Chapter 30
Chapter 30
take kuka General ya tsuguna yana rarashinta ta tubure ita baza ta koma cikin gidan ba kawai ya barta ta tafi gidansu. Umarni ya bawa Hakkim ya d'auke ta ya shiga da ita, babu yadda ya iya ya tattare hannun rigar sa ya fara kokari d'aukar ta ta dinga kawo masa duka da ya kushi yana ji ya naga ni ya sab'ata a kafad'a suka nufi cikin gidan. Ladidi ta dunga dukansa bayansa da gwiwar hannunta tana cizo da ya kushi gami da yi masa Allah ya Isa, shi ko duk yana jinta yana jin kamar ya jefar da ita a gurin amma babu halin yin haka tunda umarnin dady ne. Shi kansa General ya ji haushin abunda yarinyar take yana ji kamar ya kaude ta da mari yarinya me baud'ad'an hali in ka taro ta can sai ta baud'e ta tafi wani guri. Lallai yanzu ya soma ganin halinta. Tsakiyar parlor ya aje ta ya juya ba tare da yace da kowa komai ba ya fuce daga parlor. Hjy Asiya ta k'araso inda Ladidi take tana rarrashinta tare da tambayar ta abunda aka yi mata, kuka kawai take taki cewa komai. General ya kalli Hjy Asiya tare da fad'in" kunna mata kallo ki sanya mata film na fad'a." Aikuwa da sauri ta kunna tv India film ta d'auko ta sanya a DVD film din fassarar Hausa ne na jarumi akshey kumar,,, kafin mintu goma film ya fara d'aukar zafi can na hango ladidi ta warware ta kamar ba itace take kuka da turje-turje ba ta zubawa TV ido tana kallo fuskar ta a sake har ta manta da guduwa gidan mai koko. Hjy Asiya ta kalli mijin NATA tare da girgiza kanta tace." Anya kuwa yarinyar nan bata da matsala a kwakwalar ta."? Numfashi ya sauke ya zauna gefan ta yace." Lafiyan ta lau wallahi kin San wasu yaran haka k'uruciyar su take sai sun girma sannan hankali yake zuwa Kansu kuma kin San dama dab'iun mutanan k'auye dana birni ba d'aya suke ba." Tace." Ko dana ji iya sanina dai babu abunda akayi mata Wanda zai tunzura zuciyarta da har zata ce zata gudu gida, domin shi Hakkim ma tunda ya futa d'azu be shigo parlor ba balle in ce ko shine tunda da shine basa shiri." *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *30/October/2019* ________________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿31* General yace." Dole ki dinga saka ido a kanta saboda amana aka bamu har sanda zata gama shan magani ta koma gurin iyayen ta." Hjy Asiya tace." Insha Allahu zan kula wallahi yanzu ma ban San ta futa ba." Nan kusa cigaba da hirar da ta shafe su, Ladidi kuwa nacan tana kallon tv yayin da Salima take kwance kan kujera tana chat babu ruwanta da wani kallo tunda bai dame ta ba. Goma shaura general ya kalli ladidi yace." Aminatu ya kamata ki kwanta haka saboda gobe ki tashi da wuri zamu je kiga dector ko."? Zumb'ura baki tayi tace." Sai na gama kallona." Salima ta kalli tv din tace." Film din nan fa da saura Dan sai kin kai kusan sha d'aya da rabi na dare a zaune a gurin nan sannan zai kare." General ya mik'e yana fadin "Rabu da ita Salima ta gama kallonta ke dai ki bar dakin a bude kar ki rufe kofa." Yana gama maganar shi ya wuce bedroom Hjy Asiya ta bishi, to Salima ma minti ashirin ta kara ta mike ta shiga bedroom domin kwanciya, aka bar Ladidi ita kadai a parlor.... Sha d'aya saura Yusuf da Salim suka shigo, cike da mamaki suke kallonta, ganin irin kallon da suke matane ya bata haushi tace." Meye! Kuka zuba min ido." Shiru sukayi kawai domin suna iya magana ta sanya ihu ransu ne zai b'aci in Dady ya ji, wani daki suka shige dukaninsu suna mamakin rashin kunyar yarinyar gami da k'arfin halinta Sha daya da kwata ya shigo shima ya gaji mutuka bacci kawai yake so yayi, yana shiga parlor yaga Ladidi tsaye gaban Tv tana dariya kamar mahaukaciya tv ya kalla da sauri sai yaga jarumi Akshey kumar yana dukan boss da alama film din yazo k'arshe. Ladidi sai ihu! Take tana fad'in"Yawwa! Kashe shi! Hege! Mugu dama bashi da wani amfani"!! Takaici ya hana shi cewa komai kawai ya nufi gaban tv romt ya d'auka ya kashe TV ya zare wayoyin daga jikin soket din. A zabure!!! Ta kalle shi! Sai kuma ta ja da baya ganin Hakkim din ne. Bude baki tayi zata yi magana yace." Wuce! Kije ki kwanta mahaukaciya kawai." Ladidi takaici kamar ta Dora hannu aka gashi ana fad'an k'arshe wannan Dan rainin hankali yazo ya kashe TV kamar zata yi kuka tace" ka kunna min in karasa gani,." A fusace! Yace." An ki a kunna miki Dan uwarki ibilishi dak'ikiya wacce bata sa komai a gaba ba sai dakikanci da jahilici." Tunda take a rayuwa babu Wanda ya tab'a yi mata zagin cin mutum fi irin na yau. Ta fara sanin ciwon kanta tana a matsayin shekaru goma sha uku.yanzu idonta ya ciko da kwallah sosai. Tsawa! Ya buga mata akaro na uku yace." Kin bar nan gurin ko kuwa sai nayi kulikulin kubura dake yanzu." Da gudu ta shige dakin da Salima take tana wani irin kukan taki. Shiko wani sanyi yaji cikin zuciyarsa ganin ya sata kuka dama abunda yake so kenan, duk irin b'acin ran da ya kunsa daga gurin Dadyn sa, sai ya fanshe a kanta, d'akinsa ya nufa zuciyarsa babu dad'i. Misalin k'arfe bakwai da rabi kowa ya hallara a parlor ana shirin karyawa, ya futo cikin shiru fuskar nan a had'e General ya kalle shi tare da fadin "yawwa dama yanzu nake cewa Salim ya shiga ya kira min kai mu tafi hospital din nan da wuri." Zama yayi kujerar daining yace." Dady wane irin hospital ? Ni da zan wuce Abuja yanzu." Wani irin kallo general din yayi masa yace." Yanda muka zo tare to haka zamu koma. tare babu inda zakaje." Ganin Dady din fuskarsa babu wasa yasa ya kwantar da murya cikin laluma yace." Dady kasan sati biyu zanyi in koma America kaga yau nayi kwana Tara da zuwa, ya zama dole yanzu inje in fara shirye-shiryen tafiya ko." Shiru general din yayi masa ya cigaba da karyar warshi hankali kwance. Hjiy Asiya ta kalle shi tare da fadin "ko a had'a maka breakfast din ne." Gyad'a kansa yayi. Had'a masa tayi ta tura masa gabansa, tsatstsakura yayi a je fork din, ya cigaba da kurb'ar tea din ranshi babu dad'i. Salima da Ladidi ne suka futo tare sun shirya tsaf!! Ladidi an
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39