Skip to content

Chapter 35

Chapter 35

Ladidin Kwadage Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

yimin maganar mahaukaciyar yarinyar nan sai na ballaki! Wallahi Idoit kawai !.""" Yana gama maganar shi ya fuce a fusace! Salima tayi tsuru-tsuru tana bin hanyar da wuce da kallo ita kanta tana jin tsoron masifar yayan nasu hade da b'acin ransa, lallai yau zuciyar sa a tunzure ta, tana ganin ko Dady ne yayi masa magana zai iya fada masa magana me zafi indai akan LADIDI ne. *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ ```Shugabar mataye Binta taga mala'ika da idonta, ba shamaki ba tafinta, har ya aike ta gun Habibi``` *Fad'ima Umul Hasnaini ya tsokar jikin Habibi* ______________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* *BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM* *πŸ…Ώ39* Cike da rashin tsoro general ya tsuguna kusa da Ladidi dake wani irin Abu da idonta, yace." Kuji tsoron Allah da manzo sa ku rabu da wannan 'yarinyar marainiyar Allah me tayi muku? Kuka yi aure kuka tare a kanta, shine me zaku cewa ubangji ranar alkiyama."? "Hahahahaha!! Suka ji wata mahaukaciyar dariya, Ladidi nayi, tafi minti uku tana yi daga bisani tayi d'if!! Gurin yayi shiru Lokacin Salima sai da ta saki futsari a wando. Tsoro duk ya cika zuciyoyin su daga ita har Momyn ta Hjy Asiya..... General ya fara tofa mata dukanin addu'ar da tazo bakin sa. Ya kai Kusan 30minutes tsugune gaban Ladidi yana tofe jikinta da addu'a, sannan ta bude idon ta, gami da yin wata irin mik'a! Ta mike zaune zumbur! Kuka ta fashe dashi tana waige-waige a gurin. Su din dai ta gani a tsaitsaye sun zuba mata ido. Take kukan ta ya kara k'arfi tana nuna kafarta duk bakinta yayi mata nauyi so take tayi magana amma ta kasa. General ya fahimci ta dawo dai-dai sai ya fara kokarin daukar ta cike da tausayin ta, domin ya lura aljanun da suke kanta manya ne sosai Dole ta kasa motsa jikinta. Jiki babu k'wari su Hjy da Salima suka bi bayan general Wanda ke rungume da Ladidi a jikinsa ya nufi cikin gidan da ita. Hjy da Salima Dan babu yanda zasu yi da sun hana general shigar musu da Ladidi gida saboda tsaro , Salima tsoron mutum me aljanu take. Kan kujera ya aje ta ya kara k'arfin AC ya kalli Hjy Asiya tare da fad'in ki hada mata ruwan ka tayi sai taci abunci." Hajiya Asiya ta wuce kicin jikinta duk babu k'wari, ita kuwa Salima zama tayi ta k'urawa Ladidi ido babu abunda take tsoro da fargaba sai dare domin tasan Dady zai ce Dole sai ta kwana d'aki daya da Ladidi. Kamar me k koyon magana tace"Zan sha ruwa." General da kansa ya nufi furji ya dauko mata ruwan gora mai sanyi bayan ya bude murfin ya mik'a mata. Tunda ta kafa kanta kan robar ruwan bata d'ago ba sai da ta shanye shi tas! Sannan ta jefar da robar hade da yin wata shegiyar gyasa lumshe idonta ta fara yi, tuni ta b'ingire a gurin nannayaun bacci yayi gaba da ita. General ya saki ajiyar zuciya ganin bacci ya dauke Ladidi ya mike yana niyyar barin gurun, da sauri! Salima ta mike hade da rike rigar shi ta baya tana tafiya tana waiwayen Ladidi. General ya juyo yana kallonta da murmushi a fuskar sa yace." Na lura dake da Momy taki tsoron Aminta kuke yi tun d'azu naga sai zare ido kuke yi." Salima tace."Wallahi Dady da gaske tsoran ta nake ji, yanzu haka jikina a jike yake ban San sanda futsarin tsoro ya kuffe min ba." Dariya general yasa yace." Ho Salima sarki tsoro ki daina jin tsoron Aljan babu abunda ya Isa yayi miki Wanda Allah bai miki shi ba, ke kike da makamai a hannun ki, kina fara karatun ayatul kursiyo sai gudu." Salima tace"Duk da haka dai Dady wallahi tsoro nake ji, mu kam Big broth ya jawo mana, Dady kana jin abunda fa aljanun suke cewa zasu masa, wai sai sun dauki fansar abunda yayi mata." Murmushi general yayi a lokacin da suke taka steps yace." Duk abunda suka yi masa shi ya jawo kanshi babu ruwana. " cikin Salima ya karta!!! Cike da tsoro tace"Please Dady ka basu hakuri don Allah kar su tab'a mana bro." Salima iya Gaskiyar ta take magana. General kam dariya yake mata sosai har suka hau sama, ko wanne ya shige dakin shi. Hajiya Asiya na futowa daga kicin taga parlor babu kowa Sai Ladidi a kwance kan 3sitar wata irin fad'uwar gaba taji, da sauri ta fara hawa step ta waiwayen Ladidi dake kwance General ta samu zai shiga bathroom tace"Yallab'ai gashi ruwa har yayi zafi kuma naga tana bacci a k'asa. " Yana kokarin shiga toilet din yace." Ai bacci shine samun nutsuwar ta, ki k'yaleta tayi kar Wanda ya tashe ta, sai ta tashi Dan kanta. " Hajiya Asiya ta zauna bakin gado tana al'ajabin wannan Abu. ****** Hakkim kam ya manta da wata Ladidi don Ku da suka gama waya da Dadyn sha. Ya fada masa tayi dogon suma bai damu ba, shi tunda ya bar k'asar shikkenan, suje su k'arata su da suka daukota. Wasu had'andun gidaje ne company da suke wa aiki ya raba musu kyauta, plate uku ne shi d'aya Salmanu d'aya Bash d'aya, gidane me girman gaske babu abunda babu na more rayuwa swimming shi kanshi uku ne da gurin motsa jiki uku gurin wassanin yara iri-iri a gurin. Yanda company ya basu gurin zasu iya yin aure su tare da iyalinsu zaman america har a bada su da iyalinsu. Tofa Bash tun da suka je ya samu sake wa ya fara sha'anin shi da 'yan mata kala-kala, shi kuwa Salmanu baya Neman mata amma fa shaye-shaye babu irin Wanda baya yayi, Bash kullum da daddare yana night club, sai dare ya raba yake dawo wa gida, wataran Salmanu yana binsa yaje yayi kallo ya dawo gida a buge. Hakkim ya rasa yanda zaiyi musu kullum Cikin yi musu masifa yake sai dai suyi masa dariya kawai suna fadin "Har yanzu kanshi a tukunya yake bai san yaya duniya take ciki ba. Tunda suka Isa garin na america yau kwanaki takwas kenan wayoyin sa suke kashe, yau ta kama Sunday babu aiki duk suna gida yace bari ya kunna wayar tasa, dama saboda fad'an Dadyn d'insa ya kashe wayar ya San dai yanzu ya huce fushin sa. *24/11/2019* *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€K'WADAGAπŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€πŸ§Ÿβ€β™€* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🀝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* *BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM* *πŸ…Ώ40* Ko da General yaga kiran wayar Hakkim kin dauka yayi. Hajiya Asiya ta shigo ta same shi zaune ga waya nayi tace"Dady kana ganin kiran waya fa." Yace." Ki dauka in zaki dauka yaron ki ne sai Yau ya ga damar tunawa damu. " Hajiya Asiya ta dauki wayar tana fad'in "Ni kam zan dauka mu gaisa dashi." Hararata general yayi tare da fadin" Ke akan 'yaya bakya jin kunya ai." Dariya tayi ta d'aga wayar, b'angaran hakkim kuwa jin muryar Maman shi sai ya saki fuska cikin shagwaba yace." Mama Duk kun manta dani ko? Sai da na gaji don kaina na kira

Table of Contents

Chapters

39 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39