Chapter 17
Chapter 17
saki yayi taga-taga zai fad'i, da sauri ya dafe towol d'in jikinsa da yake barazanar fad'uwa k'asa, saboda sanin halin da yake ciki shi kadai ne a jikinsa, gwiwar sa ya sanya a gurin ya sanya hannunwa ya dafe k'asa sai cije baki yake, idonsa ya kad'a yayi ja, jini kuwa duk ya b'ata gurin. Kan gadon ta hau tayi tsaye tana kallonsa, Tace." Naji dad'i na rama abunda kayi min gaba ma sai ka k'ara dukana kaga abunda zanyi maka." Tana gama maganar ta ta dura k'asa, bude kofa tayi ta futa daga d'akin, Salima da Yusuf na tsaye harabar gurin suna jiran futowarsa kawai sai suka ganta ta futo,bagaz-bagan! ta wuce fuuuuu! tamkar zata tashi sama! Cike da tsoro Yusuf ya shiga ciki,Salima kuwa kin shiga tayi,domin ba k"aramin tsorata tayi ba, ita kam da tasan wannan masifar zata gani da bata biyo su, ba k'afafunta sai rawa suke ta nemi guri ta zauna,cikin zuciyarta take cewa gaskiya gurin nan akwai aljanu insha wata k'ila Dady bai sa anyi saukar alk'urani me girma a gidan ba. Cikin jarumta ya mik'e tsaye da sauri ya bi bayanta,yana jin in ya kama yarinyar nan to sai dai idan uwarta ta haifi wata domin har in bai kashe ta ba to sai yayi mata muguwar illah a rayuwarta, wani irin suka da azaba! Tafin k'afafun shi suke yana jin shigar kwalbar jikin jikinshi bai damu ba, bud'e kofa yayi a fusace! Suka ci karo da Yusuf ya shigo a razane! ganin fuskar Hakkim d'in babu rahama ko kad'an, yasa ya duburburce yace." Yaro wai meke faruwa ne,waye ya futa yanzu mace ko namiji? naga yaro ya futa yanzu, ina cikin rud'u fa,anya gurin nan babu aljanu kuwa." Shiru yayi masa cikin k'arfin hali ya nufi kofa da niyyar futa. Yusuf ya bishi da kallo yana kallo yadda yake Jan k'afa ga jini duk ya b'ata gurin, da sauri ya bishi ya dafa kafad'ar shi,yana fad'in." Wai ina zaka ne cikin wannan halin."? A hasale yace." K'yaleni malam." Yusuf yaje ya rufe kofar futa da key ya zura a aljihun sa, yace." Babu inda zakaje sai ka fada min abunda yake faruwa, yanzu fa na futo daga d'akin lafiya Lou amma dubi wani abun al'ajabi. " yace." Zo ka bude min kofa." Yusuf yace." Bazan bude ba wallahi." Wani uban naushi! ya kaiwa kofar da hannuwansa yana fad'in." Yusuf wallahi suma tallahi idan idona ya k'ara ganin yarinyar nan, to ina me tabbatar maka da cewar sai dai uwarta ta haifi wata,wallahi duk shad'aicin ta,sai naci ubanta sai na ragargaza ta, ni zatayi hakaaaaa."!!!!!! Salima na daga waje ta ji ihun Dan uwanta a tsorace ta fara buga kofar tana kuka, Yusuf ya bud'e mata ta shigo yayi saurin mai da kofar ya rufe, cikin mawuyacin hali taganshi tace." Babban yaya waye ya zubar maka da jini? Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Sai ta kara rurucewa da kuka. Yusuf ya rasa ma abunyi yace." Yanzu dai muje hospital ayi maka dressing d'in ciwon nan,in yaso ko ma meye sai ya faru, ni wallahi kaina ya kulle ma." Salima tace." Ya Yusuf fada sukayi ne." ? D'aga mata kai yayi ya nufi bedroom domin dauko masa kaya, to duk irin tambayoyin da Salima take masa yak'i tanka mata, yana durkushe sai sakin ajiyar zuciya yake ta b'acin rai! Da cin alwashi kan Ladidi. Wata razananniyar tsawa! ya buga mata tare da fad'in "Tashi ki bani gurin idan na fada miki waye me zakiyi, ne kin dame ni." Salima ta mike da sauri taja gefe cike da tsoro take kallonsa ganin yanda duk hallitunsa suka sauya. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿17* Yusuf ne ya katse masa tunanin da take. Yace."Ka tashi ka saka muje hospital, ko sai na taimaka maka ne."? Da k'arfi ya fuzge! kayan da ya ke mik'o masa, ya mik'e da kuzari ya fara sanyawa zuciyarsa nayi masa zafi da radadin gami da takaicin abunda Ladidi tayi shuka masa. Yusuf yayi gaba yana fad'in." Bari in matso da mota kusa." Ko kallonsa baiyi ya fara d'ingisawa Salima tabi bayansa simi-simi. Cikin gari suka futa suka nemi wani pravite hospital, nan akai masa dressing sosai suka had'a masa magunguna masu kyau da tsada, Wanda in yayi amfani dasu insha'Allah zai samu sassauci. Hanyar su ta dawowa suka tsaya suka siyi abubuwan da basu dashi, Salima ta kalli Yusuf a tsorace tace." Ya Yusuf nifa ina jin kwana biyu ko uku zanyi in koma gida wallahi tsoro nake ji." Yusuf ya fashe da dariya har da dukan kan mota yace." Nima ai munyi d'aya dake gaskiya tafiya zamuyi tsakanin jiya da yau mun sha fargaba mu da muka zo Hutu mun b'ige da jinya, ga tashin hankalin wannan yarinyar." Hakkim ya ja tsaki! yace." Wallahi babu inda zaku je,ni kadai na shirya tafiya ta,saboda gulma da munafurci kuka ce dole sai kunzo, mussaman ke." Ya fada yana kallon Salima da ta sunkuyar da kanta ya cigaba da cewa "har da kuka sai kinzo saboda haka dole ku zauna sai sanda naga damar tafiya sannan." Yusuf yace." Ni indai tani ne babu matsala Salima ce abun ji." Aikuwa ta marairaice fuska, Yusuf ya dinga mata dariya yana tsokanar ta da daddare zata ga Ladidi a kusa da ita tazo taya ta kwana aikuwa duk ta gigice. da wannan suka Isa, Hakkim ya futo daga mota yana kalle-kalle wai ko zai ga Ladidi,duk suka shige suka barshi a gurin, daga bisani ya bi bayansu yana d'in gisa k'afafu. ********* Ladidi kuwa tunda ta samu ta d'auki fansar abunda Dan burni yayi mata sai kawai ta manta dashi da al'amuran shi ta cigaba da sabgarta. Tafe take fakam-fakam da allo a hannunta ta cire d'ankwalin ta taci Uwar d'ammara dashi, tana sane ta cire ko wani zai tsokane ta ta samu na duka, bayan haka kuma tana so ta b'akantawa Kawun ta D'alha rai tunda ta lura baya so ya ga tana yawo babu d'ankwali, shi kanshi hijab dinta na hannuta, karo suka ci da Iliya dai-dai wani lungu, Tun daga nesa yake k'unshe dariya, har ya k'araso daf da ita, taki kaucewa tamkar zasu bangaji juna, Iliya ya sha kunu ya d'an kauce mata tazo ta wuce, shima kamar zai wuce sai ya tsaya ya mik'a hannusa ya daki! kanta sosai yace.' Woooo k'waryar malo dama a namiji aka hallice ki domin kin fi kyau da maza!yana gama fad'ar haka ya runtuma da gudu yana dariya, aikuwa a sittin! Ta bishi da wani irin mugun gudu kamar zata tashi sama, yana gudu yana waiwayen ta,ganin ta kusa cimma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39