Chapter 29
Chapter 29
ya bashi, yayi ta godiya ya tafi. Motar ya shiga ya kunna suka bar gurin, General da 'yayansa hira suke sosai babu me saka sunan Hakkim a ciki to shima nashi b'angaran yaji dadin haka, sauri-sauri yake suje gida ko ya daina ganin mummunar fuskar yarinyar duk sanda zasu hada ido da ita ta mirror mugun kallone yake raba su da ita. Suna Isa gida ana kiran sallahr la'asar da sauri ya futo daga motar domin baya so ma wata magana ta had'a shi da Dady din don kar yace ya d'ibi kayan ya shiga dasu ciki. Yana shiga parlor dircat bedroom d'insa ya shiga babu wanda ya kula a cikinsu Salim ne yake masa magana da cewar "broth kun dawo kenan"? Uffan be ce masa ba ya wuce ciki." Hjy Asiya tace" butsu kenan mybe sun tafka rigimar shida Dady shiyasa ya shigo yana bugun iska" Yusuf yace." Aikuwa kuma nasan duk akan Ladidiya ne" Salim yace." Aikuwa na lura yarinyar ta shiga ran Dady wallahi ". Hjy Asiya tace." Ni kaina yarinyar tana bani tausayi sosai na lura shima Dadyn Ku tausayin ta yake ji kasan shi da tausayin tsiya" Yusuf yace "hakane Mama." General na shigowa ya umarci su Yusuf da Salim suje su kwaso kaya cikin mota, suka mike domun cika umarni, daining ya nufa yana fad'in" Zo ki had'a mana abunci mu kwaso yunwa sosai." Hjy Asiya ta mike tana fad'in "ai naga alama gashi wancan sarkin zuciyar ya shigo a fusace kamar zai duke mu." K'wafa general yayi yace." Rabu dashi kinji! Na rasa me ke damun Hakkim wallahi zafin zuciyarsa yayi yawa, Aminatu ya samu Sahad sto ya k'ara duka jama'a suka taro a Kansu." Hjy Asiya ta saka salati tana fad'in " Me tayi masa kuma"? Girgiza kai yayi yace." Ta nuna tana son takalmi to kinsan halin mutuniyar taki da k'auyanci tana k'okarin yi musu barna shine ya yanke wannan hukunci a kanta." Hjy Asiya ta kalli LADIDI dake tsaye tana kumbura kamar zata fashe tace." Zo Amina ke Salima Zo Ku ci abunci." Suka k'araso gurin tare da zama kan kujera. Nan ta hadawa kowa nashi cikin hikima take wa Ladidi Fad'a sosai jikinta yayi sanyi da abunda ta aikata Hjiy Asiya ta kalli Salima tace." Ki nuna mata yadda zata yi amfani da komai ki dinga koya mata abubuwa burni ta fara girma kinga ko zaki girme ta da k'adab ne ki dauketa a matsayin k'anwar ki". Salima tace." Insha Allah Mama na dauki alk'awarin yin haka, sai naji ina ma kakarta zata barma na ita." General yace." Ba ke kadai kike wannan tunanin ba Salima." Haka dai suka ci abunci suna hira , bayan sun gama General ya mike ya shiga bedroom domin yin wanka da sallar la'asar Salima da Ladidi suma suka shiga cikin wani bedroom Sukayi Wanka tare da Sallah nan Salima ta baje kayan tana nunawa Ladidi yanda ake amfani da komai. Magariba kowa ya shiga domin yin sallah Ladidi ta futo parlor taga babu kowa da sauri ta nufi kofar futa, harabar gurin shiru duhu ya fara kawo wa masu gadi duk sun juya baya suna sallah tazo ta bud'e k'aramar k'ofa ta futa, ko ina zata oho!!!! *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ *26/October/2019* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿30* Waige-wage take yi babu kowa a layin tsitt!! Kawai ta sai ci hanyar zuwa gidan su tana yi tana waiwayen bayan ta, Hakkim ya futo daga wani massalaci dake bayan layin ya hango ta tana tafiya kamar wata mahaukaciya, bayan ta ya bi da sauri domin ya tsorata mutuk'a yana jin tsoran kar ta gudu Dady ya sirfa masa bala'i yasan cewa zai yi shine ya kore ta, jin ana bin ta a baya yasa ta wai wayo da sauri suka hada ido da Hakkim din a guje!!! Ta falle, siket din jikinta na harde ta, shima gudun ya sanya da k'arfi yana tattare hannun rigar shi saboda ya lura sai yayi da gaske domin yasan halin taurin kan yarinyar. Garin waiwaye taji tun tub'e da wani k'aton dutse ta fad'i a gurin tare da rik'e k'afar ta guda tana kurma ihu!!! Ya k'arasa gurin yana watsa mata wani banza kallo. Cikin wata razananniyar tsawa! Yace." Don ubanki ina zakije? Kurrr!!! Tayi masa da ido tana cije bakinta. Ya k'ara buga mata tsawa a karo na biyu tare da fadin "ba magana nake dake ba ne shashasha mahaukaciya kawai." Da sauri ta mike tsaye tare da fad'in." Kaine mahaukaci bani ba." Cike da mamaki yake kallonta. K'irjinsa ya nuna da hannunsa yace." Ni." Gyad'a kanta tayi babu tsoro a idonta. Wani bahagon mari ya kwarfa mata a fusace! Yace." Wuce muje gida ko yanzu in karasa toshe miki d'aya kunnen naki." Ido jazur tace." Ank'i a wuce din." Janta ya fara yi a k'asa ita kuma tana d'ebo k'asar gurin tana watsa masa a jiki tana zaginsa." Hakkim yaji kamar zuciyarsa zatayi bundiga wai wannan yarinyar wace irin ibilishiya CE ne? Yake fada cikin zuciyarsa. Wayarsa ya Ciro da sauri ya fara Neman numbar Dadyn nasu.General ya dauki wayar da sallama Hakkim din yace." Dady ka futo yanzu ga yarinyar nan a bayan layi na ganta zata gudu." General ya aje wayar da sauri! Ya mik'e Hjy Asiya tace." Wani abun ne ya faru."? Cikin fada yace." Garin yaya kika bari Aminatu ta futa amanar da kika d'auka kenan." ? Hjy Asiya ta mike tsaye da sauri tace." Yarinyar da suke daki ita da Salima Yallab'ai. " futa yayi ba tare da ya tsaya ya saurari sauran zan can ba. Ita kuma ta nufi dakin Salima hankali a tashe! General yana futa ya hango Hakkim na janta kamar Wanda yake Jan ice ranshi ya b'aci da sauri ya karasa gurin yace." Hakkim mutum fa kake ja a kasa ba dabbah ba." Cike da jin haushi yace." Dady kasan halin kaurin kan yarinyar fa, yanzu ma bakaga yanda take zagina ba. Aikuwa kafin ya rufe bakinsa Ladidi ta dibi kasa ta watsa masa k'asa tare da fadin "Allah ya isa mugu azzalimi sai na rama duk abunda kamin kuma na fasa zama a gidan NAKU." Ta k'arashe maganar muryar ta na karkarwa. Hakkim ya sake ta ta fad'i a gurin aikuwa da sauri ta mike zata zunduma da gudu General yayi saurin rike hannunta tamau!! Sai ta soma lauyewa zata fad'i kasa Hakkim ya kalla dake k'okarin shiga gida yace." Zo ka d'auke ta ka shiga da ita ciki Aminatu fitinar ki tayi yawa." Ya fada cike da kosawa. Kukan da take boyewa ne ya kwace mata,kafin kaga Abu yasa ta kuka zaka dad'e. Sosai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39