Chapter 13
Chapter 13
shegiyar yarinya k'azama zo ki fuce daga gurin nan ko in karya miki k'afafu" ya k'arashe maganar yana zuwa kanta, wani tsalle ta buga! Ta d'ane jikin bishiyar mangwaro can kololowa, cikin mamaki ya d'aga kai yana kallonta, itama shi take kallo tace." Idan ka isa kazo ka Kore ni, bayan ma gonar ta kakana ce kuka sace mana" Hakkim ya saki baki galala! Yana kallonta ,wasu mangwaro ta Ciro sun gaji da nuna ta mulmulasu sukayi ruwa tafasa da bakin ta ta saita shi, ta jefo masa a jiki kafin kace me yayi fallatsi ya b'ata masa duk gaban rigar sa da fuskar sa. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/29, 6:51 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *Ayi hak'uri da errow⚠* _Yau pege d'in babu yawa saboda ina fama da zazzab'i, ina b'ukatar addu'ar ku😓👏🏻_ *🅿12* Cikin tsantsar b'acin rai! Ya d'aga kansa sama yana kallonta, tana k'okarin saukowa sai dariya take k'yalk'yala masa, tana dura k'asa ya cafki hannunta wanda yaji tamkar ya rik'e bushashan ice dan tauri, k'okarin fuzge hannunta take tana zabga masa harara tamkar idonta zai fad'o k'asa!. A fusace! ya kai mata wani wawan mari! ta kauce da sauri! amma duk da haka sai da ya samu gefan fuskar ta, zagi ta hau d'ura masa tana tsalle, kamar zata kai masa duka take fad'in "Sakar min hannuna ni ba " yar iska bace". Hakkim ya buge mata baki da d'aya hannun nasa, kafin kace kwabo jini ya fara zuba, ihu! ta kurma wanda yasa su Yusuf suka runtumo da gudu gurin. Hakkim na tsaye hannunsa tam! da na Ladidi sai buge-buge take tana kwanciya a k'asa dole sai ta k'wace daga hannunsa, wawan hauri ya kai mata da k'afar shi guda, ta k'ara k'wala k'ara tana kuza masa ashariya! Yusuf ya k'araso gurin, hankali a tashe yake fad'in"Wai meye yake faruwa ne? wannan yarinyar fa, daga ina".? Bak'in ciki da b'acin ya hana shi cewa uffan,sai cije baki yake yana dukanta da k'afar sa, Salima ta k'araso gurin jikinta a sanyaye take fad'in"Broth waye ya b'ata maka jiki da wannan k'azantar " Yusuf ya Kai dubansa gurin shi sam bai lura ba, hankalin sa na kan Ladidi, har hanzu hannuta na rike a nashi yana dukanta da k'afafunsa ita kuma bakin ta bai bar zaginsa ba, tana deb'o k'asar gurin tana watsa masa a jiki. Yusuf ya fara k'okarin kwace daga hannunsa, ya fuzge da k'arfin yayi wani mugun boll da ita ta gangara can gurin k'ofar futa kanta ya bugu da wani dutse, da sauri ta mike tamkar ba ita akai wa wannan dukan ba, wani mugun tsalle tayi sai gata a gabansa, dama ya tsammaci zuwan ta, k'afar sa ya sanya ya tad'eta! Ta fad'in a gurin a sume!! Yusuf ya saka salati yana fad'in"Shikkenan kaga ka kashe yarinyar mutane ko, innalilahi wa'inna ilahi raji'un"!! Salima ta fashe da kuka tayi kan Ladidi tana tattab'a jikinta, Yusuf ya futa daga gurin da sauri, gabansa sai fad'uwa yake, ashe k'addara ce ta kawo shi, shi ko Hakkim ko a jikinsa, karkad'e rigar sa yayi cike da bak'in ciki da b'acin rai! Yake k'okarin barin gurin,Salima ta rik'e hannunsa tana kuka take fad'in"Broth ina zakaje LA tsaya ka duba wannan yarinyar ko suma tayi don girman Allah, ni kam Wallahi da nasan haka zata faru da ban biyo ka ba" . Fuzge hannunsa yayi cikin b'acin rai! Yace"Yanzu ma kina iya komawa gida babu Wanda ya rike miki k'afafu ga hanya nan" yana gama fad'in maganar shi ya futa daga gurin. Karo suka ci da Yusuf ya tawo da sauri hannunsa rike da robar ruwa na faro, ko kallonsa bai yi ba yayi fucewar sa. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/30, 10:08 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟♀🧟♀🧟♀K'WADAGA🧟♀🧟♀🧟♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _Alhmdullahi jiki yayi sauk'i_ *Gaskiya naji dad'i sosai da kularwar ku akaina nagode masu kirana a waya kuna yimin ya jiki da fatan samu lafiya,masu min sannu ta pravite wanda na sani da wanda ban sani ba nagode sosai da sosai ina muku fatan alkairi* *Jan kunne⚠* _Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin book d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ ki siyar min da littafi ba da sanina ba, Wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan haka, hattara dai!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje yaci gumin sa, kane mi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿13* Cikin sauri Yusuf ya k'araso gurin da Ladidi take kwance, ya bud'e ruwan,ya fara zuba mata a fuskar ta furgice! ta mik'e zaune ta k'wala k'ara! Waige-waige take tana neman Hakkim a gurin, Salima ta rik'e hannunta tana son tayi mata magana. Fuzge hannunta tayi da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in" Yana ina."? Duk suka mik'e suna kallonta, Yusuf yace." Ke yarinya me ya shigo dake gurin nan?,da har kika jawo wa kanki suma." Banza kallo tayi masa ta murgud'a bakinta, bata ce masa komai ba, ta bar gurin bagazan-bagazan! kallo suka bita dashi, Yusuf ya kalli Salima yace." Anya kuwa yarinyar nan me lafiya ce"? Salima ta k'unshe dariya tace." Lafiyan ta lau. Kamar ka manta da a k'auye kake dole kaga haka." Yusuf ya girgiza kai yace." Ni abunda ya bani mamaki da ita shine yadda ta shigo gurin nan wallahi". "Gaskiya nima nayi mamaki." Salima tafad'a yayin da suke k'okarin futa dafa gurin. ******** Ta inda ta shiga gurin tanan ta haura ta futa Hakkim na kallonta tun futowar ta har lokacin da take haure katangar yana gani, zuciyar sa yana mamakin ibilicin yarinyar, yau d'in nan zai sanya a kewaye katangar gurin, da waya mai k'ayoyi, duk saboda ita dole kuma a zuba masu gadi a gurin. tuni ya cire kayan da ta b'ata masa ya watsar dasu harabar gurin, domin mugun k'yamk'yami ne dashi, idan ya tuno halittar yarinyar sai yaji zuciyarsa tana wani irin tashi! sosai zuciyar sa take masa zafi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya tab'ai masa irin abunda yarinyar tayi masa dole ne ya d'auki mataki akanta mutukar ya kara ganin k'afarta a gidan, karya ta zaiyi kawai kowa ya huta. Su Yusuf suka k'araso gurinshi ya sha kunnu domin baya son ma yayi masa maganar, Simi-simi Salima ta shiga ciki, Yusuf ya samu kujera ya zauna yana kallon Hakkim d'in, da yake k'ara yin kicin-kicin da fuska, yace." Zauna zamuyi magana da kai". A fusace! Ya juyo yana fad'in"Ubana ne kai zaka bani umarni". Yusuf ya kalleshi , da alama zuciyar sa har yanzu batayi sanyi ba. Yace." A'a ba ubanka bane". "To ka fad'i duk abunda zaka fad'a kunne na yana ji". Ya k'arashe maganar yana juya masa baya. Yusuf ya mik'e ya k'arasa inda yake, kafad'arsa ya dafa cikin taushin murya yace." Aboki wai me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39