Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
Download Book

sai cin magani yake, Dady yayi k'wafa yana girgiza Kai cikin zuciyarsa yace." Zakaci malafar ubanka ne yaro." Yace." Ka shiga kayi driving domin babu wani direba da zan d'auka. " zuciyarsa babu dad'i ya shiga motar gami da kunna ta, suka futa daga gidan. ******** Hankali Mai koko bai k'ara tashi ba sai da taga tana yiwa Ladidi magana tana shiru tamkar bata ji ba,sai ta d'aga murya sosai sannan take amsa mata, tace." Oh! ni 'yarnan Allah yasa wannan mugun mutumin bai lahanta miki kunne ba." Jira kawai take D'alha ya dawo domin tafad'a masa hankalin ta yayi mugun tashi, duk da ta gaggasa mata jiki tare da shafe mata jiki da Robb hakan bai hana ta cize baki ba,daga an tab'ata zata kurma ihu!! Jikinta duk ciwo yake. D'alha ya dawo a gajiye ya Tatar da wannan tashin hankalin ,Iya ta kwashe komai ta fada masa hankali sa ya tashi shima ya kwatanta kiran Ladidi shiru sai da ya d'aga murya sannan taji shi, nan ya k'ara tambayar ta abunda ya faru, tana kuka ta warware masa komai. Shikam bai yadda ba yafi yadda da cewar wani abun tayi masa shine shi kuma ya mata wannan dukan, tunanin mafuta kawai yake, d'an jarinsa bai taka kara ya k'arya ba shi zai rusa dole ya kaita asibitin burni a duba mata kunnuwan ta, tun kafin Abu yayi tsanani, dama asibitoci suna kuka dasu mutanan k'auye cewa basa tashi zuwa asibiti sai sunga cuta tayi tsanani, shikam baya fatan haka. ****** Gudu yake shararawa General ya buga masa tsawa! tare da fad'in." Ka jamu a hankali ka kaimu ko muma za ka gwada mana zafin zuciyar ne, sai faman gudu kake damu a mota kamar Wanda zai bar gari." Hakkim ya rage gudun da yake, yana jin wani daci a zuciyarsa wai yau shi Dady yakewa tsawa kan wata bare yarinyar da bai sani ba, kwata-kwata ya kasa fahimtar shi, fad'a sosai General ya dinga yi masa har suka Isa Kano bakinsa baiyi shiru ba, Hakkim duk ya koma kalar tausayi saboda abunda bai saba ne, Yusuf ne dinga bawa Dady Hakuri,shima Yusuf din ya samu rabonsa, sai yaja bakinsa yayi shiru cikin zuciyarsa yake cewa" da alama allurar soja ce ta motsawa Dady. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿21* Sai bayan sallahr magariba suka isa K'auyan D'an kunkuru, Dady ya futo daga mota yana hamdala ga Allah, gurin yake bi da kallo sosai yayi kyau ya k'ayatu haske fitila ko ina,nan ya jagoran ce su suka shiga ciki domin su samu nutsuwa suyi sallah, in yaso ko meye sai ya biyo baya. Sallolinsu sukayi suka ci abinci, Dady ya kalli agogon dake manne a bangon farlon takwas da rabi na dare, ya kalli Hakkim da fuska a turb'une yace.'" Yanzu dai ka huta sai ka tashi ka fara laluben inda yarinyar mutane take domin inyi abunda ya kawo ni garin." Ya d'ago kanshi dake sunkuya yace." Dady dare yayi yanzu ga hanya babu kyau ga yanayi na damuna gari duk ya jike kayi hakuri sai Gabe." Tsawa! Ya buga masa tare da fad'in." Bana son wata banzar magana ka tashi ka fara laluben yarinyar nan da halin da take ciki." Mik'ewa yayi da sauri Yusuf ya mike shima suka futa tare. Dady yace." Ai ka jawowa kanka tunda kai kace me kunnen k'ashi ne." Cikin d'ari-d'ari Hajiya Asiya tace." Ayi hakuri Yallab'ai." Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da girgiza k'afarsa guda. Tsaye suke a harabar gurin suna shawarwarin me za suyi. Hakkim ya nufi gurin masu gadi jikinsa duk yayi sanyi fad'an Dady ta soma damunshi, Sam! bai saba ba. Suna ganinshi ne suka nutsu nan ya k'arasa gami da mik'a musu hannu suka gaisa a mutunce. Sai ya rasa me zai ce. D'aya daga cikinsu yace." Akwai abunda za'ayi ne Oga."? Girgiza kai yayi alamun a'a yace." Tambayar ku kawai zanyi." Sukace Allah yasa mun sani. "Wata yarinya siririya nake tambaya zaku ganta fara 'yar fulani k'azama yarinyar bata da kintsi tana tafiya kamar mahaukaciya ko kun santa." Shuru sukayi na minti biyu daga bisani suka had'a baki gurin fad'in." Gaskiya ba mu gane yarinyar ba domin kasan yaran K'auyan nan suna da yawa kuma dai duk haka d'abin ansu yake na rashin kintsi." Yusuf yace." Ko d'azu ma ta wuce ta nan wajejen k'arfe goma na Safiya, ko gilmawarta baku gani ba." ? Nan suka ce Sam basu gane taba. Cike da jin haushin su Hakkim ya futa waje yana kalle-kalle Yusuf yace." Bari in d'auko mota mu nausa ciki ko za'a dace." Shiru yayi masa kawai ya soka hannuwansa duk biyun cikin aljuhu. Yusuf ya futo da mota ya shiga suka kama nausa cikin karkarar ba tare da sun san ina zasu je ba. Ganin mota tana shigowa ne yasa matasa da suke zaune Suna shan rake tsakiyar su futalar aci bal-bal ce sai hayaki take suna ta hira da shewa duk suka bi motar da kallo. Yusuf yace." Ina ganin mu tsaya mu tambayi matasan can." Parking yayi suka futo a tare matasan suka bisu da kallo. Cikin nutsuwa suka k'arasa kusa dasu duk suka basu hannu sukayi musabaha. Yusuf yace." Muna tambaya ne." Sukaje Allah yasa mun sani." Shiru yayi domin ya rasa da yaya zaiyi kwatan Ladidi. Hakkim yaja tsaki yace.' Ka fara magana kuma kayi shiru, muna tambayar wata ibilishiyar yarinya a garin nan, ita ba mutum ba ita ba'ajana ba siririya tamkar tsolan rake, zaku ganta k'azama tana da manyan idanu." Shiru sukayi na minti biyu daga bisani sukace ."Gaskiya bamu gane taba, sai da Ku k'ara shiga cikin k'auyen ko za'a dace." Ko gama sauraransu baiyi ba yayi gaba ya bud'e mota ya shiga Yusuf ya biyo bayanshi shima duk ya sare da al'amarin. Har ya kunna mota zasu tafi, d'aya daga cikinsu ya taso da sauri yana fad'in." Ku tsaya Ku tsaya." Hakkim yace." Dallah ja mota mu tafi ya Wani taso yana mu tsaya mybe ma yayi mana shirme." Yusuf ya share shi kawai ya kashe mota, saurayin ya k'araso yana fad'in." Ina kyautata zaton yarinyar da kuke magana akanta baza ta wuce Ladidi ba, domin duk siffofin daka fada ita take dasu." Yana daga cikin mota tace." Shigo ka kaimu gidansu." Da sauri yaja baya cike da tsoro, chaiiiii! Akan me zai shiga motarsu ya sani ko 'yan yankan kai ne, Karin abun damuwar ma Ladidi suke nema, tabbas yasan abun babbane. Ina-inda ya fara da k'yar yace." Yanzu dare yayi zani gurin iyalina,amma bari in yi muku kwatance." Yusuf yace." Ok muna jinka." "Idan kuka mike wannan hanyar

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39