Chapter 23
Chapter 23
karɓa cike da naiman ƙarin bayani. “Akwai dabino da busasshen nama da kuma kubuz a ciki, zai isheku ku ci har na tsawon kwana uku da za ku yi kuna tafiya. Idan har kun isa Askar kuma naiman abinci ya ƙare, domin abokin tafiyar da za ku haɗu da shi a can shi ne zai ci gaba da kula da cikinku da ma lafiyarku!” Adam ya rataya jakar a kafaɗarsa, lokacin da tsoho yake bawa Arman wani takobi dake cikin gidansa. “Za ku buƙaci wannan a hanyarku, na san kai kaifi dacewa da iya sarrafata, ka kula JAGORA!” Ya ƙara kiransa da sunan da ya kira shi da shi ɗazu, tun da Arman ya kalli takobin abu ɗaya ne ya faɗo ransa, wata rana, wata magana da ta taɓa shiga tsakaninsa da Gulzar. _“Daga an yi magana sai ka ce kana zuwa fencing class, bayan ko takobin gaske ba ka taɓa riƙewa ba!...”_ _“Wata rana zan riƙe”_ Ita ce amsar da ya bata a lokacin, yanzu kuma ga ranar ta zo, cike da martabawa ya sa hannu biyu ya karɓi takobin, wani abu mafarkinsa, wani abu burinsa, wani abu da yake matuƙar son ya cimma a rayuwa, wato mallakar takobin da ba na fencing ba. Ya ɗan ɗaga takobin sama kaɗan, sannan ya zaroshi daga cikin gidansa, ƙyallin takobin ya haska a cikin rana, hakan ya sa ya dalle masa ido da har sai da ya rintsesu, a hankali ya sauƙe takobin yana ƙare masa kallo... Wani mafarki da ya saba yi na yaƙin nan da yake na tariyowa kansa a cikin tunaninsa, wato dai wannan mafarkin da ya daɗe yana yi yana da nasaba da wannnan JUYIN KWAƊON da rayuwa ta yi da su?. Daga ruwa zuwa ruwan zafi, takobin ya mayar gidansa, sannan ya kalli datijjo dake ta fara'a. “Mun gode sosai” Ya girgiza kansa. “Ni ya kamata ace na gode muku, domin zuwanku yau ya sa na sauƙe nauyin dake kaina, fatan nasara” Ya ƙarashe yana dafa kafaɗar Arman guda ɗaya, Arman ya gyara zaman glashinsa, sannan yace. “Mene ne sunanka?” A wannan karon kuma dariya ya yi. “Babu buƙatar sanin sunana yanzu, domin akwai yiyiwar sake haɗuwarmu a nan gaba, ku je, Allah ya bada sa'a.” Daga haka suka juya suka fara tafiya a kan hanyar da ya nuna musu, kowa a cikinsu jikinsa a sanyaye yake, ban da Arman, wanda ya sa fata da yaƙinin cewa ko ba yau ba tabbas za su koma gida, kuma zai tabbatar da hakan!. Sai da suka yi nisa sosai, sannan datijjon nan ya soma ja da baya, ya tsaya a gaban bukkarsa, ya lusmhe idonsa yana taɓa jikin bukkar, nan da nan bukkar ta ɓace, kamar ba'a taɓa hallitar wata bukka a wurin ba. Ya buɗe idonsa yana murmushi, sannan ya daka tsalle, kafin ya dire ya bi iska ya ɓace. Sun ɗauka cewa tafiyar mai sauƙi ce, dan tun da suka kama hanya ba su tsayawa sai idan sun lura da lokacin sallah ya yi, kuma daga sun tsaya sun gabatar da sallahr za su ci gaba da tafiya, duk da jikin kowanne a cikinsu a sanyaye yake, Arman ne kaɗai ke ƙokarin ƙarfafa musu gwiwa. Ba su tsaya yada zango ba sai da dare ya yi, shi ma a cikin dokar daji suka kafa tantinsu guda uku. Amma ba su shiga sun kwanta ba, suka zauna a waje suna jin ɗumin wutar da suka hura. Sai a lokacin Adam ya buɗe jakar abincin da tsoho me abin al'ajabi ya basu, ya shiga fitar da kayan ciki. “Ni dai ba na jin zan iya cin wannan abincin” Faɗin Adam yana nunawa Arman, Arman da ya nutsa duniyar tunanin 'yan uwansa ya dube shi. “Za ka ci idan har abincin da muke da su suka ƙare” Adam ya yi shiru kawai... Ita kuma Ivana na gefe tana duba service ɗin wayarta babu ko ɗaya, chajin wayar ma ya kusa ƙarewa. “Ba service, ba wutar nepa, babu abincin da muka saba ci, babu komai na more rayuwa!” Cewarta tana aje wayar, dan ta ga babu amfanin da za ta mata. “Ba ki da chaji ne?” Adam ya tambayeta, ta jinjina masa kai. “Ina da solar, gobe sai ki yi chajin” Ta sake jinjina kai tana shan tea ɗin da suka dafa. “Ban taɓa tunanin cewa zan wayi gari na yi rayuwar da babu abubuwan ci gaban zamani ba, wai ashe akwai lokacin da rayuwa za ta juya mana mu kasance a halin da ba mu isa mun yi communicating with wani ba?” Faɗin Adam yana rufe system ɗinsa. “Duk abin da zai faru damu a gaba ba mu da masaniyarsa, ba mu da ikon canza komai” Arman ya ba shi amsa. “Kuma ka san ina ga kamar wannan babbar dama ce na samu da zan ɗauki hotunan abubuwan da babu photographer ɗin da ya taɓa gabatar da su, masarautun mutanen da, al'adu da shigarsu da ma abincinsu!” “Ƙwarai, kuma ina ga kamar wata dama ce da za ta sauya tunanin Arman a kan Alhadi!...” Adam da Arman suka dubi Ivana da ta yi wannan furuci cikin mamaki... “Ke! A wannan duniyar fa ba su san masana'anta ba ballantana babban kamfani kamar Alhadi, ta ya za'a samu wani kamfani da zai sa Arman ya sauya ra'ayinsa kafin mu koma gida?” “Masarautun zamanin nan suna kama da kamfanunuwan zamaninmu!” Ta basu amsa, suka sake duban juna, amma shi dai Arman bai ce komai ba. Har suka gama zaman hirar suka koma cikin tent ɗinsu suka kwanta, cike da fatan wayar gari lafiya. MAMLAKATUL JIYAD. Cike da ƙasaita, izza da isa wani basaraken matashi ke tafiya, kamar wanda ba ya son taka ƙasa, hannayensa goye a baya, yayin da masu gadinsa ke take masa baya. Wasu irin kayan sarakunan da ne a jikinsa, wanda kai daga ganinsu ka san sun amsa sunansu kayan alfarma. Sai da suka kai ƙarshen dogon falon dake ƙarshen sashen sarki, sannan ya dakata, hakan ya sa su ma dakarun dake take masa baya suka dakata, cike da izza ya daga hannayensa, ba sa jira ko buƙatar ya furta musu abin da yake buƙata, cikin hanzari mutum biyu dake cikinsu, suka ƙara matsawa kusa da shi, sannan suka kama rigar sarautar dake saman kayan nasa da za'a iya kira da alkyabba. Suka sauƙeta daga kan kafaɗunsa, sannan suka ja da baya a tare suna riƙe da rigar tasa, sai da suka ja da baya, sannan mutum biyun dake jikin wata ƙofa da aka ƙera da zallar baƙin ƙarfe suka buɗeta, hakan ya bayyanar da doguwar matakalar da ta yi ƙasa zuwa harabar fadar. Kuma daga ƙarshen matattakalar akwai wani keken doki da matuƙinsa, wanda ke jiran fitowar sarki. Cikin wannan takun nasa na izza ya soma tafiya, har ya kai ƙarshen matattakalar, matuƙin keken dokin ne ya sauƙa daga wurin da aka tanada dominsa, ya buɗe gidan baya na keken, inda aka tanada domin zaman mai martaba, sai da ya shiga ciki ya zauna, sannan matuƙin ya rufe ƙofar keken dokin. Kana ya koma wurin zamansa, ya fara sarrafa dokuna biyun dake jan keken, suka bar ginin fadar, suka hau wata hanya ɗoɗar, wadda za ta sadasu da hanyar barin gari, da yake kowa ya san keken dokin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35