿27* General yace." Iya Aminatu ta samu kallo ai ba zata saurare ku ba." Murmushi Mai koko tayi tace." Aikam gashinan naga alama Humm Ladidi da son kallon talabijin ai sai addu'a." Dariya sukayi dukaninsu Hajiya Asiya ta mike domin tayi musu rakiya, tare suka futa harabar gidan Wanda yayi dai-dai da shigowar Salim cikin mota yana k'okarin gyara parking General yace." Ya bari tukkuna ga bak'i nan ya mai dasu gida, cike da mamaki Salim yake kallonsu suka gaisa sama-sama ganin kallon da yakewa su D'alha na rashin sani yasa ya fara yi masa bayaninsu, sai ya saki fuskarsa sosai suka shiga mota General na daga musu hannu suka futa daga gidan. Salima kuwa da aka futa aka barta ita da Ladidi cike da tsoro take kallonta, sai taga Ladidi kwata-kwata hankalinta baya kanta tana can tana kallo abunta. Muryar ta na rawa tace." Ya sunan ki na gaskiya."? Ladidi ta juyo fuskarta d'auke da murmushi tace." Amina kefa."? Tace." Salima sunana." Dariya Ladidi tasa tace." Sunan 'yan gayu 'yan burni da dad'i Wallahi. " Salima tasa dariya wanda yayi dai-dai da shigowar su General yace." Yawwa Salima kuje da ita ki nuna mata komai tayi wanka sosai sai kuzo muje cikin gari a siya mata kayan kwalliya irin naki domin so nake Aminatu ta dawo 'yar burni.' Ladidi ta buga tsalle ta koma kusa da General tana washe baki tace." Ni so nima wallahi baba daga yanzu ka zama Ubana zan zauna daku ina sha'awar Ku." Tausayin ta yaji sosai yace." Muma muna sonki Aminatu zan nemi alfarma gurin Kawun ki ya bani aronki in sanya ki a makaranta.". Murna sosai ta dinga yi, Hajiya Asiya taji tausayin ta da so da kaunarta. Nan Salima ta jata d'akinta suka shiga toilet ta nuna mata komai. Dake Ladidi akwai saurin fahimta bata sha wahalar hada ruwan Wanka ba tayi tsaf ta wanke bakin ta da miskilin kamar yarda Salima ta nuna mata ta futo daure da towol Wanda ta aje mata. Salima ta kalleta tana b'oye dariya ganin yanda kanta yake babu gashi duk yayi cibiri-birici gashi nan ya fara futowa ta wanke shi tas! Tace." Yanzu in muka shiga cikin gari za siya miki man gashi me kyau daka gani kina da kufan gashi ganin ya fara daga farko sinkif dashi." Ladidi ta zauna kusa da ita tace." Kwarkwata ce ta dame ni shine Kawuna yasa aka aske min amma duk cikin k'awayena babu wacce ta fini
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39