Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

abuja, domin yana kwad'ayin tayi karatu kuma ta nutsu tabbas hankalin sa ya kwanta da mutumin yasan bazai cuce shi na. Sosai general ya karb'i mai koko fuska a sake yake gaishe ta ta amsa babu yabu babu fallasa tace"Naga kun shirya dama ina addu'ar Allah yasa na tadda daku domin tun jiya jikina yake bani da akwai wata a k'asa." General yace." Hak'ika Iya kina da gaskiya kuma maganar cewa za'a b'oye miki sam! bata taso ba, jiya mun Dade da D'alha a waje muna tattsunar maganar . Nan duk ya kwashe komai ya fada mata. Mai koko tace" Kun munafur ce ni Alhaji, ina ganin mutumncin ka, Wallahi wato dama da biyu kace dole sai ta zauna a gidan ka ko domin Ku cusa mata k'in zama cikinmu ai babu komai, Alhaji ga amanar Ladidi nan a hannuku marainiya ce,duk Wanda ya cuceta shi da Allah." Ta k'arashe maganar muryar ta na rawa. General bai ji dadin kalaman da Mai koko tayi amfani dasu ba gurin fada masa magana amma domin a zauna lafiya yasa ya dinga lallab'ata hade da rarrashin ta, cewar ta kwantar da hankalinta yayi mata alk'awarin duk wata zai dinga sanyawa ana kawo ta suna gaisawa. Ba tace komai ba ta mik'e ta fuce daga parlor zuciyar ta babu dad'i, Hjy Asiya ta biyo bayan ta tana yi mata magana mai koko ko juyo wa ba tayi ba, babban abunda ya bata shaushi ganin yanda Ladidi taki kallon inda take balle ma tayi mata magana. Tana komawa gida ta Tarar da D'alha ya futo zai tafi gurin sana'ar sa, nan ta rufe shi da fada tana share hawaye tana fadin"me yarinyar nan ta tsare maka ne ? Ka dauke ta ka bada ita hannun mutanan da baka sani ba." D'alha ya tsaya yana fahimtar da ita, kin sauraron sa tayi ta shige cikin gidan ranta a bace.! Futa yayi kawai yasan duk maganar da zai fada mata yanzu ba sauraransa zata yi ba, dole ya bari ta huce tukkuna sai yayi mata bayani yadda zata fuskarta. ******* *LADIDI A ABUJA* Tunda suka isa birnin tarraya take kalle-kalle cike da k'auyanci gine-gine take kallo iri-iri Salima ta tab'o da hannunta tace"Salima kuma wannan dogwayen gine-ginen basa fad'owa kan mutane." Salima tayi murmushi tare da fad'in"Amanatu kenan, duk haka ginin garin yake, babu kuma Wanda zai fad'o." Ladidi tayi shiru cikin motar zuciyar ta fara zugata da tasani bata biyo su ba tabi Iya wata kila ma zasu siyar da ita ne, hawaye ta fara sharewa cike da tausayin kanta, Salima tace"Kuka kike Amina." Fuskarta ta b'oye tsakanin k'afafun ta,General ya juyo da sauri tare da fadin"Kukan me takeyi Salima." Tace" Wallahi ban sani ba Dady." Salim ne yasa dariya tare da fadin "ko ta tuno gida ne"? Hjy Asiya tace" Salim kar ka kara yi mata dariya " gumtse bakinsa yayi yace." Toum, Hjy ASIYA ya juyo tana rarrashinta da kyar tayi shiru, suka Isa gida. Ganin mai gadi na bude wani wangameman get yasa Ladidi ta tsorata ganin doguwar kanta kewaye da kayoyi lokaci guda zuciyarta ya fara sak'a cewar in tayi sha'awar futa wasa ta ina za ta futa, bata k'ara tsinkewa da al'amarin na sai da taga wasu manya-manyan sojoji guda uku ko wanne hannunsa rike da budinga sun taso daga gurin zaman su, suna wa General barka da zuwa. B'uya tayi bayan Hjy Asiya tana zare idonta, nan Salima taja hannunta suka shige ciki. Tunda suka shiga parlor take bin ko ina da kallo gaskiya haduwa lparlor ya kai ya kawo wasu tafka-tafkan hotona ne kafe a hango uku general ne da iyalinsa, sai kuma nashi shi kadai yana sanye da kayan sojoji Jikinta yayi sanyi ta kalli Salima tare da fadin"Dama Baba soja ne."? Salima tace" Eh amma ritaya shekaru biyar da suka wuce. " shiru tayi tana kara bin parlor da kallo can ta hango wani tafkeken hoton Hakkim jikin bango Yana sanye da wasu suit Wanda suka yi masa mugun kyau dariya yake yi lokacin da aka dauki hoton tsantsar kyawun shi gami da haibar shi ya sun futo da alama ma hoton na anan aka dauke shi ba, kamar a k'asar waje ne................ *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ *5/November/2019* ^^^°^^^^^^^^^^^^^^^^^^ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿34* Jikinta a sanyaye ta zauna kusa da Salima, a lokacin idan ka ganta baza ka tab'a cewa Ladidi ta Mai koko bace saboda yanda ta koma kalar tausayi duk babu wannan rawar kan da ta saba. General da Hjy Asiya suka shigo palo bakin su dauke da sallama, mai aikin gidan ce ta futo daga kicin da sauri tana yi musu barka da zuwa. Hjy Asiya ce kawai ta saurare ta tuni general ya hau sama, jikinshi duk babu dad'i wanka kawai yake son ya yi. Baito mai aiki ta kalli Ladidi tana washe bakinta tace"Hjy bak'uwa muka samu ne." ? Hjy Asiya dake kokarin hawa sama tace"E gatanan bak'uwa ce kuma 'yar gida." Baito tace"Masha Allah yarinya kyakyawa da ita gata 'yar Fulani, ya sunan ki."? Baki na rawa tace." Sunana Ladidi." Salima tace"Daga yau ba sunan ki Ladidi ba, sunan ki Aminatu." Baito tace"Suna me daraja sunan mahaifiyar Annabi MUHAMMADU (Slw)." Ita dai Ladidi shiru tayi kawai tana satar kallon hoton Hakkim dake mak'ale a bango.. Take wani irin fargaba da tsoro suka shige ta, Sai hawaye sharrrr! Suka fara biyo kumatun ta. Salima tace"Kuka kike yi Aminatu." ? Mik'ewa tayi zumbur!! Ta kama hanya zata futa." Baito ta matsa gefe ganin tana k'okarin buge ta. Salima ta mike da sauri tana k'okarin rike hannunta LADIDI ta fuzge hannunta tana kokarin futa.. Cikin sauri Salima ta kara rike hannunta, wata irin bangaza tayi mata sai ga Salima a k'asa, Ladidi ta bude kofa ta fuce da gudu. "Momy"!!! Salima ta kwalawa Hjy Asiya kira, da sauri Hjy Asiya ta sauko jin irin kiran da Salima ta kurma mata fad'i take " Lafiya kike kurma min uban kira haka."? Baki na rawa tace" Amin.... Kafin ta karasa Hjy Asiya ta katse ta da fad'in",Tana ina."!? Da hannunta ta nuna kofa tana fad'in"Ta futa da gudu." Cikin sauri Hjy ta bude kofar parlor ta futa tana salati. Can ta hango Ladidi bakin gate suna rigima da masu gadi, sai kuka take tana burgima a kasa wai dole sai sun bud'e mata k'ofa. Tun daga nesa Hjy Asiya take fad'in"Kar Ku Bari ta futa duk Wanda ya bar ta ta futa a bakin aikin shi." Jin abunda Hjy take cewa ne yasa Ladidi zabura! Ta buga wani uban tsalle! Sai gata ta d'are gatangar dake kewaye da gidan, duk da cewa

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39