Chapter 4
Chapter 4
raji'un , nono ya rine! Ya koma jajazur dashi, ya kalli Mutari mai nama dake hada-hadar sallamar jama'a yace"Mutari"!!!!! *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/23, 7:47 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ ```Komai yayi tsanani yana tare da sauk'i, cikar muminin mutum yarda da k'addara mai kyau da mara kyau, idan ubangiji ya jarrabe ka, da musiba ka karb'a hannu biyu kar kace wani ne yayi ma, ko da wani mutum ne silar faruwar haka to kasani babu abunda bawa ya Isa yayi face da sanin mak'agin ka, Ubangijin baiwa kenan alimul gaibu washahadati, ka mik'a masa al'amarin da sannu zai yaye maka damuwar ka, Allah kasa mu dace``` _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿4* Da sauri Mutari ya juyo jin irin kiran da Halliru ya kurma masa, baki na rawa yace"Akwai wanda yazo gurin nan bayan naje guri Umaru mai rake yanzu"? Cikin mamaki Mutari yace"Gaskiya babu wanda yazo kan kayan ka ina kallo tun d'azu" Kamar ya fashe da kuka yace"Zo kaga abunda akai min" Mutari ya baro gurin sa da sauri yazo yana dubawa,, salati yasa yana mamaki tare da fad'in"Wannan aikin Ladidi ne wallahi, d'azu ba kaje har inda suke ba, ina jin kana zaginta" Halliru yace"To kuma da kace baka ga wanda yazo gurin ba" "Tabbas ban ga kowa ba, amma na tabbatar da cewar Ladidiya ce zatayi maka wannan aikin, wallahi kasan ta kamar aljana take, sam ba'a ganinta a guri" Cikin fushi Halliru yace"Billahillazi sai sun biya ni kud'in nono na, idan ta saba yi wa wasu suna k'yaleta to ni wallahi bazan d'auki asara ba" Murmushi Mutari yayi yace"Shiyasa d'azu kamar in ce maka kar kaje inda suke saboda nasan halin yarinyar bata da mutum ci wallahi shiyasa kaga ni bana shiga sabgar ta, ko kaman ta lokacin da ta watso min ruwan kwata kaina kasan ranar har nama da gurasa basu tsira ba sai da ruwan kwatar ya same su,, ko da na je na fadawa kakarta hakuri kawai ta bani, da k'yar na kara tayar da wani jarin" Halliru ya tsuguna yana goge gumi, Ladidi ta kassara masa rayuwa ta rusa masa jarin sa, yau-yau d'in nan ya d'auko sabon nono duro guda dubu goma sha biyu yarinyar nan ta zuba masa k'asa a ciki,, kewaye shi sukayi suna bashi hakuri wasu na bashi shawarar kawai ya tafi ya fadawa mai gari a bi masa hakkin sa. Tana tafe tana d'aura zaninta,, gami da kad'e ragowar k'asar dake jikin zanin,, ta gyara d'aurin d'ankwalin ta,, ta cigaba da tafiya fagam-fagam! Ko tsoron dare ba tayi, Tara da rabi na dare, haka ta dunga wuce majalisa ta maza babu abunda ya dame ta,, har ta karya kwana zata nufi gida sai ta canza shawara juyawa tayi ta koma da baya, kwanar gidan kallo ta nufa,, tun daga nesa ta gango matasa sun cika rumfar kwanon ga hasken wuta nan tar! Masu gyad'a da daddafan k'wai da saurarnsu sai cini ki suke,, bayan gurin kallon bola ce,, gashi ba wani dogon gini bane wani gurin ma da langa-langa a ka rufe,, a hankali ta hau kan bolar ta daddafa ta d'ane kan k'aramar katangar,, kanta ta zura tana lek'awa, aikuwa taga matasa sun cika gurin suna zaune kan bainci wasu ma basu samu guri ba, suna tsatstsaye sai ihu! Suke da alama film din ya d'auko dad'i, sosai take zura kanta domin taga wane irin film ne da ake ihu!! Wani saurayi ne ya kare mata da tsahon sa, ji take kamar ta sauka ta zabga masa mari,, ihun da sukeyi yana hana aji komai sai wani take take ji babu alamun k'usha-k'usha,, kunne ta kasa sosai lokacin da Taji wannan saurayin yana magana dana kusa dashi "Gaskiya ina son film d'in nan wallahi, Sharukahn ya iya soyayya , nifa lokacin da ya rungume ta, he da na kusa suma dan dad'i wannan film din yayi kyau wallahi" Dariya d'ayan yasa yace" Ya sunan film din ma"? "Khoch-khoch hotaih" Hahahaha Gaskiya film din yayi ko nawa ake ce zan biya domin in kalle hi" Ihun!! da suka ji ne yasa suka mai da hankalin su kan Tv,, Ladidi tace"Hegu "yan iska ni da nasan ba na fada bane ma bazan zo b.... Maganar ta ta katse lokacin da Allah ya bata ikon hango akwatun tv an hasko Sharukan da kajol suna soyyaya da rungume-rungume! " Kan Uba!! Ta kurma wani uban zagi,, tsaki taja tana k'okarin dura kasa tace"Allah wadaran in tsaya in kalli wannan iskancin, nifa shiyasa na tsani wannan Dan film din gwara Salman kan,, yana da mutum ci,, dura tayi k'asa tana Jan tsaki sai mita take da ta sani bata zo ba, inda ta San ba fim din fada bane, Shiru gurin duk masu saye da siyarwa dake gurin sun tashi,wasu ma har sun soma futowa daga gurin kallon dana film din yazo karshe, ko a jikinta, ta kama hanyar gida fud'un-fud'un,, kamar daga sama, taji an cafki hannuta, ta juya a fusace! Ilu ne ya ke mata wani kallo yana lashe baki. Hararsa tayi tace"Sakar min hannu ko in ci abu ta kazar ka" Ilu yace"Ni kike zagi takand'a" ? Fuzge hannuta tayi a fusace! Ta tsani ya kira da wannan suna wai takand'a, tace"Uwarka ce takand'a bani ba" Mari ya kai mata, ta kauce da sauri,, hannuta yaja da k'arfi ya na kokarin kai ta wani lungu ta turje tana zagin sa,, yace"Dama neman ki nake ruwa a jallo Dan uban ki, d'azu kin fasawa k'anwata baki ranan kin zage ni ,to yau zaki gane kuran ki" janta yake tana turjewa, gami da durzar k'asa da kafafun ta, duk k'arfin sa sai da ya sare, ya kama haki!! Tace"Sake ni ni ba "yar iska bace" Yace"Sai ki gayawa wanda bai sani ba, Dan uwarki daga gidan Uwar ki kike shegiya jiki duk jijiya sai k'arfin tsiya" "Uwarka ka zaga ba tawa ba" tafad'a a fusace! Yace"Au! Baza kiyi shiru ba" ? "Sai kayi shiru zanyi, kuma wallahi zaka San ka zagi uwata" "To me zakiyi Takand'a" ? yafad'a yana mata dariya ta k'arfin hali, domin duk ya gaji yau ya kara tabbatar da cewar yarinyar ba ita kadai bace,, shamtar sa tayi yana fad'in "Zaga kuwa abunda zanyi yanzu" kafin ya ank'ara ta kwashe k'afafun sa da hannu daya ta zubar dashi a gurin ta falfala da gudu tana shek'a dariya babu ruwanta da dare. Ilu ya rike bayansa yana rintse ido sosai bayan sa ya bugu da wani dutse ya Dade a kwance a gurin "yan gidan kallo na ta wuce shi a kwance,, cikin takaici ya mike tsaye yana da ya sanin kula Ladidi gashi ta ji masa ciwo a banza. Mai koko na tsaye a soro cikin tararrabi, k'arfe goma da rabi na dare, Ladidi ba ta shigo gida ba, ta duba ko ina bata nan,, D'alha ya gama fad'an sa ya futa nema,, da ya d'auka abun wasa ne, sai da yaga an gama Taskar labarai, hankalin sa ya tashi, babu shiri ya bazama neman ta,, duk ya duba inda ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39