Chapter 15
Chapter 15
zan kawo malamin ruk'iya zai yi mata idan da makarai a jikinta sai a sulhun ta dasu" Shiru tayi na minti biyu, ta d'ago kai tana kallonsa, tace." Ba wai nak'i taka bane, gaskiya ka janye maganar ruk'iyar nan,domin su wad'annan mutane ba a haka dasu, idan kuma basu suka rab'e ta b,kaga sai a jawo mata su da hujja, abar maganar ruk'iya mu cigaba da yi mata addu'a" Dan Fulani da D'alha suka kalli juna, girgiza kai kurum D'alha yake yasan dama Mai koko baza ta yarda ba, shi ko D'an Fulani saboda tsabar haushi da takaici bai sake cewa komai ba. Ya mik'e yana musu sallama, sama-sama Mai koko ta amsa masa, D'alha ya mik'e domin ya raka shi. Mai koko ta dinga rarrashin Ladidi, da lallab'ata tamkar ba wacce tayi mata laifi ba, tace." Tashi ga ruwan zafi can muje kiyi Wanka ko"? Mak'ale kafad'a tayi. Tace." Akwai miyar kifi nan a fulas na aje miki sai ki siyo buredi" Mik'ewa tayi zaune tana Sosa kai tace." Amma ni zanyi wanka na gaskiya" tace." E amma zan cud'a miki baya." Mik'ewa tayi tana tube kayan jikinta ita kuma ta nufi kicin din, bakin rijiya ta tsuguna tana wasa da ruwan Wanka, Mai koko ta k'araso da abun sabulu a hannuta tace."Ladidi waye ya fasa miki leb'e haka? Ko garin tsalle-tsallen ki ne"? Hannuta tasa ta shafo gurin, girgiza kai tayi tace." Wani d'an burni ne, kawai babu abunda nayi masa don zalin ci." "A'a Ladidi nasan halin ki fa"? Iya tafad'a tana murza sabulu jikin soso. " Kawai don na shiga gonarmu shine ya doke ni" "Wace gona kuke da ita Ladidi'? Iya. Ta fada cike da mamaki! " Ranan da zamu wuce Kawu ya nuna min gonar tun kafin a gina gurin yace."Tasu ce da babana." "To yanzu na gane inda kika dosa" Iya tafad'a tana durzar jikinta da soso, ta cigaba da cewa " Ladidi kin cika futuna me ya kai ki gurin nan, yanzu bs gonar su bace, domin sun siyar da ita dalilin haihuwar ki, ranar bakiji Kawun ki yana fad'in wani mai kud'i ya siya har da tasu Malam Tanimu da Manu ba" girgiza kai tayi tace." Ni babu ruwana ko sun siyar ko basu siyar ba, in naga dama zanje ne" Mai koko tace." To sai ki kiyaye domin mutanan burni ba dai-dai suke da na k'auye ba." Zumb'ura baki tayi tace." Aiko sai na rama abunda yayi min ko shugaban k'asa ne ya haife shi." Mai koko dai shiru tayi domin bata so ta tsanan ta mata kar ta sake guduwa. Kawu D'alha kuwa akwai abunda ya k'udura a ransa kan Ladidi. Sai da ya tabbatar da sunyi bacci sannan ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mai koko ya nufa, dama duk ranar da tayi ibilincin ta. To in ta kwanta bacci bata motsawa sai gari ya waye, Mai koko ma bacci take sosai ansha fargaba an gaji, reza ya futo da ita daga cikin aljinunsa ya kwance d'aurin d'ankwalin Ladidi a nutse a shafa sabulu da ruwa ya soma yi mata aski babu abunda ya dame shi. Har D'alha ya gama aske mata kai bata motsa ba, ya mayar mata da dankwalin ta ya daure mata kanta kamar yanda tayi, ya sunkuya ya tattare gashin da zube k'asa ya zuba cikin leda shara ya zuba yasa omo ya wanke hannunsa tass!!! . Ladidi bacci tayi sosai da sosai sam bata san inda kanta yake ba, sai wajan shiga da rabi na safe ta tashi lokacin Mai koko ta Dade da tashi tana can tana hidimar huta huta domin ta d'ora ruwan kuka. D'ankwalin ta take laluba kan shinfid'ar ta d'auka zata d'aura akanta tana tab'awa taji sumul tamkar gwiwa hannuwa biyu tasa tana shafawa, Ihu!! Ta kurma tana fad'in "Wayyo!! Mai koko wani ya aske min kai na" Mai koko ta aje icen dake hannunta da sauri ta nufi dakin. Tana shiga taga Ladidi ta d'ora hannu aka tana kurma ihu! Ga kanta sumul! Babu k'wallin gashi ko d'aya, cikin mamaki tace."Ladidi waye yayi miki k'wal kwabo hak..... Kafin ta k'arasa muryar D'alha ta katse ta inda yake cewa." Iya nine nayi mata aski saboda in cika rantsuwa bayan haka kuma da wahalar da ta bamu jiya, shiyasa na yanke wannan hukuncin a kanta." *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿15* Mai koko tace." To kinji inda maganar take, don haka sai kiyi hak'uri kinji da kunnen ki,wanda ya aske miki kanki." D'alha ya kalle ta cikin taikaci ya buga mata tsawa tare da fad'in."Rufe min baki ko inzo k'ara fasa miki shi,shashasha kawai!! Gum! tayi da bakin ta dama kukan babu hawaye sai dai ihu! Sai dai kana kallon idonta kasan tana cikin b'acin rai! Yarinya 'yar shekara goma sha biyu ta san d'aukar fansa, abunda take ta raya wa kenan cikin zuciyar ta Kawunta da d'an burni sai ta rama abunda sukayi mata. Mai koko ta kalleta ganin yadda take ta sauke ajiyar zuciya yasa ta sassauta murya tace." Yanzu ke kanki zaki ji dad'i kuma iska zata shiga kanki sosai kinga kin rabu da kwarkwata har abada,domin wani sabon gashi ne zai futo miki." Banza tayi mata. Kawu D'alha ya futa ya barsu a d'akin, Mai koko dai da taga tak'i kulata sai ta futa ta k'yaleta tana addu'ar kat Allah yasa ta b'ullo da wani abun kuma. Aikuwa futowa tayi babu d'ankwali a kanta nufi gidin rijiya, 'yan siyan koko suka bita da kallo, tuni wasu daga cikinsu suka fara futa waje cikin tsoro ganin kan Ladidi a cikin rana sai k'yalli yake, Mai koko tace." Ya kuke futa kuma kowa ya tsaya a sallame shi." Wani Yaro yace." Iya wacece wacan kamar Ladidiya ko." Iya ta kalli inda Yaron yake nunawa Ladidi ta gani da buta a hannu tana durzar bakin ta da dakakkaken gawayi kanta sai k'yalli yake cikin hasken ranar da ya fara futowa, cikin takaici tace." Ladidi ke ko kika futo babu Dan kwali ko kunyar k'awayen ki baza kyaji, ki koma ki dauro dan kwalin ki." Kuskure bakinta tayi tace." Daga yau na bar d'aura d'ankwali wallahi haka zan dinga yawo da kai na, kuma duk yaron da ya tsokane ni, inci Ubansa." Jiki a sanyaye Mai koko ta juya ta cigaba da abunda take cikin zuciyar ta take fad'in"Ba a rabu da bukar ba an haifi Habu,dama ni nasan wata futunar zata k'ara b'ullo da ita." Tana gama Alwalar ta bar gurin. Wani tsohon buhu ta kwance nan kayan ta na sawa suke ta ciro wata doguwar riga irin ta kanti duk taji jiki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39