Chapter 31
Chapter 31
sha kwalliyar fuska leb'anta jazur da Jan janbaki babu yanda Salima bata yi da ita ba kan kar ta sanya sai da ta saka, ta zabga jar hoda fuskarta tayi fururu!! Kauda kansa yayi yana Jan tsaki! Salim ya sunkuyar da kansa yana kunshe dariya. General yace. " Aminatu wannan kwalliyar fa." Washe baki tayi tace." Yanzu nayi tayi kyau ko." Yace." Kinyi kyau mutuka amma ke Salima gyara mata hodar fuskar tata zata fi kyau." Salima ta fara goge mata fuskar nuna wa tayi bata so don sai kauda fuskarta take. Hjy Asiya tace." Rabu da ita kawai tunda bata so." Suna zama kan kujearar daining din ya mik'e hannunsa rike da cup din tea ya wuce can parlor had'e da zama kan kujera yana ya mutse fuskarsa kamar Wanda yaga kashi. gurguje Salima ta had'a musu breakfast suka karya General ya mik'e yana duba agogon hannusa yace." Ku tashi mu tafi. Salima da Ladidi suka mik'e da sauri suka futa waje Salim ya mik'e Yana fadin "Dady bari inzo inyi draving d'inku tunda big broth zai tafi.. General ya kalli Yusuf da ya futo daga daki cikin shiri yace." Kai yau zaka koma ne."? Yusuf yace." Eh Dady." Gyda kai kurrum general yayi yace." Wato ya sauya maka ra'ayi kenan.". Murmushi yayi tare da fadin "ba haka bane Dady" wuce wa yayi yana fadin" Nayi karya kenan, Ku sauka lafiya." Yana gama maganar shi ya futa Salim ya rufa masa baya. Hajy Asiya nayi masa adawo lafiya. *30/October/2019* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ ________________________ *1/NOVEMBER/2019* ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿32* Wannan karon Ladidi ba tayi hauka a hospital ba tsaf ta tsaya dector ya duba ta sosai yayi mata wankin kunne kamar yanda ya fad'a jiya, nan sukayi sallama da general, cikin mutum ci da mutuntawa suka dawo gida, lokacin Hakkim da Yusuf sun Dade da barin garin, general yace." Gwara da ya tafi domin ina ganin zaman sa a gidan zai iya sanya wa Aminatu ta gudu kamar yanda ta fara yunk'uri guduwa da farko." Ita dai Hjy Asiya lallaba Ladidi kawai take kamar yanda mijinta ya umarce ta, bayan sallahr la'asar ne Mai koko ta iso gidan cikin walwala da sakin fuska Hjy Asiya ta karb'e ta lokacin general ya shiga cikin gari domin gaisawa da tsoffin abokansa, Ladidi ta dinga ihu!! Tana murna ta rungume mai koko tana fad'in"Iya kin ganni ko dubi kayan jikina Iya wallahi ina son zama da mutanan suna da kirki, don Allah ki barni a gurin su." Mai koko tace" Ai kya bari mu gaisa tukkuna kafin ki fara yi min wannan sangar ta taki ko." Ladidi ta zauna kusa da ita sai washe baki take ta fara gaishe ta. Mai koko ta amsa fuska a sake tace"Dole ne ki so zaman gidan nan tunda kin samu tv da vedio amma ni kam babu Wanda zan iya barwa ke Ladidi ." Ladidi ta b'ata fuskarta kamar ta kurma ihu!! Hjy Asiya tace" Tunda tana son zama damu Iya muna Neman alfarma ki bamu ita don Allah mu tafi da ita can abuja mana." Mai koko ta bude baki cike da mamaki tace." Habuja fa kika ce Hjy? Kina nufin in baku Ladidi Ku tafi da ita yaron ku ya k'arasa ta, shi da naga bashi da imani, ba da ban Allah ya kiyaye ba da tuni ya kurmantar da ita, Hjy kuyi hakuri bazan iya ba." Ta k'arashe maganar ta tsakanin ta da Allah. Girgiza Kai Mai koko tayi alamun bata amunce ba, Hjy Asiya ta kalli Salima dake zaune kan kujera da waya a hannu tace"Salima kawo wa Iya ruwa da abunci." Da sauri Mai koko tace"Alhamdullahi Hjy a koshe nake wallahi." Hjy tace"A'a Iya dole ki ci wani abun kam ai ko ruwa kyasha." Shiru mai koko tayi tana addu'ar kar Allah yasa Ladidi ta tubure mata kan abunda ta fad'a, jiya ma kwana sukayi suna Abu guda ita da Dalha domin ya fad'a mata yanda suka yi da General, tace masa bata amince ba, ko da wasa kar ya kuskura ya amsa masa. Ganin take taken Ladidi ne yasa Mai koko mik'ewa tana niyyar tafiya Ladidi tak'i kallon inda take sai zumb'ura baki take." Mai koko ta rik'e hab'arta cike da takaici take fadin". 'Yar nan kar dai da gaske take." Bata da me bata amsa, don haka sai ta nufi hanya futa Hjy Asiya ta mik'e da sauri tayi mata rakiya har waje. Salima ta kalli Ladidi a tsanake tace"Idan fa kina so ki shiga birni dole ne duk wannan shashanci ki daina ki nutsu ki daina k'auyanci da rawar kai shima na tabbatar da cewa rashin kamun kan da kike yi ne yasa bakwa shiri da big brother, idan kika kama kanki zaki ga kowa yana son yin mu'amula dake." Ladidi ta kalleta a nutse tace"kina nufin idan na daina magana yayan ki zai dai na hantara gami da ce min aljana." ? Salima tace"K'warai kuwa Big brother ya tsani k'azanta da rashin kamun kai, ki nutsu zaki ga ya daina hantarar ki." Shiru Ladidi tayi tana sak'e-sak'e cikin zuciyarta. ******* Yau kwanan Ladidi biyar a gidan gona kullum ta wanke goma ta tsoma biyar ta ci abunda ranta yake so ta sha abunda ranta yake so, dodon ta baya gidan shiyasa take sakewa tayi kallonta son ranta, duk sai a tashi a barta a parlor ita kadai.domin kar ranta ya b'aci yasa general yake k'yaleta, ta more saboda ya fuskanci yarinyar dole sai da siyasa. Yau ne Ladidi ta gama shanye magungunan ta kuma Alhmdullahi jin ta ya dawo rad'au! DOMIN har har yaso yafi da. A yau ne kuma Mai koko ta dira a gidan da niyyar tafiya da ita. *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ ^^^^^^^^°^^^^^^^^^^^^ *3/November/2019* ^^^°^^^^^^^^^^^^^^^^^ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *WANNAN PEGE D'IN NAKA NE ABUE SALEH ZAMANI WRITARS, ALLAH YA K'ARA MAKA HIKIMA DA AZANCI* *33* General yana ganin Mai koko yasan da abunda tazo, shi tun jiya sun gama magana da D'alha ya yardar masa ya tafi da Ladidi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39