Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

yara. “Marhaba (Hello)” Ta ji muryar a bayanta, hakan yasa ta juya domin ganin me maganar, duk da ta ji kamar ta san muryar. Wannan matashin ɗan kasuwar da suka haɗu a Cavo Espresso Bar ne tsaye a bayanta yana murmushi, sanye yake da farin plain jogger sets. Hannayensa zube cikin aljihun hoodie ɗin kayan, yana kallonta yana murmushi a lokaci guda. “Ahalain (Hi)” Ta amsa da ɗan guntun murmushi, sai ta ga ya faɗaɗa murmushinsa yana nufota, sannan ya tsaya a gefenta. “Mu je” Ta jinjina kanta, sanna suka jera suka fara tafiya, kanta a ƙasa tana kallon interlocks ɗin dake ƙasan hanyar da suke bi. “Ke kaɗai kika zo nan?” Ta ji ya tambaya bayan wani lokaci, sai ta ɗaga kai ta kalle shi, amma shi ba ita yake kallo ba, ita ma kuma sai ta ɗauke kai tana faɗin. “A'a tare da yaron 'yar uwata na zo” Tana jin sautin murmushinsa, kafin yace. “Shi ne wancan?” Ya nuna mata Imran dake wasa tare da wasu yara. Ta kalli yaron da ya nuna, sanna ta jinjina masa kai. “Eh shi ne, ka san shi ne,? Ya girgiza kansa. “Ban sa shi ba, amma na ga sanda kuka shigo nan tare” Ta ɗan yi murmushi kaɗan, a lokacin da suka isa jikin wani bench, suka zauna ta kiran Imran. Imran ɗin da ta kira ya zo da gudu ya karɓi juice ɗin da ta siyo masa, sai da suka gaisa da Uwais, sannan ya juya ya koma suka ci gaba da wasa. “Asir?” (Lemo?) Ta faɗa tana miƙa masa cup ɗin da ya rage a hannunta, ya girgiza mata kai yana shafa sumarsa me kyau da ƙyalli a ido. Ita kuma sai ta jinjina kanta, sannan ta ɗan sha lemon kaɗan, kana ta aje shi a gefenta tana saƙala ganshinta a bayan kunnenta, sakamakon iskar da ake ta sa yana tashi a iska, dan yana cikin style ɗin flat iron waves ne “Wani aiki kike?” Ya sake tambayarta, wannan karon ma kafin ta amsa masa sai da ta kalle shi. “Ina aikin koyar da kiɗan guitar ne a Repton school Dubai...” Ya jinjina kansa. “Aiki me kyau... Ni ma na iya kaɗa guitar, ta kan bani nutsuwa a lokuta da dama, shi yasa ban cika kaɗawa ba sai ina cikin nishaɗi, domin ta ƙara daɗaɗa yanayin da nake ciki” Ivana ta yi murmushi. “Kai fa, menene aikinka?” Wannan karon ma kafin ya bata amsa sai da ya shafa sumar kansa. “Kasuwanci, mahaifina shi ne shugaban rukunin kamfanunuwan Al Aida, ni kuma ni ne magajinsa” Ta dube shi, dan ta san Al Aida babban kamfani ne, da suke sarrafa abubuwa da dama. Shiru ya ratsa wurin na wasu mintuna, kafin ya miƙe tsaye yana faɗin. “Ni zan tafi” Ita ma sai ta miƙe tana kallonsa. “Sai mun sake haɗuwa” Ya miƙa mata hannunsa alamun su gaisa, tare da faɗin. “Sunana Uwais Faizal” Ta kalli hannun nasa, sannan ta miƙa nata hannun suka gaisa. “Ivana Sagar” A lokacin da ya jinjina hannunsa tare wani abu kamar wucewar iska ya gifta a cikin kanta. Haka kawai take jin kamar ta taɓa haɗuwa da wani kamar haka a can baya, kamar akwai wani me kammani irin nasa da suka taɓa gaisawa irin haka, amma ba'a Dubai Miracle Garden ba, a wani unknown wuri da ba ta isa tace ga shi ba. “Na ji daɗin haɗuwa da ke Ivana” Faɗin Uwais yana murmushi, ita ma sai ta jinjina kanta. “Ni ma haka” *Salma Ahmad Isah ✍️* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-4 *House No. 106, Street 14, Jumeirah Bay Island, Abu Dabhi, Dubai.* “Ban san da wani yare zan yi wa Arman magana da shi domin ya gane abin da nake nufi ba... A ko da yaushe ɗana na nisantata saboda wannan dalilin guda ɗaya!” Faɗin Abby, yayin da suke hira da Immi a cikin katafaren ɗakinsa, da aka ƙawata da kayan adon ɗaki na zamani, kuma masu kuɗin gaske. Immi ta aje cup ɗin shayin dake hannunta, sannan ta shiga wasa da yatsunta tana faɗin. “Tun tasowarsa yayanka da wasu daga cikin 'yan uwanka ke nuna masa cewa kasancewarsa makaho ba shi da wani fata a rayuwa. Buri da mafarkin cimma shi na masu lafiya ne, shi da ya kasance nakasasshe ba shi da ikon son cimma wani buri nasa a rayuwa. Tun ɗana yana ƙarami aka nakasta min zuciyarsa, domin kalaman tozarci da na aibantawa su ne suka sa ya tsani duk wata harkar kamfani ko kasuwanci” Abby ya kai hannu aje nasa cup ɗin da yake riƙe da shi, sannan ya lumshe idonsa yana shafa kyakkyawar sumar kansa. “Abin da kika faɗa haka ne Zahra, amma a halin yanzu ba ni da ikon canzawa Arman ra'ayi, batun nakasa kuma ke kanki shaida ce, da ace ina da hali, da na bayar duk abin da na mallaka, domin sama masa lafiya...” Ya buɗe idonsa yana jin zuciyarsa na masa zafi. “Ina da wata shawara” Abby ya kalli Immi da ta yi wannan batu. “Shida ga watan nan da muke ciki ranar haihuwarsa za ta zagayo. Dan haka me zai hana mu haɗa shagalin taya shi murnar zagayowar ranar da aka haife shi. Ko da ba babban party ba, ɗan ƙarami, wanda za mu gayyaci ahali da abokai, yayin da ake cikin shagalin bikin, za ka gabatar masa da takardun kamfani, a gaban kowa, ka umarce shi da ya sa hannu, na tabbatar ba zai ƙi ba, kuma ka ga mu ma sai mu huta, dan daga zarar ya sa hannu magana ta ƙare, babu shi babu sake cewa ba ya son shugabanci!...” Abby ya yi shiru na wani lokaci yana shafa sajensa. “Arman yana da taurin kai, zai iya ƙin amincewa” Immi ta girgiza kai. “Duk taurin kansa ba zai so ya bamu kunya a idon duniya ba” Abby ya yi murmushi. “Na gode da wannan shawarar taki Azizati” Ya ƙarashe yana kamo hannunta na dama, tare da sumbatarsa. Immi ta yi murmushi tana kallon mijinta. “Bari na je na duba yaran nan, wata ƙila sun yi bacci” Ta miƙe tana tura gashin kanta baya. “Sai kin dawo” Cewar Abby yana ɗaukan cup ɗin teans. Immi na fita ta fara da ɗakin Gulzar, kuma kamar yanda ta yi zato ne, sanda ta isa ɗakin nata samunta ta yi tana bacci. Dan haka ta shiga ɗakin cikin kulawa, ba tare da ta bari ta yi making sound ɗin da zai sa ta farka ba. Sunkuyawa ta yi ta sumbaci kanta, sannan ta juya ta bar ɗakin. Daga nan kuma ɗakin Arman ta wuce, shi kam bai yi bacci ba, dan zaune ta same shi a kan gadonsa yana kallo a system. Tana shiga ɗakin ya tsayar da kallon, sannan ya rufe system ɗin yana binta da kallo, har ta zauna a kan gadon nasa. “Tu abhi tak kyun nahin soya?” (Me yasa ba ka yi bacci ba har yanzu?) Ta tambaya cikin harshen Urdu tana kallon kayan dake jikinsa, dan yana sanye da khaki trouser da shirt ne, sumar kansa duka ta sauƙo kan goshinsa, sannan glasses ɗin da suke tamkar rayuwarsa na maƙale a fuskarsa. Sai ya kwanta a kan gadon, sannan ya ɗora kansa

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35